← Book details Sakayyah Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 38

Sashe 5

Sakayyah Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duna shiga Khausar tayi saurin komawa bayan Modibbo tare da riƙe hannunsa gama, cikin rawan jiki ta ɗago hannunta tana nuna wasu ƙattun mutum biyu da babu alamun imani tare dasu, shiyasa aka ɗan waresu gefe suna zaune sai kuzurai suke.
Cikin tashin hankali gami da tsanarsu ta fashe da kuka murya narawa tace.
“Ga sunan wallahi Yah Mu'allim sune, sukayi ta bin motarmu da Yah Jameel randa aka sace shi, kuma sune suka je Jauro Yaya sannan kuma sune suka je bakin Makarantar.
Wallahi tallahi sune suka bibiye mu aranan da muka rabu da Yah Jameel na ƙarshe har da muka tsaya a suma suka tsaya”.
Cikin Tsananin tsana takaici da ƙunar rai Modibbo ke binsu da wani irin kallo mai nuna jin zafin illar da sukayi mishi.
Shi kuwa Sheikh Jabeer nan take yasa aka killace su waje na musamman da kansa ya tsananta bincike Matsayin sa na SS mai zaman kansa wanda yasan kansa da aikinsa da ƙirewa.
Bisa jagorancin Jalal yasa aka musu ɗan banzan bugun da ya karya ƙarfin zuciyarsu.
Kana yacewa su Modibbo su shiga.
Cikin tsaresu da ido ya nuna musu Khausar tare da cewa.
“Kunsanta?”.
Agalabaice suka ce.
“Eh mun santa itama an bamu kwangilar kashe ta”.
Aruɗe ta zare ido kana ta ɗaura hannunta aƙirji tace.
“Kasheni kuma nima? me nayi muku”.
Kai Sheikh Jabeer ya jinjina kana ya nuna Moddibo dake binsu da wani irin kallon tsana gaba ɗaya jikinsa rawa yake shi kuwa Sheikh Jabeer cikin sanin makamar aikinsa yace.
“Wannan fa kun san shi”.
Kai na farkon ya gyaɗa tare da faɗin.
“Eh ai dama shi tare aka bamu kwangilar karshe sa da Malam Jameel”.
Zama sheikh Jabeer ya gyara tare da faɗin.
“Waya baku kwangilar kashe su?
Sannan akan me zaku kashe su?”.
Ɗayan da yafi galabaitane ya ɗago fuskarsa da duk halittarsa ta canza saboda azabebben bugu da ya sha yace.
“Mu mutanen garin dake gefen Jauro Yaya ne, kuma manyanmu ne suka bamu kwangilar karshe su".
Akai Khausar ta ɗaura hannu tare da faɗin.
“Ai kune ma na gani a Jauro Yaya ”.
Cikin tsawa Sheikh Jabeer yace.
“Me ya kaiku Jauro Yaya kuma?”.
Na farkon ne ya karɓi zancen da cewa.
“Mu muka kashe Garkuwan Rugar Jauro Yaya Umaru”.
Wani irin raunataccen kuka ne ya kubcewa Khausar yayinda gaba ɗaya jikinta ya ɗauki rawa.
Jalal kuwa a hankali ya gyara riƙon da yayiwa wayarsa saboda video'nda yake yi musu.

