Sashe 24
Sakayyah Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nan take suka tafi asibiti kafin su isa ma Already an shirya komai.
Suna isa aka karɓesu aka shirya komai kana akayi duk kan abinda ya kama na gwaje-gwaje.
Bayan an gama gwaje-gwaje Dr Jameel ya fito zuwa lokacin kuma ruwan dake zuban nan zubansa ya ƙaru sosai shigowa yayi kana ya kalli Niyna ya kalli Didi kallonsa Didi tayi kana ta miƙe tabi bayansa zuwa office ɗin sa tace.
“Jameel ya akayi?”.
Ƙofan ya ɗan tura tare da zama kan kujera kana ta zauna gefe sai kuma Moddibo dake biye dasu yazo ya zauna gefen Didi gyaran murya Dr Jameel yayi tare da kallon Didi yace.
“Kinga Didi tun cikin nan yana da wata bakwai munyi Sikaynin komai lafiya sannan ko kwanan nan bai daɗe ba still munyi Sikaynin komai lafiya”.
Cikin bugawar zuciya Moddibo ke kallonsa cikin sauƙe numfashi ya cigaba da cewa.
“Kuma ko yanzu ma Alhamdulillah zaman yaro lafiya to Amma kuma kinga yanzu ruwa yana ta zuba mata kuma ba alamun naƙuda tare da ita”.
Numfashi Didi ta sauƙe tare da cewa.
“A wannan Normal ne in dai wannan ne ruwan zaƙine”.
Kai Dr Jameel ya jinjina kana yace.
“Eh nima ina ga kamar Normal ne?”.
Cike da gamsuwa ta gyaɗa masa kai tare da faɗin.
“Eh dan nima wani lokaci yana kai kusan sati kafin naƙuda yazo ya tashi idan na ƙuda ya tashi kuma baya wuce awa ɗaya ko biyu shikenan na haihu”.
Cikin rauni da tarin tausayi Moddibo ya juya ya kalleta yace.
“Didi Amma ba matsala?”.
Kai ta gyada tare da cewa.
“In sha Allahu ba matsala wannan ana ce mishi zaƙi zaƙine yake zuba”.
Numfashi Dr Jameel ya fesar kana yace.
“For now dai zaƙine yake zuba amma yanzu zaku tafi gida, tunda ba haihuwar bane amma kullum da daddare kafin ku kwanta azo in duba ta saboda kada ruwan ya canza ya zama wanda yaro ke rayuwa a cikine ke zuba, amma for now ba matsala”.
Hararansa Moddibo yayi tare da faɗin.
“Toh munji”.
Murmushi Dr Jameel yayi tare da cewa.
“Ha'a Yayanmu laifin me nayi kuma?”.
Murmushi Didi tayi daga nan dai suka tattara suka koma gida.
Haka Khausar suka yini da Asma'u sai dai har zuwa lokacin ruwan nata zuba sai dai ba sosai yake zuba ba, da daddare bayan sunje asibiti Dr Eshaa ce ta duba ta tace in sha Allah babu wata matsalar komai kuma ba haihuwa bace...
Kwance Khausar take agefen Moddibo yayin da hannunsa ke kan cikinta yana tofa mata addu'oi.
Ahankali ta juya ta kallesa tare da cewa.
“Yah Mu'allim!”.
Idanunsa dake lumshe ya buɗe kana yace.
“Na'am Minha ya akayi?meke damunki meke kiki ciwo”.
Ya ƙare maganar cikin tsananin kulawa, tausayi, jin ƙai.
Kai ta girgiza tare da faɗin.
“Babu abinda ke yimin ciwo amma Yah Mu'allim dan Allah don darajar Annabi ka cewa Momyna tazo mana”.
Cikin sauri ya miƙe ya zauna ya kalleta tare da cewa.
“Meyesa kika ce haka Minha?”.
Kai ta girgiza asanyaye tace.
“Ni dai kawai nafi so Momyna tazo ina son ganinta kaga bata taɓa zuwa ba kuma ina so in na haihu tazo kaga ga abin na zuba kuma Dr Jameel yace in sha Allah nan da sati ɗaya zan haihu kaga ai tazo yafi”.
