← Book details Sakayyah Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 38

Sashe 35

Sakayyah Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna fitowa suka ga wani mahaukaci yara na binsa suna ta ihu yana cewa.
“Nine dai Boka Kar'uzu na aikata shirka na ɓatar da mutane na shuka zunubai da yawa Ni nariƙa yiwa mutane Sihiri!”.
Cikin tsananin mamaki da rawan jiki Samira ta kalli Amina tare da cewa.
“Amina wanna Boka Kar'uzu ne fa”.
Da sauri Amina ta dafe ƙirjinta tace.
“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un wallahi Samira shine rayuwa ba tabbas duk wanda ya saki Allah ya kama waninsa ya shiga uku”.
Cikin sanyi Samira tace.
“Wallahi kuwa Allah ya yafe mana Ubangiji yajiƙanmu ya gafarta mana zunubanmu”.
Cikin kaɗuwa da rauni Amina tace.
“Ameen ya hayyu ya ƙayyum ”.
Boka Kar'uzu kuwa cikin ihu irin na ƙazamai lalatattun mahaukata da ƙarshen su ya munana ya cigaba da ihu yana faɗe-faɗe yaje zai tsalle ke kwalta wata ƙatuwar Mota ta buge kansa atake yayi daga-daga akan kwaltan mai motar kuwa ko tsayawa baiyi ba ya gudu.
Irin ƴan iskan samarin nan ne suka sa Shebir suka kwashe Jejjegen naman gawarsa suka tura aƙaton kwalbet da ruwa ke gudu ruwa yaja gawarsa ya wuce ya kai sa cikin Fadamar Gembila kifaye suka samu abinci.

Haka dai Rayuwa ta cigaba gaba da tafiya mai aikata Alkhairi ya fuskanci Alkhairi mai aikata sharri ya fuskanci sharrinsa ra'anul aiyn...

Morocco rayuwa ta cigaba da tafiya cikin daɗi da kwanciyar hankali Keyah yayi kuɓul-kuɓul dashi ya shiga wata na takwas har ya fara tsayuwa Moddibo ne zaune a tsakiyar falon Didi yayin da Keyah ke rarrafe cikin Murmushi Moddibo yace.
“Iyeeee Toyi manga toy-toy Toyi manga toy-toy manga”.
Yana ɗan tafa hannunsa Keyah kuwa ƙoƙarin miƙewa yake yana ƙyalƙyala dariya.
Didi dake gefe tayi Murmushi tare da cewa.
“Ohhh zai fa haukataku in baku nutsu ba fa”.
Dariya Moddibo yayi kana yace.
“Didi kin gani dai ya fara tsayuwa ko”.
Kallon Keyah dake tsaye ya dafe jikin kujera tayi tare da faɗin.
“Toh Barka tunda ya fara tsayiwa yayi kyau anyi Sa'a Barka”.
Matar Ibraahim dake gefen Didi tayi Murmushi tare da cewa.
“Wallahi kuwa Didi kallifa ya tsaya fa”.
Sai kuma ta juya ta kalli Khausar tace.
“Ba ina faɗa Miki ba shekaran jiya ya riƙe kujera ya tsaya ba. cewa kin dai ji baki yardaba tunda ba ki gani ba Lalla Khausar”.
Murmushi Khausar tayi tare da cewa.
“Ato yanzu kam na gani da idona Oum Keyah”.
Cikin sauri Matar Ibraahim ta rungume Keyah tare da faɗin.
“Allah ya raya mana kai da Imani Keyah”.
Murmushi Moddibo yayi kana yace.
“Ameen ya hayyu ya ƙayyum”.
Miƙewa tayi ta ɗauki Keyah tana masa wasa ta nufi Side ɗin sa.
Khausar kuwa Ahankali ta juya ta kalli Moddibo cikin sanyi tace.
“Yah Mu'allim na kwana biyu banji labarin Asma'u ba tun ranan sunan Addah Asiya fa bamu sake haɗuwa ba”.
Cike da kulawa Moddibo ya gyara zamansa yace.
“Toh badamuwa in Sha Allahu da daddare zamu je”.