Zama Sheikh Jabeer ya gyara tare da ci gaba dayi musu tambayoyi.
Shi kuwa Moddibo gaba ɗaya ilahirin jikinsa rawa yake ji yake duniyar tayi masa ƙunci ji yake tamkar ya fisge bindigar dake hannun Sheikh Jabeer ya kashe su kowama ya huta”.
Amma ya kasa motsa wa saboda Khausar dake rungume dashi ita ta hana shi motsi.
Dayan ne ya karɓi maganar da cewa.
Kamar haka uuna ɗaya daga cikin mutanen dake Maƙoftaka da Rugar Jauro Yaya wanda sun kasance arna ne sannan manyan sune suka bamu umarnin su kashe Garkuwan Rugar Jauro Yaya saboda shine yake shiga cikin Sabgoginmu yana hana mu Kidnapping yanda suke a yankin, dan da in sun sato mutane a nan cikin tsaunukan dake zagaye dasune suke zuwa su ɓoye mutane, sai an biya su kuɗi wanda in za'a samu mutane a wurin kai tsaye cewa za'ayi Fulani wurin ne suke satosu.
saboda haka ne in sunje sunyi kidnapped shi yake hana su sakewa, kuma basu isa su ɗauki dabbobi yanda suke so saboda kasancewar mutum mai sa ido da kuma Jarumta”.
Cikin tafarfasan zuciya Sheikh Jabeer ya dasa masa bindiga akansa kana yace.
“Shi kuma Malam Jameel meya muku?,”.
Cikin haki da fusgar numfashi yace.
“Shima Malam Jameel manyan mune suka bamu kwangilar kashe sa Saboda shine mutum na farko daya buwayi al'ummar mu da wa'azi wanda yake zama sanadin da matasanmu da yawa suke Musulunta shiyasa manyan mu suka bamu umarni shi da Moddibo mu haɗa su mu kashe su shine abinda zai fi mana sauƙi da kwanciyar hankali idan ba haka ba zasu janye mana ra'ayi da tunanin matasan mu”.
Dafe kai Sheikh Jabeer yayi tare da cewa.
“Innalillahi wa'inna alaihi raji'un”.
Cikin tashin hankali Moddibo ya dafe kansa tare da faɗin.
“Hasbunallahu wani'imal wakin".
Sai kuma ya koma ya zauna yana dafe kansa da hannun ɗaya yayinda ɗaya hannun kuma ke tallabe da Khausar cikin kaɗuwa yace.
“Ana zaton wuta amaƙera sai gata a masaƙa ina zaton kashe J akayi tunda aka kamasa na tabbatar cewa magautane acikin kashe sa amma duk atunanina akwai sa hannun ɗaya daga cikin Yadikkonsa ashe babu su Astagfirullah Allah na tuba ka yafe min da zargin da Nai ta yiwa Hajia Turai da Karima Allah na tuba”.
Cike da rauni da tausayinsa Khausar ke zubda hawaye, shi kuwa Modibbo cikin rauni ya cigaba da cewa.
“Manzon Allah (S.A.W)da kansa yace _Azzhana zhambu Walau kana haƙƙun_ sai naje na nemi yafiya da gafarar Hajiya Karima saboda duk tunanina ko ita ko Hajiya Turai akwai sa hannun ɗaya daga cikinsu aɓacewan J ashe suma ba abinda suka sani waɗan nan kafiran maƙiya Allah da Manzonsa suka sa aka kashe min J ɗina”.
Sosai Sheikh Jabeer yasa aka azabtar dasu suka faɗi duk laifinsu daga nan aka tura su waje na daban aka killace su domin jiran yanke musu hukunci.
Jalal kuwa nan take ya tura Modibbo video da yayi musu na cikekken bayanansu da sukayi.

Sheykh Jabeer kuwa da kansa ya tara su Abualeey yayi musu cikekken bayanin, ya ƙara da cewa, sai yazo ɗaurin auren su Dr Jameel shi da kansa zai yiwa Ummi da Abban Jameel dukkan bayani.

Aranan ƙarfe goma dai-dai na safe suka kama hanyar tafiya Membila da rakiyar motoci na musamman.

Ƙarfe huɗu dai dai ya musu acikin garin Gembilan...

By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAKAYYAH Book 3 PAGE 2*

Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*

KAZAURE COLLEGE OF NURSING SCIENCES (KCONS)
Lafiya Uwar jiki, Kuma sai da lafiya ake morar rayuwa. Kazaure College Of Nursing Sciences (KCONS) ta kawo muku ingantaccen tsarin koyar da jinya da unguwar zoma, mun himmatu wajen samar da kwararrun ma'aikatan jinya da unguwar zoma a fadin Nigeria da ma matakin duniya baki daya, a KCONS mun tanadar muku kwararrun malamai, ingantaccen yanayi da tsarin koyo da koyarwa kai harma da tsarin e-learning, ka zalika akwai tabbataccen tsaro a dakunan kwanan dalibai maza da mata, bugu da kari kudin makaranta dai-dai aljuhu ne, KCONS munanan a lamba 5 layin fadar sarki dake kan hanyar kano zuwa daura a Kazaure jahar Jigawa, za'a iya samummu a shafikanmu na facebook da instagram @KCONsciences domin bayani, za'a iya tuntubanrmu a wadannan lambobin, 07066542055, 08035298851, ko shafin mu na yanan gizo @ http://kcons.edu.ng/admission KCON sciences kan turbar aiki da kwarewa muka shahara.

