← Book details Sakayyah Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 38

Sashe 30

Sakayyah Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ga masu buƙata ga number' wayata wanda nake whatsApp dashi 08069423567 kimin mgn ta whatsApp in har kin tabbatar kin shirya saya mu dai-dai ta, kayana ba ƙanana bane, shiyasa bana harkan karanta, muddin kinsan baki shirya sayaba Please kada kiyi min mgn ki bari sai kin shirya kuɗinki a hannu, ba ina nufin kayana bana talaka bane, no akwai ƙananan set na masu karamin karfi, banson aimin mgn a ɓatamin lokacin aiyukana a shirme baki shiryaba. Shine karantan da bana so.
0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU. In kin shirya ga number ta ga kuma account number ta wanda in mun gama mgn zaki turo kudin ki, kana insa miki kaya a mota, duk ƙasar da kike kayana zaije gareki, amman fa in kinada dalilin zuwan nasune🤝🏻sayan na gari meda kudi gida.

GARKUWAR MA'AURATA

Tana wani sassayan tari, wanda take ta son danneshi, cikin sauri suka ƙara sa cikin ɗakin da sauri Dr Jameel yace.
“Ha'a ya dai?”.
Momy ce ta ɗago kanta tare da cewa.
“Kamar ƙwaruwa tayi”.
Cikin tsoro gami da damuwa Moddibo ya kalli Dr Jameel kana yace.
“Jifa tari take ba matsala ko?”.
Kai Dr Jameel ya girgiza tare da faɗin.
“A'a ba matsala bari nasa akawo mata wani magani tasha tarin zai bari”.
Ya ƙare maganar tare da kiran Line-line dake cikin wayar ya kira Pharmacy ya faɗa musu su kawo maganin jim kaɗan Norse ta kawo maganin karɓa yayi ya bata tasha cikin ikon Allah atake tarin ya bari.
Sai alokacin ta samu nutsuwa numfashi ta fesar kana ta maida kallonta kan Abualeey tare da cewa.
“Abu ina yini”.
Cike da kulawa yace.
“Lafiya lau ya jiki?”.
Ahankali tace.
“Da sauƙi ”.
Kai ya gyaɗa tare da faɗin.
“Masha Allah Allah ya raya abinda aka samu”.
Karɓan Jaririn yayi tare dasa mishi albarka kana ya miƙawa Waziri da Galadima dai-dai lokacin kuma kira ya shigo wayar Khausar Momy anutse ta duba ganin sunan Hajja Nana yasa ta ɗauka muryanta cike da farin ciki tace.
“Hajja Nana Alhamdulillah anyi Theater ancire ɗa namiji”.
Cikin jin daɗi da sauke ajiyar zuciya Hajja Nana tace.
“Alhamdulillah amma tana lafiya ko?”.
”Eh lafiya lau gata nan ma”.
Cewar Momy na miƙa wa Khausar wayar karɓa Khausar tayi suka gaisa cike da farin ciki Hajja Nana tace.
“Ƴar tsele da zaki kasheni azaune”.
Murmushi Khausar tayi cikin rashin jin karfin jikinta tace.
“Yaushe zaki zo?”.
Fuska ɗauke da farin ciki Hajja Nana tace.
“Kwanan nan in sha Allah kafin ayi suna”.
Murmushi Khausar tayi tare da maida kallonta kan Moddibo da idanunsa ke kan Jaririn tace.
“Ayiwa Hajja Nana shiri in Sha Allahu tana kan hanya zata zo”.
Kai ya gyaɗa mata tare da cewa.
“In sha Allahu”.
Akuma dai-dai lokacin Dija da Yah Aliyu suka shigo Murmushi Khausar tayi tare da cewa.
“Dija”.
Cike da farin ciki Dija tace.
“Na'am Khausar ai mu bamu sani ba Khausar baku faɗa mana ba”.
Still da Murmushi afuskarta tace.
“Kiyi haƙuri Dija gaba ɗaya abin ne yazo min atsorace”.
Dariya Yah Ali yayi tare da faɗin.
“Raguwa gaba ɗaya kin gigice kin gigita bayin Allah”.
Langwaɓar da kai tayi kana tace.
“Hmmm ba dole inji tsoro ba Yah Ali abinda ance wasu da yawa idan an musu kafin afito dasu ta can suke wucewa”.
Murmushi yayi tare da cewa.
“A'a ke kam in Sha Allahu kina nan sai kin kawo wasu ƙannensa goma sha ɗaya sun zama Dozen”.
Idanunta ta zaro tare da faɗin.
“Goma sha ɗaya”.
Baki ɗaya ɗakin suka sanya dariya.
Raudat dake zaune gefen Asma'u ta ƙyalkyale da dariya kana tace.
“Addah khausy idan kika haifi Dozen sai ki bani biyun saman na riƙa kulawa dasu kar suyi Miki yawa ai Yah Moddibo zaku bani ko?”.
Ta ƙare maganar tana kallon Moddibo kai Moddibo ya gyaɗa yana Murmushi.
A ranan haka suka yini suna kula da ita.

