← Book details Sakayyah Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 38

Sashe 19

Sakayyah Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bayan kwana biyu Moddibo ne zaune akan sallaya gabansa ɗauke da starm da Kur'ani ke kai, bayan ya dawo daga sallar Asbah yayin da Khausar ke gefensa ahankali ta ɗago kanta jin ringing ɗin wayarta kallon Moddibo tayi kasancewar ya fita kusa da wayar da ido ta mishi alamar ya dai wake kira?.
Juyawa yayi kana ya kalli screen ɗin wayar sai kuma ya kalleta yace.
“Asma'u ce”.
Da ɗan sauri ta miƙe ta karɓi wayar tare da amsawa takai kunnenta tare da cewa.
“Hello Besty na kiyi haƙuri laifin yayanki ne. Yah Mu'allim ne ya hanani zuwa wai in barku ku gurji amarc...
Sai kuma tayi shiru ba tare da ta ƙarasa mgnar ba, sabida jin muryan Asma'u a disashe kana yayi sanyi alamun taci kuka ta godewa Allah cikin raunin murya tace.
“Khausar”.
Da damuwa Khausar ta ɗan jingina bayanta da kafaɗar Moddibo kana tace.
“Subhanallah Asma'u meke faruwa”.
Cikin rauni da zubda hawaye Asma'u tace.
“Khausar zan mutu dan Allah ki cewa Yah Mudibbo kuzo ki ɗaukenu, wannan mutumin mungu ne ya kasheni ”.
Dariya mai sauti Khausar ta fashe dashi har tana ɗan bubbuga kanta da jikin kafaɗar Moddibo kana tace.
“Ya kashe ki kuma kike magana?”.....

By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAKAYYAH Book 3 PAGE 5*

NA
*Aysha Aliyu Garkuwa*

*WOHOHO IN KAJI ANA ƘI GUDU TABBAS SA GUDU NE BEZO BA*

_Ina kuke Ma'aurata masu sha'awar ganin sun zama taurari kuma fitilu a idanun mazajensu Uwar gida,Amarya,Tsakar gida,hadda tan kaɗen gida Shararriya kuma ƙasaitacciya data saba kawo muku nau'ikan sirrin sahihan magungunan ma'aurata wato *AYSHA ALIYU GARKUWA* Garkuwar Marubuta ayau ma ta dawo muku da Ingantattun magungunan mata masu kyau da inganci domin gyara kanki ki zamto tauraruwa a idanun mijinki...Muna da Ingantattun Abubuwa kamar haka_ :_Munada Garin mallaka, garin maɗi, garin Hakkin mayi, garin ɓelɗamhi Garin ilanwaddihi, Gumbar da ba'a baiwa mai kishiya, Gumbar kolli mai kellin al'khairi, Gumbar Riɗi wato 3 in 1, Gumbar makwaranyi, Masin Maliƙi mai masifar ƙarfi da matse mace, ka masin Daɗi har Maɗigan Akwai, kwanon ƙasaitacciyar mace mai masifar kyau da ratsa jiki da samar da inƙantacciyar ni'ima yanada abubuwa masu kyau haɗinsa, Zumar goron tula mai masifar kyau, tsumin dabino, mai ratsa jiki, tsumin Riɗi mai ƙarfi, Furar Mata mai tsastsafo da ni'imantaccen damshi, Cida kaza, Ciccibi Abodi, Tsumin Ɓaure, tuwon ɓauren, kana akwai maganin sanyi sadidan, da dai sauransu...Se kuma fannin ƙamshi kasance da Shu'umin ƙamshi wanda ze gigita ƙwaƙwalwar Oga tare da jin ko wacce mace bata kaiba...._ _Shin ko kina da labarin Miskilinci da ƙasaitar Rayyan Naaan amma lokaci ɗaya ya zamto zautacce sakali akan soyayyar Jannart bakomai Jannart ta riƙe ba face sirrinkan gyara da kuma shu'uman humran da kulaccar sirri na Aysha Aliyu Garkuwa(Tubali) tabbas taga tasirin haka domin Naanunta ya zame mata tamkar bawa_
_Shin ko kinsan sihirtaccen haɗin da Aysha ke sha kenan ta zamto tauraruwa a idanun Hamma Yusuf(Miwasmiti)...Tabbas Mahmud ya zamto zautacce kuma makaho akan sauyayyar Bazawara wato khadijarsa duk da kuwa gashi da budurwa(Namiji Baya Kaɗan) ko kinsan hakan nada alaƙa da amfani da sahihan maganin da kuma shu'uman humran Aysha Aliyu Garkuwa??.Nasan ba zaka ku manta da irin kima da kuma darajar da Aysha ke dashi acikin Idanun Sheik Jabeer ɗin ta duk da kuwa shekaru sunja anma jinta yake tamkar budurwa 'yar sha bakwai(Garkuwa) sirrin hakan na tare da Ingantattun kuma sahihan magungunan Aysha Aliyu Garkuwa Wato Garkuwar Marubuta da kuma Ma'aurata na tabbata kunsan da cewa basirarta ba'a iya rubutun littafi ya tsaya ba hadda inganta rayuwar ma'aurata ta hanyar kawo musu Nagartattun abubuwa Ga duk wacce ta shirya saya seta tuntuɓi number ta 08069423567 muna iya tura kayan mu aduk inda kuke afaɗin Nigeria harma da ƙetare Dan Allah 'yar uwa idan baki shirya siyaba kada kiyi min magana muɓatawa kanmu lokaci...._

🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🥰😘sai.kunzo. sayan na gari maida kuɗi gida,

Cikin dariya sosai ta ƙarshe Maganar, sai kuma tayi saurin sa tafin hannunta na dama ta rufe bakinta, sabida jin yanda muryan Asma'u ya fito tana shesh-sheƙa.
Tare da saki sanyayyan kuka tana cewa.
“Dariya ma kike min Khausar?,Baki san halin da nake ciki bane wallahi zai kashe ni fa!”.
Da sauri Khausar ta gyara zamanta cike da tausaya wa tace.
”Kiyi haƙuri My Besty babu abinda zai kashe ki in Sha Allahu, wahala ce dai anshata kuma in sha Allah baza amaimaita irin taba”.
Sai kuma ta kalli Moddibo da idanunsa ke lumshe yana motsa laɓɓansa amma bisa duk kan alamu yana sauraron tattaunawar wa tasu tace.
“Kin manta nima lokacin haka kike ta min dariya idan kin tuna alokacin har ce miki nayi kema kwana nawa ya rage Miki amma kika cigaba da dariyar ki”.
Araunane Asma'u taja dogon numfashi tare da cewa.
“Baza ki gane bane Khausar Ni ba maganar dariya nake Miki ba Ni dai yanzu dan Allah ki daina yimin dariya,yanzu ina Yah Moddibo yake ki bashi wayar”.
Cikin tausayinta da kuma yanda take jin shesh-sheƙan kukanta Khausar tace.
“Menene? me zaki ce masa?”.
Asanyaye Asma'u tace.
“Ni dai dan Allah ki bashi wayar”.
Kai Khausar ta gyaɗa tare da cewa.
“Toh”.
Kana ta sanya wa Moddibo wayar akunnensa.
Ahankali ya juya ya kalleta kana ya ɗaura hannunsa akan nata ya riƙe wayar.
Asma'u kuwa da muryanta ya gama dishewa da kuka tace.
“Yah Moddibo”.
Ahankali ya ɗan runtse idanunsa yana mai jin tausayinta, rauninta, damuwarta, domin jinta yake tamkar jininsa tsatsonsa yana jinta tamkar yanda yake jin Rahama Aransa, cikin sanyi da tausasawa yace.
“Na'am Asma'u me ya faru? Me yake damunki?”.
Kuka ta fashe dashi cikin dashewar murya tace.
“Yah Moddibo bani da lafiya ni dan Allah kazo ka ɗaukeni”.
Cikin fesar da numfashi Moddibo ya ɗan gyara zamansa tare da cewa.
“Kiyi haƙuri Asma'u, Kwantar da hankalinki ki daina kukan ki faɗa min meke damunki!?,Mene matsalar ki?”.
Cikin son danne kukan dake taso mata tace.
“Bani da lafiya zazzaɓi nake ji ƙafafuna, bayana, kaina, duk ciwo suke min”.
Ahankali yace.
“Toh kiyi haƙuri Yi shiru yanzu me kike so?”.
Tana shesh-sheƙan kuka tace.
“So nake ka kawo min Khausar kuma kaima kazo”.
Kai ya gyaɗa tare da faɗin.
“Toh kiyi shiru in Sha Allahu zan kawo miki ita”.
Cikin muryanta da bai fita sosai tace.
