Sashe 22
Sakayyah Part 3 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Ahankali ya janyota jikinsa ya ɗaura hannunsa akan cikinta yana shafawa saboda yanzu cikin yashiga wata na biyar zuwa na shida haka yasa cikin ya ɗan bayyana ya girma yayi ɗas a jikinta gwanin ban sha'awa ganin yanayin fuskarsa yasa tace.
“Ya akayi Yah Mu'allim?”.
Fuska ya narkar da damuwa atare dashi yace.
“Minha kuka fa kike yi ya za'a yi kintam bayeni ya akayi?”.
Asanyaye ta bashi labarin da Momy ta bata ta faɗa mata sai abinda take ga sirrinsu ne bai kamata ya saniba ta ɗan sakaya.
Jikinsa ya sake janyota ya rungumeta kana yace.
“Mu godewa Allah, Allah ya sake tsarkake zuciyanmu Allah ya hanamu samun damar da zamu cutar da wani, Allah ya hana wani ma samun damar da zai cutar damu.
Cikin sanyi da rauni ta gyara zamanta ajikinsa tare da cewa.
“Ameen”
Yana shafa gadon bayanta yace.
“Kuma ki daina damuwar nan ki riƙa yi musu addu'a Ubangiji Allah ya gafarta musu”.
Tana ɗan lumshe Idanunta tace.
“In sha Allahu ”.
Sake janyota jikinsa yayi, bakinsa ya kai saitin kunnenta cikin wata kasalalliyar murya mai cike da shauƙi da bege yace.
“Minha babu matsala ban takura ki bako?”.
Cikin lumshe idanu da yanda hannunsa ke yawo a sassan jikinta ta fesar da wani sanyayyan numfashi tana sake shiga jikinsa tace.
“Ya zanyi Yah Mu'allim tunda kana da buƙata?Kuma dole in ɗauke buƙatar ka tunda bana so wata ta raɓeka”.
Ya tsarsa manuniya da babba yasa ya kamo tsinin hancinta ya jijjiga tare da cewa.
“Kishi! Kishi!! Kishi!!!”.
Cikin Cunno baki ta langwaɓar da kai kana tace.
“Toh ba dole inyi kishi ba,
Idan banyi kishin kaba waye zai yi kishinka a duniya”.
Sai kuma ta marairaice fuska tace.
“Ka ƙi kayi min al'ƙwarin baza kayi min kishiya ba”.
Jawota jikinsa yayi ya rungumeta kana ya haɗe bakinsu waje ɗaya daga nan yashiga sarrafa ta cike da bege da tarin ƙaunarta...
Bayan wani ɗan lokacin Alhamdulillah yanzu cikinta ya cika wata bakwai Cif-cif.
Ahankali take sauka kan tsep ɗin sauƙa Falon Didi.
Didi dake zaune tayi saurin miƙewa hangota da tayi kana ta riƙe hannunta cike da kulawa tace.
“Ba nace miki sauƙan nan idan yana wahalar dake ki bari ba?,Idan kina son ganina ki riƙa kirana in zo ba”.
Murmushi tayi tare da faɗin.
“Toh ai Didi Likita ma da kansa yace na riƙa motsa jiki na zaman bazai yiba”.
Kai Didi ta jinjina tare da cewa.
“Haka ne kam ƴata zo ki zauna me kike so in dafa Miki?”.
Murmushi tayi kana ta maida kallonta kan Moddibo da Ibraahim dake shigowa cikin langwaɓar da kai Ibraahim yace.
“Toh koma menene za'a dafa adafa dani”.
Dariya Didi tayi tare da cewa.
“Wannan ba naku bane ”.
Murmushi Moddibo yayi tare da shiga Falon kana ya zauna agaban Khausar tare da janyo ƙafarta ya ɗaura akan cinyarsa yana ɗan jan yatsunta sai kuma ya maida kallonsa kan Didi yace.
“Didi kalli ƙafafun tan nan kamar kumbura sukayi?”.
Juyawa Didi tayi ta kalli ƙafafun kana tace.
“Eh nima naga kamar kumbura sukayi amma Dr Eshaa tace bakomai dan tun shekaran jiya da naga kumburin na kirata tazo ta duba ta tace bakomai wannan Normal ne mafi akasari wasu na fuskantar haka daga ciki wata Bakwai kuma kaga kumburin bamai yawa bane”.
