← Book details Sakayyah Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 38

Sashe 26

Sakayyah Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read

By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAKAYYAH Book 3 PAGE 7*

NA
*Aysha Aliyu Garkuwa*

*Masu son Maganin infection da maganin mata, ku marmatso wannan account no in ne naku ta ciki zaku turo kuɗin ku 0005388578 Jaiz bank AISHA ALIYU GARKUWA, Sai ki turo shaidar biyanki ta WHATSAPP NUMBER'N na 08069423567. akwai sabbin kaya masu zafi suna nan bisa hanya, ki turo kuɗinki a saki cikin lissafi. Kayanen mata masu zafi sadidan daga Chadi akwaisu Garukan daka, gumbunan, Tsumummuka, cida Ciccibi Abodi cida kaza ci da jan nama kwanon ƙasaitacciyar mace biyar sirri, furar mata, gumbar madara Gumbar kolli mai ƙyallin al'khairi gumbar uku al'khairi, gumbar da ba'a baiwa mai kishiya, gumbar riɗi, garin maɗi garin melɗamhi garin ilanwaddihi garin mallaka, tsumin riɗi tsumin tsirtai tsumin kinfi budurwa, tsumin riɗi, tsumin ta baje Sabaya, matsin maliƙi mai masifar matse mace matsin daɗi har maɗiga, mai ɗan kare kyau. Kullacar sirri al'ajabu shu'umar Humra, da duk sauran kan ƙamshi. Haɗin amarya budurwa ko bazawara haɗin mai jego ko uwar gida, akwaisu Available set ɗinmu hawa hawane akwai manya akwai ƙananan, ƙanan daga 40k ne 35k 30k 25k 20k 15k 10k shine ƙarami haɗina na karshe sai kuma haɗin kwanon ƙasaitacciyar mace shi 7k ne shine ƙarshen haɗina kenan... Manyan set ɗin kuma daga 50k 60k 70k 80k 90k 100k ke zaki faɗi haɗin nawa kikeso anyi miki kana kimin bayanin yadda kikeso da matsalarki ni kuwa nasan abinda zan haɗa miki, ina araha kam amman ina hana bashi*

Haka dai yinin ranan Didi suka yini da ita kana suka kwana Asma'u kuwa sai da Dr Jameel ya gama duty inda suka tafi tare da barin Dr Esha.

Washe gari da sassafe Asma'u ta zo hannunta riƙe da wani madaidaicin Basket Dake ɗauke da Warmer masu kyau bisa ga duk kan alama abinci ne tayi kana kafadarta maƙake da waya ta ƙara sa shiga ɗakin alamar waya take yi sai kuma tace.
“Eh Ummi gata nan ma yanzu na shigo”.
Ta ƙare maganar tare da miƙa wa Khausar wayar kana ta ajiye Basket ɗin hannunta tana mai gaida Moddibo dake magana da Dr Jameel.
Khausar kuwa cikin sanyi tace.
“Ummi”
Cike da kulawa Ummi tace.
“Khausar lafiya dai kike jin jikin ki ba abinda yake Miki ciwo?”.
Kai ta gyaɗa kamar tana gabanta tare da cewa.
“Ummi ba abinda. Yake min ciwo fa”.
Cikin jin sanyi da tausayinta Ummi tace.
“Toh Allah ya rabaku lafiya ”.
Tana ɗan lumshe Idanunta ta gyara zamanta tare da cewa.
“Ameen ya Allah Ummu kuyi min addu'a”.
“In sha Allahu muna miki kuma zamu ci gaba daya miki yanzu ma mukayi waya da Momynki tace min yanzun jirginsu zai tashi”.
Juyawa Khausar tayi ta kalli agogon wayanta tare da cewa.
“Yanzu ma ai sun tashi tun da gashi har tara da rabi kuma tara dai-dai ma jirginsu ya tashi”.
Cikin sauƙe numfashi Ummi tace.
“Toh Allah ya kawo su lafiya”.
Ameen ta amsa suna cikin waya da Ummi taga kiran Hajja Nana ya shigo ta wayarta cikin sauri ta miƙa wa Asma'u wayarta kana tayi picking nata takai kunnenta atake muryan Hajja Nana ya ratsa kunnenta tana cewa.
“Khausar”.
Ahankali Khausar tace.
“Na'am”.
Cike da so irin na Kaka da Jika Hajja Nana tace.
“Ya jikin naki?”.
Tana ɗan lumshe Idanunta ta gyara zamanta tare da cewa.
“Da sauƙi”.
Cikin sauke ajiyar zuciya Hajja Nana tace.
“Jiya mukayi waya da Momy take cewa baki jin daɗiba ma tana kan hanya zata zo”.
Kai ta gyaɗa tana kallon Asma'u dake cire warmers cikin Basket tace.
“Eh lafiya lau ba abinda ke damuna Hajja Nana amma wai ance Theater za'a min”.
Cikin son kwantar mata da hankali kana da son sama mata nutsuwa tace.
“A'a kada ki damu ki kwantar da hankalinki ai Theater ba abinda yake yi nima in Sha Allahu da izinin Ubangiji zanyi ƙoƙari in zo”.
Murmushin tayi cikin jin daɗi ta gyara zamanta tare da cewa.
“Allah ya kawo min ke lafiya Allah yasa ki same ni araye”.
Cikin rashin walwala Hajja Nana tace.
“Wani irin magana ne wannan in Sha Allahu ma araye zan sameki kar ki karya min zuciya”.
Murmushi tayi tare da faɗin.
“Toh Allah ya kawo ki lafiya”.
Ameen ya Allah ta amsa kana sukayi sallama.
Kallonta ta mayar kan Moddibo dake riƙe da hannunta cikin rauni yace.
“Kina so ki karya min zuciya ko Minha? wani irin kalma ne kike faɗa haka”.
Ɗaya hannunta ta ɗaura akan nasa tare da cewa.
“Bakomai Yah Mu'allim”.
Dr Jameel kuwa kallon Asma'u dake tsaye gefensa yayi wacce tunda ta cire Warmers cikin Basket bata zauna ba yace.
“Toh ki zauna mana”.
Ahankali tace .
“Toh bari in sa mata abinci”.
Idanunsa ya zare tare da cewa.
“Dear wa yace Miki idan za'a yiwa mutum Theater yana cin abinci ai baza taci abinci ba sai bayan an fito da ita”.
Kallonsa Khausar yau cikin langwaɓar da kai tace.
“Kuma wallahi yunwa nake ji Dr”.
Idanunsa akan Asma'u yace.
“Ki ƙara haƙuri in Sha Allahu ana fito dake ba daɗewa zaki samu ki ɗanci wani abu”.
Rau-rau tayi da Idanunta tare da faɗin.
“Toh shikenan”.
Bayan zuwan Asma'u ba daɗewa Niyna da Innayi suka iso wanda hakan yasa Didi ta samu ta koma gida tayi wanka ta sake shiryawa.