Kai ya jinjina kana yace.
“Amma dai ba abinda yake Miki ciwo ko?”.
Tana riƙe tafin hannunsa acikin nata tace.
“Um bakomai kawai ina so Momyna tazo kuma dan Allah in zata zo taxo min da Raudhat in yaso in na haihu kafin suna Hajja Nana ma tazo kaji ko Yah Mu'allim”.
Cikin sanyi yace.
“An gama Minha in Sha Allahu Momy za tazo”.
Cikin jin daɗi tace.
“Yaushe za'a faɗa mata?”.
Kallon haɗeɗɗen agogon dake ɗaure atsintsiyar hannunsa yayi ganin 10pm yayi ya sanya shi sauƙe numfashi yace.
“Kinga karfe goma tayi sai gobe zan faɗa mata”.
Marairaice fuska tayi tare da cewa.
“Um-um Yah Mu'allim a faɗa mata yanzu mana”.
Kai ya girgiza kana yace.
“Minha idan na faɗa mata yanzu kinga dai lafiyarki lau, toh Amman in taji zatayi zaton baki da lafiya ne karshe muzo mu hanata bacci”.
Idanunta ta narkar acikin nasa tare da cewa..
“A'a Yah Mu'allim baza ta tsorata ba ai zanyi waya da ita zata fahimta”.
Sake kallon agogo yayi yace.
“Mu dai bari har sai da safe”.
Kamar za tayi kuka tace.
“Ni dai Um-um mu faɗa mata yanzu”.
Ganin yanda ta damu yasa yace.
“Toh shikenan”.
Ya ƙarashe Maganar tare da ɗaukar wayarsa yayi dearlin number mommy.
A can Nigeria kuwa dai-dai lokacin Momy ce tare da Amina zaune a falonta cikin sanyi Amina tace.
“Momy kinji ɗazu an kirani ko?”.
Kai Momy ta gyaɗa tare da cewa.
“Eh Amina naji".
Cikin fesar da numfashi da kuma yanda nutsuwa da nadama ya baibaye rayuwarta tace.
“Kin san waye ne ya kirani”.
Cikin sanyi gami da rauni ta gyara zamanta tare da faɗin.
“Baban Samira Sani ne fa yazo wajena”.
Da mamaki Momy tace.
“Kai haba dai?”.
Araunane ta gyaɗa kanta tare da cewa.
“Wallahi”.
Ajiyar zuciya Momy ta sauke tace.
“Lafiya dai?”.
Kanta ta sunkuyar ƙasa idanunta na ciko da ruwan hawaye tace.
“Wai cewa yayi yana sona zai Aureni”.
Shiru Momy tayi kana ta ronƙofar da kanta kafin sai kuma ta ɗago kanta ta kalleta.
Amina kuwa cikin sanyi ta cigaba da cewa.
“Momy nikam kuma da zama hakan nan tunda ya sanni kawai zan Aureshi kawai yafi min tunda tuntuni na gama iddah kuma babu wanda yake zuwa wajena”.
Cike da tausayinta Momy tace.
“In dai har kin gamsu kinga zaki Aureshi ai babu laifi, tunda dama mun sanshi mutum ne mai mutunci da kamala da daraja”.
Tana wasa da yatsun hannunta tace.
“Hakane kam Momy kuma ma kinga ya bada hujjan cewa zamu zauna cikin aminci, tunda dama nida Samira mun saba zanje in zauna in maye mata gurbin Mahaifiyarta sannan kuma muyita mata addu'a Allah ya fito mata da mijin Aure na Alkhairi ”.
Kai Momy ta jinjina cike da gamsuwa tace.
“Toh shikenan Amina Allah ya tabbatar da abinda yafi Alkhairi ”.
Ahankali tace.
“Dama shine nace bari na faɗa Miki saboda ki faɗawa Abbana, nikam na yarda shiɗin in Aureshi dama Momy Ni yanzu waye zai kalleni ya Aureni in ba tsohon ba?”.
Cikin kwantar mata da hankali Momy ta ɗan muskuta tare da cewa.