Bayan Khausar sun idar da sallar Isha'i suka tafi gidan Asma'u afalon suka same su zaune Dr Jameel na zaune ƙasa Asma'u na saman kujera kallon Khausar Dr Jameel yayi tare da cewa.
“Yawwa gwara ma da kika zo”.
Cikin kula Khausar tace.
“Toh meke faruwa?”.
Ta ƙare maganar tana miƙawa Asma'u Keyah data miƙo hannu”.
Karbansa Asma'u tayi cikin sanyi murya take masa wasa tare da cewa.
“Keyah ɗan Albarka”.
Wangale baki yayi yana ƙyalƙyala mata dariya ƙyal-ƙyal-ƙyal rungumesa tayi tare da sumbatar sa kana tace.
“Allah ya maka albarka”.
Khausar na Murmushin yanda Asma'u ke nunawa Keyah soyayya tace.
“Ameen!”.
Moddibo kuwa ido ya ɗan zubawa Asma'u dan ya lura kamar fuskantar na ɗan kumbere kaɗan more especially eyes ɗinta.
Ajiyar zuciya Dr Jameel ya sauƙe kana yace.
“Ki ganta nan wai ita tana ga bata da rabon haihuwa tunda duk gwaje-gwajen da za'a yi anyi lafiyanta ƙalau nima lafiyata lau, amma gashi har yanzu bata da ciki shine take ta kuka b'na faɗa mata lokacine, ta kwantar da hankalinta”.
Cikin sanyi tayi Murmushi hawaye na zuba a idanunta tace.
“Ka gani fa Addah Asiya ta haihu Dija ma ta haihu amma Ni har yanzu ko ɓatan wata ban taɓa yiba ina so in haifawa Keyah Mata”.
Murmushi Khausar tayi tare da faɗin.
“Ai zaki haifa masa lokacine fa Asma'u yaushe ma akayi Auren badan haihuwar wuri da ake yiba”.
Lumshe Idanunta hawaye suka zubo kana ta taune lips ɗin ta na kasa tare da faɗin.
“Hmmm Khausar yanzu fa kusan shekara biyu muke nema tunda mun cika shekara ɗaya da wasu watanni da yin Aure har na biyu muke nema”.
Araunane taci gaba da cewa.
“Khausar am har yanzu fa ban haihu ba ko ɓatan wata ban taɓa yiba kuma duk gwaje-gwajen da za'a yi anyi ance lafiyata lau shima Dr bashi da matalan komai”.
Gyaran murya Moddibo yayi kana yace.
“Kiyi haƙuri Asma'u lokacine idan ban manta ba Ummi ta faɗa mana sai da tayi shekara bakwai ana takwas ta samu cikin J ɗina.
Tace mana a randa ta cika Shekara tara ta haifi Jameel dan haka kema ki kwantar da hankalinki, in sha Allahu Babu abinda zai faru sai alkhairi kinji ko My dear”.
Ya ƙare maganar cikin kulawa a matsayinsa na babban yayanta.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Toh shikenan Yah Moddibo yana iya amma dai ku sani a addu'a Allah ya kawo min masu albarka ”.
“In sha Allahu zakmu yita Miki addu'a ”.
Sai kuma ta juya jin Khausar na cewa.
“Kima kwantar da hankalinki daga Yaye in kawo Miki Keyah shikenan zan bar miki ɗanki”.
Murmushi tayi tare da kallon Moddibo tace.
“Allah dagaske Yah Moddibo zaku bani?”.
Zamansa ya gyara tare da cewa.
“Toh me aciki Asma'u ɗana ai ɗan kine, kuma ɗan Khausar ɗan kine”.
Cikin jin daɗi tace.
“Toh Allah ya raya mana shi da Imani ”.
Atare suka amsa da Ameen ya hayyu ya ƙayyum.
Haka dai ranan sukai ta hiransu suna bata ƙarfin guiwa sai karfe 12 suka tafi.

Bayan wata biyar Khausar ta yaye Keyah kana ta kaiwa Asma'u kamar yanda ta mata alƙwari satinsa uku agidan Asma'u ya saba da yaye ya daina tambayar Nono.
Inda ya zamana mafi akasarin zamansa a tsakanin su koda Moddibo ya matsa aje a ɗauko sa Khausar zata danne sa akan abarwa Asma'u.
Bayan Yaye Keyah da wata Uku Allah ya sake baiwa Khausar wani cikin.
Bayan shekara watannin tara da kwana tara ta haifan ɗa namiji aka sa masa sunan Abualeey Youseef ana kiransa da Ayman haka ranan sunansa aka ta biki da hidindimu bayan ta haihu da wata biyu matar Ibraahim ma ta haihu hakama Dija da Asiya da Matar Yah Abba duk sun haihuwa, Ameena ma ta haifi ƴan twagaye duka maza, Samira Sani ma ta haifi yarta mace Masha Allah itama Khausar ta kuma haihuwa Uwar ƴaƴa maza.

Haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya akwana a tashi asarar mai rai.

Keyah yana da shekara takwas Ayman nada shekara shida sun girma sunyi kyau gwanin ban sha'awa sunyi kuɓul-kuɓul dasu zuwa lokacin ƴaƴan ta maza Uku Keyah, Ayman, Haiydar mai shekara huɗu daga nan bata sake haihuwa ba sai yanzu da take rainon ciki na huɗu wanda yama ɗan girma.

Ahankali Khausar dake zaune a babban Falonsu na ƙasa ta ɗan ɗago kanta ganin yaran na sauƙowa daga matakalan Benin Keyah na gaba Ayman na biye dashi Jikinsu sanye da wani Gezner Fari ƙall ƙafafunsu sanye da half covel golden color na maza mai masifar kyau yayin da kansu ke dauke da hula Zhanna bukar blue mai ratsin fari daya dace da kayan jikinsu sosai sukayi nasifar kyau tamkar ka sace su ka gudu.
Anutse Moddibo da shigowar sa kenan daga Fada ya durƙusa tare da buɗe musu hannayensa alamar suzu ya rungumesu.
Da gudu yaran suka rungumesa.
Sai kuma suka maida kallonsu kan Ibraahim kana suka haɗa baki wajen cewa.
“Uncle Ibraahim mun gama”.
Ibraahim dake riƙe da ƴa mace Kyakkyawa mai suna Mifra wacce bisa alamu ƴar sace da sauri Ayman yace.
“Mifra Oyoyo zo?”
Da sauri tazo ya rungumeta sai kuma suka kalli Moddibo dake cewa.
“Ina zakuje?”.
Keyah na Murmushin yace.
“Zamu tafi gidan Ummina”
Kasancewar da Ummi suke kiran Asma'u.
Yana murmushi yace.
“Toh ku gaida Ummin ku” ya ida mgnar yana kamo hannun Haiydar dake ƙoƙarin kwanciya a jikin Khausar yace.
“Tashi kuje kaima”.
Cikin lingwaɓar da kai yace to kama ya miƙe.
Kai suka gyaɗa kana suka fice tare da nufar gidan Asma'u.

Suna shiga gidan suka sameta kwance a falo ta lulluɓe jikinta da bargo tana rawan sanyi cikin sauri da kulawa Keyah ya ɗaura hannunsa kan Fuskarta tare da cewa.
“Ummina meke damunki?”.
Cikin alamun zazzaɓi da rawan jiki tace.
“Zazzaɓi nake ji Keyah”.
Da damuwa atare dashi yace.
“Uncle ya sani?”.
Kai ta girgiza tare da cewa.
“Bai sani ba ɗazun ne ya fara min”
Cikin sauri ya juya gudu kna yace.
“Bari naje na faɗawa Uncle Ibraahim yazo ya ɗauke ki mu tafi asibiti”.
Ya ƙare maganar yana fita dai-dai lokacin kuma Ibraahim ke reverse ɗin motar yana shirin fita cikin ɗan ɗaga murya yace.
“Uncle Ibraahim ka tsaya”.
Ahankali Ibrahim ya tsaya cikin damuwa Keyah yace.
“Ummina bata da lafiya Uncle Ibraahim ka Kaita asibiti”.
Kai ya gyada tare da cewa.
“Toh”.
Kana ya yayi Parking tare da zaro wayarsa ya kira Dr Jameel ya sanarmasa.
Shi kuwa Keyan da gudu ya koma cikin gidan hannunta ya kamo tare da cewa.
“Ummi tashi mu tafi asibiti”.
Ahankali ta gyada kai tare da miƙewa ta gyara mayafinta.
Kama ta tasasu a gaba duka fita.
Tun suna mota ta kira Dr Jameel ta faɗa masa gasu ahanya Ibraahim ya kawo mata yara yanzu zai kawota asibitin nan yake cemata ai Ibraahim ɗin ya gaya mishi.
Chapter 35 · 0% Book details