12:30pm dai-dai suka fito da niyyar komawa Asibitin wanda kuma yayi dai-dai da Jirginsu Ummu ya kusa sauƙa hakan yasa tace da Ibraahim dake driving ya wuce da ita Airport kana sai motar Hadimai dake biye dasu wanda sun kai huɗu motar Ajere-Ajere suke tafiya motar Hadimai ɗaya agaba saina su Didi sai kuma sauran ukun abaya ƙarfe 1:05pm dai-dai suka shiga cikin airport Akuma dai-dai lokacin jirginsu Momy yayi Landing.

Bayan Fasinjoji sun fiffito Momy ta fito hannunta riƙe da Raudhat yayinda wani yaro daga cikin ma'aikatan wurin ke gabanta da troling su.
A hankali take tafiya tana ɗan jujjuya ido alamar tana neman ta inda zataga fuskantar da ta sani, sai kuma tayi saurin juyawa jin Raudhat na cewa.
“Oyoyo Didi Yah Ibraahim Oyoyo”.
Murmushi Momy tayi kana tace.
“A'a gasu can ma”.
Ibraahim kuwa sunkuyawa yayi tare da buɗewa Raudhat hannu da gudu tajeta ta rungumesa tare da cewa.
“Ina Addah Khausy?”.
Yana ɗan Sharking ɗin hannunsa acikin nata yace.
“Addah Khausy na asibiti”.
Cike da zumuɗin son ganinta tace.
“Toh mu tafi inganta ina son ganinta ”.
Miƙewa yayi tana riƙe hannunta yace.
“Toh shikenan ”.
Cikin sassarfa Didi ta rungume Momy tare da cewa.
“Momyn Khausar Barka da zuwa”.
Fuska ɗauke da Murmushi Momy tace.
“Barka dai ya mai jikin?”.
Suna tafiya Didi tace.
“A'a Alhamdulillah mai jiki tana can anata hira da ita amma yanzu nan da minti arba'in za'a shiga da ita sai muyi ƙoƙari mu tafi asibiti kafin a shiga da ita”.
Momy ta gyaɗa kai tare da cewa.
“Toh shikenan”.
Daga nan suka shiga motoci Madadin su wuce gida kai tsaye asibiti aka wuce dasu.

Dai-dai lokacin kuma Lalla Khadijah da Rahma ne da Asma'u ke tare da Khausar, cikin kulawa Lalla Khadijah ke kallon Khausar ɗin jin yadda tayi mgnar a yunwace.
“Ayyah Rahma kije ki tambayi Dr Jameel, zan iya shan tea ne”.
Cikin kula Rahama tace.
“Ai ɗazuma naje Lalla Khausar cewa yayi ki ɗan ƙara haƙuri”.
Gyara zama Lalla Khadijah tayi tare da cewa.
“Kiyi haƙuri ko Khausar ba komai zuwa yamma dai zaki samu kici wani abu”.
Ɗan kwaɓe fuska tayi tare da kallon Asma'u dake cewa.
“Toh ni bari inje in kira Dr suzo su shiga suyi mata mana ta samu taci abinci”.
Ta ƙare maganar tana fita.

Su Momy kuwa da Didi tafe suke suna hirarsu, duk da dai duk karfin hali suke.
Raudat kuwa sai surutu take zubawa Ibraahim.
Chapter 26 · 0% Book details