“Bakomai Amina in Sha Allahu zan faɗawa Abbanku Allah kuma ya sanya Alkhairi kuma ai mutum ne mai mutunci”.
Cikin sanyi Amina tace.
“Ameen ya Allah”.
Suna cikin hiran ne kira ya shigo wayarta da mamaki tace.
“Toh Moddibo kuma”.
Sai kuma ta amsa kiran ta kai kunnenta tare da faɗin.
“Assalamu Alaikum ”.
Anutse Moddibo yace.
“Wa'alaikum Salam Barka da dare Momy kina bacci na tashe ki ko?”.
Murmushi tayi tare da faɗin.
“A'a idona biyu muna hira da Amina ce ma”.
Kai ya gyaɗa yana shafa cikin Khausar yace.
“Masha Allah”.
Sai kuma yayi shiru cike da kulawa tace.
“Lafiya kuwa Moddibo?,Me yake faruwa faɗa min mana?”.
Kansa ya sunkuyar ƙasa tare da ɗagowa ya kalli Khausar sai kuma ya maida hankalinsa kan wayar yace.
“Momy Khausar ce kin san yau tun da safe”.
Sai kuma yayi shiru ya rasa ta ina zai fadi maganar.
Ganin haka ne yasa Khausar ta karɓi wayar tasa akunnenta tare da faɗin.
“Momy”.
Cikin sauƙe ajiyar zuciya Momy tace.
“Na'am Mamana lafiya kuwa?”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Lafiya lau Momy?”.
Tana ɗan jingina da jikin kushin momy tace.
”Toh me yake faruwa?”.
Tana gyara zamanta tace.
“Bakomai fa Momy kinga yau munje asibiti an duba ance ba matsalar komai, kuma in sha Allahu nan da sati ɗaya ko kwana biyar zan haihu shiyasa nake so ki tambayi Abba in ya barki kizo”.
Da damuwa Momy tace .
“Amma dai kin tabbatar Babu komai”.
Idanunta ta lumshe tare da buɗe su akansa tace.
“Allah Momy ba komai kawai dai ina so kizo ne kuma dan Allah Momy kizo da Raudhat yanzu ki tura mana hoton Passport ɗinki amiki booking”.
Murmushi Momy tayi tare da cewa.
“Da gaggawa haka Mamana?,Ba dai abinda kike ji?”.
Kai ta gyaɗa tare da faɗin.
“Bafa abinda nake ji”
Cikin ɗan radaɗine Mommy tace.
“Ok toh shikenan zan faɗawa Abbanku idan ya amince zanzo, tunda ga Amina da sauƙi zata zauna da ƙannen ku kafin mu dawo”.
Tana ɗan lumshe Idanunta tace.
“Toh shikenan Momy ina Aminan?,Ki bata mu gaisa”.
Momy na ƙoƙarin miƙa wa Amina wayar tace.
“Gata nan”.
Jin Amina ta karɓi wayar Khausar tace.
“Amina ina yini”.
Asanyaye Amina tace.
“Lafiya Khausar ya gida ya labarin Addah Asiya ”.
Khausar na jinginar da kanta kafadarta Moddibo tace.
“Munyi waya ma tace kwanan nan zasu zo hutu akwai bikin abokinsa da za'a yi zasu zo”.
Ahankali Amina ta gyara zaman wayar akunnenta tare da cewa.
“Allah ya kawo su lafiya ya jiki?”.
“Alhamdulillah”.
Cewar Khausar tana lunshe idanu.
Cike da kulawa Amina tace.
“Toh Allah ya raba lafiya”.
Daga nan sukayi sallama.
Nan take Momy ta mike taje ta faɗawa Lamiɗo ba gardama Lamiɗo ya amince tare da yi mata fatan Alkhairi kana ya fara yi mata booking ɗin tafiya cikin ikon Allah ya ga nan da kwana huɗu akwai jirgin da zai tashi daga Abuja zuwa Morocco direct cikin Rabat zai sauƙa nan take yayi mata komai da komai a online kasancewar ranan juma'a ce kuma jirginsu zai tashi ranan Laraba