Ajiyar zuciya ya sauƙe yana cigaba da matsa ƙafafun yace.
“Toh shikenan ”.
Didi kuwa Kitchen ta shiga ta ɗauko Pride rice da yaji Vegetables da naman zabbi sai Perpersoup ɗin Kifi da yaji kayan ƙamshi ta kawo fitowa dasu tayi da plate guda biyu ta zubawa Khausar kana tasa mata kifin agefe.
Kana ta zuba aɗaya plate ɗin tasa spoon biyu aciki ta ajiye atsakanin Moddibo da Ibraahim.
Daidai lokacin Rahama ta fito daga ɗakinta ware idanunta tayi tare da cewa.
“Didi anyi Babu Ni ko?”.
Murmushi Didi tayi kana tace.
“Na isa ƴar Autana bata ciba ɗauko plate kizo ki ɗibi na ki”.
Kai ta gyaɗa kana ta juya ta shiga kitchen ta ɗauko plate tazo ta zuba suka fara ci suna hira...
Yayinda hadimai keta zuryan aikace-aikacen yau da kullum.
A haka rayuwa ta cigaba da tafiya Alhamdulillah Khausar na samun wadatacciyar kulawa daga wajen tako wani sashin, sosai rayuwa take tafiya zuwa yanzu cikinta ya cika wata tara Cif-cif amma dai na ƙuda har yanzu bai zoba kuma.
Cikin kulawa Asma'u da tazo mata yini, ta zuba mata ganin ta yunƙura ta nufi bedroom cikin sauri Asma'u tace.
“me kike so in kawo Miki?”.
Kai ta girgiza tare da faɗin.
“Bakomai kawai ina so in shiga bathroom ne yau tunda gari ya waye fitsari da yaƙi ƙarewa nake tayi”.
Ɗan zare idanu Asma'u tayi tare da cewa.
“Fitsari kuma?,Kin fa ɗawa Dr?”.
Kai ta girgiza kana tace.
“A'a ban faɗa masa ba bakomai ai”.
Cikin cikin kulawa Asma'u tace.
“Toh bari in tai maka Miki?”.
Ƴar dariya Khausar tayi tare da faɗin.
”Laaa da kin bari babu inda ke min ciwo fa”.
Cike shaƙuwa Asma'u ta gyaɗa kai tace.
“Toh shikenan ”.
Khausar kuwa ban ɗakin tashiga.
Asma'u kuwa wayarta ta dauka tare da kiran Dr Jameel yana ɗauka tace.
“Hello Dr”.
Daga ɗaya ɓangaren cike da begenta yace.
”Na'am dear ya akayi?”.
Cikin sauƙe numfashi da da kulawa tace.
“Kaga tun daga ɗaxun da muka zo zuwa yanzu bai wuce awa ɗaya zuwa biyu ba ko?”...
Kai ya gyaɗa mata tare da faɗin.
“Eh”.
Numfashi ta fesar tare da cewa.
“Toh wallahi daga lokacin zuwa yanzu Khausar ina ga tashiga ban ɗaki tayi fitsari ya kai sau biyar nace ta faɗa maka tace wai babu matsala kawai yau yawan fitsari ne take fama dashi”.
Da mamaki yace.
“Ha'a ikon Allah kuma tace ba abinda yake mata ciwo?”.
Kai ta gyaɗa tare da faɗin.
“Eh”.
Cikin sanin makamar aiki da yanayin masu ciki yace.
“Alamun na ƙuda ne yana iya tashi ko yaushe”.
Cikin sauƙe numfashi tace.
“Kuma fa tace babu abinda yake mata ciwo”.
Ajiyar zuciya ya sauke tare da faɗin.
“Eh ba komai bari idan ta fito sai ki haɗa Ni da ita”.
Kai ta gyada kana ta katse wayar, jim kaɗan Khausar ta fito.
Tana fitowa Moddibo na shigowa kasancewar Dr Jameel ya kirasa ya faɗa masa yana shiga ya kama hannunta ya zaunar da ita akan kujera kana ya zauna aƙasan lallausan Darduma tare da k...
By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAKAYYAH Book 3 PAGE 6*
NA
*Aysha Aliyu Garkuwa*