https://chat.whatsapp.com/HCji7xLpR1VEJGYcZJMP6k

Ajere-Ajere motocinsu suka fara shiga harabar gidan Innayi. Moddibo kuwa sassayan numfashi ya fesar a hankali ransa cike da mamakin, shin meyesa Abban Jameel yace su sauƙa anan duk da yasan cewa ba wasu wadatattun ɗakuna bane a gidan, kasancewar daga ɗakin Innayi sai Side ɗin sa dake da 2 bedroom sai single room a bakin ƙofar falon, yace wa Abba su sauƙa a hotel daya musu booking Amma yace a'a yaƙi masa musu ne, saboda bai san mai ya shirya ba duk da yafi tunanin Abba yace hakane ko sai sunci abinci kafin su tafi Masauƙinsu.

Akuma dai-dai lokacin motocinsu sukayi Parking a farfajiyar gidan.
Daga can waje kuma cikin sassarfa Haiydar da Bashir suka nufo gidan wanda har sun dauki hanyar komawa gida kasancewar sun jira su basu zoba sai kuma suka hango motocin su.

Acan harabar cikin gida kuwa cike da matsanancin mamaki da al'ajabi Moddibo ke bin baki ɗaya ilahirin gidan da kallo wanda aka tsara shi yayi masifar kyau wasu dan ƙara dan ƙaran Side ne akayi su guda biyu wa ɗan da kusan komai nasu irin nasa ne sai dai basu da wadatan flowers kamar nashi cikin fesar da numfashi da mamakin dake kwance saman fuskarsa ya ziro ƙafarsa na dama kafin ahankali ya gama fito da gangar jikinsa daga motar, hannunsa na riƙe cikin na Khausar still Idanunsa na bin harabar gidan da kallo.
Akuma dai-dai lokacin Idanunsa suka sauƙa kan Abban Jameel, Lamiɗo da Malam Ahmad suna sauƙa daga kan barandar ɗaya daga cikin Sabon Side biyu da aka gina still da mamaki ya maida kallonsa kan Innayi data fito daga Motar da suke.
Murmushi Innayi tayi ganin kallon mamakin da yake bin gidan dashi kana tace.
“Bismillah ku shiga side ɗinka”.
Kallon yaushe akayi wannan ginin yayi mata, fahimtar kallon da yake mata yasa ta jinjina masa kai tare da cewa.
“Tun kwanaki ai aka fara ginin saboda sanin cewa zamu zo Auren su Jameel, kana lokaci zuwa lokaci zamu buƙaci zuwa nan tunda ni da kai dai ba zamu manta garin Membila ba”.
Sanyayyar ajiyar zuciya ya sauƙe kana yayi murmushin gefen baki sosai yaji daɗin hakan saboda bawai ya tsani garin Membila bane saboda ya samu nasa garin, kawai dai Membila ta fita a ransa ne saboda rasa amininsa, Amman duk da haka yasan gari Membila garine wanda yake da tarihi arayuwarsa yana jin Membila na cikin garin da yake tamkar tsagin jikinsa, ya sani bazai manta garin arayuwarsa ba, ko ina yaje a duniya watara zata faɗo masa arai kuma dole zai buƙaci jin yana son zuwa cikin garin.

Anutse Didi ta fito kana Lalla Khadijah, Lalla Hafsat, Sai Rahama tana fita ta nufi gefen Khausar fuskarta ɗauke da murmushi tace.
“Woww Lalla Khausar haka garinku yake daɗi?,Masha Allah kina jin weather Mai daɗi haka Masha Allah i like it”.
Murmushi Khausar tayi kana ta gyaɗa mata kai da faɗin.
“Aikuwa zaki sha sanyi”.
Idanu Rahama ta lumshe sai kuma ta buɗe tace.
“Aikam akwai sanyi kam, duk da muma A Morocco ana mana sanyi but time to time ne amma bai kai wannan ba sanyin nan daban ne”.
Ta ƙarashe maganar tana ƙanƙame jikinta waje ɗaya jin yanda sanyi ke ratsata.
Chapter 5 · 0% Book details