Bayan sunyi kwana uku aka sallame ta suka koma gida.
Haka Didi da Momy suka cigaba da kula da ita suna bata kulawa na musamman...
Washe gari da safe Misalin ƙarfe 7:30 Asma'u ta zo zaune ta samu Lalla Khadijah, Rahama, na zaune kan lallausan Darduma Yayin da Didi,Momy,Innayi ke zaune gefe ɗaya Hajja Nana kuwa na gefen Khausar da Moddibo dake riƙe da Jaririn yana masa addu'a kana su kuma suna hira.
Ahankali Asma'u ta ɗago fuskarta ɗauke da Murmushi ta miƙa wa Khausar wayarta tare da cewa.
“Kalli wani special abu dana ajiye Miki wanda nake da yaƙinin sai kinyi min kyauta na musamman”.
Ɗan ware idanu Khausar tayi tana kallon Rahama dake cewa.
“Aikuwa dai Addah Asmeey muma dake gefe muna sa ran samun khauta”.
Dariya Khausar ta sanya kana tace.
“Aikam dai zanso gani”.
Ta ƙare maganar tana playing video
Da sauri ta zaro Idanunta waje ganinta kwance kan gado tana surutai.
Moddibo kuwa wani Amintaccen Murmushi ya saki ganin yanda ta zaro Idanunta waje sai kuma tayi saurin ɗaga kanta cike da kunya jin yanda suka ƙyalƙyale da dariya cikin tura baki ta kalli Asma'u tare da cewa.
“Asma'u Ni ko?,Aikuwa kin ci bashi sai na rama”.
Ta ƙare maganar cike da kunya ganin yanda suke maimaita maganar.
Asma'u kuwa Gwalo Asma'u tayi mata tare da cewa.
“Aikuwa sai dai ki rame yarinya dama can abinda ke Ranki kika faɗa”.
Khausar kuwa juyawa tayi jin Hajja Nana na cewa.
“Yoh ai gaskiya Asma'u ta faɗa ke da wannan mijin naki duk ba kunya ne daku idan ke baki cikin hayyacin ki kika faɗa ai shi yana sane bare keɗin ma kina sane”.
Rau-rau da idanu Khausar tayi ta shiga bubbuga ƙafa daga zaune tace.
“Didi kiji fa abinda Hajja Nana ke faɗa wai bani da kunya”.
Murmushi Didi tayi tare da faɗin.
“Rabu da Hajja Nana am Khausar ɗina kina da kunya sosai ai bada sanin ki kikayi ba”.
Momy kam Murmushi kawai takeyi.
Daidai lokacin Jakadiya ta shigo tare da sanarwa Didi tayi baƙi ƴan Barka.
Miƙewa Didi tayi kana tace.
“Toh ganan zuwa”.
Sai kuma ta kalli Momy dake cewa.
“Mu tafi”.
Atare Didi Momy Innayi,Niyna suka fice.
Kallon Rahamah kalla Khadijah tayi kana tace.
“Rahama muje ki tayani haɗa Alawar Madara da gullisuwa tun jiya naso yi kuma ina zirga-zirga”.
Murmushi Rahama tayi tare da miƙewa Lalla Khadijah kuwa har taje ƙofa ta juya ta kalli kana tace.
“Ƙanwata kema zo muje”.
Kai Asma'u ta gyaɗa tare da miƙewa suka fita.
Falon ya rage daga Khausar, Moddibo sai Hajja Nana da itama ta miƙe ta fita falon.
Cikin shagwaɓa Khausar ta kalli Moddibo tare da narke fuska kana ta tura baki tace.
“Yah Mu'allim”.
Murmushi yayi kana ya kwantar da jaririn ya janyota jikinsa bakinsa ya kai saitin kunnenta yace
“Na'am Minha Viddaaaa ya akayi?”.
Ya ƙarashe yana jan sunan.
Cike da shagwaɓa tace.
“Jifa yanda na saki baki naita faɗan magana gabansu Momy da Didi kuma baka hanani ba”.
Murmushi yayi yana shafa bayanta yace.
“Ya za'a yi in hanaki fallasa min sirrin dake Ranki?,Taya kike tunanin bakina zai iya dakatar da zinaren kalaman da suke fitowa daga bakinki suna ratsa kogon zuciyata?,Kin kuwa san farin ciki da shaukin dana kasance alokacin?”.
Ya fesar da sanyayyan numfashi mai cike da zallan so da shauƙi yace.
“A lokacin ji nake tamkar ina yawo a gajimare ji nake tamkar nafi Mazan duniya Sa'a da samun Nagartacciyan mace irin ki kin nuna min so tun baki san menene so ba shin mai zanyi in biyaki”.
Cikin wani irin yanayi na musamman tace.
“Ka ƙaunaceni ka kuma soni fiye da yanda nake son kaina kada ka haɗa ni da kowa atare da kai idan kayi min haka kaga yimin komai Yah Mu'allim”.
Ahankali ya ɗago kanta tare da ɗaura lips ɗin sa asaman nata yashiga kissing ɗin ta...

Alhamdulillah zuwa yanzu jikinta yayi ƙwari bazama ace Thearter aka mata ba kullum Asma'u da Dija anan suke yini ana I gobe suna Dr Zakariyya, Asiya Hajja Nana, Abban Jameel, Lalla Hafsat suka zo.
Chapter 30 · 0% Book details