“Yanzu fa?”.
Kai ya gyaɗa mata kamar tana gabansa yace.
“Eh in Sha Allahu yanzu”.
Ya ƙarashe maganar yana mai jin matsanancin tausayinta kasancewar yasan wanene Dr Jameel mutum ne mai shegen fitina kana yasaba neman mata ya saba ko yaushe rayuwarsa da mata sannan yasan tunda sukayi maganar Aurensa da Asma'u ya daina neman mata, tun lokacin yake fama da Azumi yasan ya tara fitinar da tafi ƙarfinsa shi kansa shiyasa yake jin tausayinta dan ya san ya mata wawan riƙone.
Cikin sanyi ya fesar da numfashi kana ya cigaba da cewa.
“Kiyi haƙuri ki share hawayenki kuma ki daina kuka, kukan da kike yi zai sa kiki zazzaɓi da ciwon kai”.
Kai ta gyaɗa kamar yana ganinta ta share hawayenta tare da cewa.
“Toh ka bawa Khausar ”.
”Toh”.
Yace kana ya miƙawa Khausar wayan tare da faɗin.
“Tashi, tashi ki shirya mu tafi”.
Khausar kuwa cikin sanyi da tarin tausayin aminiyar nata tace.
“Asma'u kiyi haƙuri ganin nan zuwa ki daina kukan dan Allah ”.
Ba tare data tsaida kukan nata ba tace .
“Nikam dan Allah kizo kuma idan akwai magani ki kawo min”.
Murmushi Khausar tayi kana ta kalli Moddibo da fuskarsa ta nuna damuwa numfashi ta fesar tare da cewa.
“Kamar ya in kawo kiki magani Asma'u!,Keda kike tare da Likita?,Ai ke kece gidan magani”.
Sabon kuka ta fashe dashi kana tace.
“Baza ki gane bane yanzu ma yamin allurai sannan yaban magunguna kuma duk nasha”.
Ajiyar zuciya Khausar ta sauke tare da cewa.
“Toh kiyi haƙuri in Sha Allahu zaki ji sauƙi ”.
Kai ta gyaɗa tare da katse kiran kana ta mike suka fito.

A Corridor sukayi kiciɓis da Innayi wacce bisa alamu taje ta gaida Didi ce ta dawo cike da kulawa ta kallesu kana tace.
“Lafiya ina zaku je?”.
Kallon Khausar Moddibo yayi kana cikin sauri yace.
“Zamu je tayi Anti nytel ne”.
Kai Innayi ta gyaɗa tare da cewa.
“Toh shikenan amma da sassafe haka?”.
Yana kallon Khausar data ɗan lumshe Idanunta yace.
“Eh”.
Kai ta jinjina kana tace
“Ok kuma naga wancan zuwan nata da daddare kuka je wannan kuma da sassafe?”.
Yana riƙe hannun Khausar acikin nasa suka nufi hanyar fita kana yace.
“Eh”.
Kai ta gyada tare da shigewa ta nugi kitchen.
Nan ta samu Hadimai da already sun fara girki.

Dr Jameel ne zaune dafe da kansa fuskarsa ɗauke da Murmushi.
Cikin kasala da alamun rashin wadataccen bacci ya muƙe a saɓule jin ana knowking ɗin ƙofar.
Chapter 19 · 0% Book details