← Book details Sakayyah Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 38

Sashe 12

Sakayyah Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Lamiɗo kuwa kullum binshi nake yakai su asibiti yaƙi ance kuma ya ɗaga Auren Asiya tun da ga jikin Mahaifiyarta da ƴar uwarta ba lafiya yace babu wanda ya isa ya hana suje can su ƙarata da zunubin su”.
Cikin jimami Khausar ta tallafe kuncinta tare da cewa.
“Kai Rayuwar Nan Allah dai yasa mu cika da imani” .
Cikin sanyi jiki Momy tace.
“Amin ya Allah, haka rayuwa take dan kayi abu a ɓoye Allah na ganin ka gashi yau yaya da kanta ta fito take ta faɗamin abubuwan da tayi ta min da bakinta, wai harda cewa ita ta kashe min Ramadan nace a'a ni karya ɓatamin gawar ɗa, dan dama tunda yayiwa wannan haɗarin garin gwaje-gwajen aga kanshi bai buga aka gane cewa yana da cutar brean Cancer.
A lokacin ma sunce ya cinye kaso biyu cikin uku kanshi shiyasa ko mgnin basu bashi ba.
Ni nasan kuma Abbanku ma ya sani kune dai bamu faɗawaba.”
Cikin zubda wa Khausar tace.
“Allah Sarki Ramadan Allah ya jiƙanshi”.
Cikin sanyi Momy tace.
“Amin ya Allah kinga
ni dai na yafe mata kema ki yafe mata”.
Tana shafa cikinta tace.
“Na yafe mata Mommy, kuma in sha Allah duk randa na haifi mai kama da Ramadan tun asibiti zan bakishi ya meye Miki madadin Ramadan ɗinmu ki raineshi”.
Murmushin jin daɗin Momy tayi tare da cewa.
“Allah ya sauƙeƙi lfy Khausar am ki raini abinki da kanki Mamana”.
Cikin kunya ta ce
“Amin ya Allah”.
Sai kuma ta kalli Momy jin tana cewa.
“Wata nawa ne yanzu”.
Kai ta ɗan sunkuyar tare da cewa.
“Wata uku ne ya shiga na huɗu”.
Kai Momy ta jinjina.
A wannan ranan haka Momy da Khausar suka yi yammacin suna hira.

Da daddare bayan an idar da Sallar Isha'i Moddibo yazo ɗaukarta.

Bayan Moddibo yazo suna hira Momy ta kalli Khausar tare da cewa.
“Khausar kawo masa abinci”.
Kai Khausar ta gyaɗa kana ta miƙe ta shiga kitchen ta kawo masa.
Gabanshi ta zauna tare da matso da warmars ɗin.
Tuƙeƙƙen tuwon shinkafa da miyar kase wanda yaji man shanu, da kifi haɗi da nama.
A plate ta zuba masa mai ɗan yawa kana ta ajiye masa agabansa tare da sa kishi sassayan kunun ayan da Momy tayiwa su Didi cika cup ɗin tayi kana ta koma bisa kujerar.
Gyara zamansa tare da cewa.
“Toh saƙƙo muci”.
Kai ta girgiza tare da shafa cikinta tace.
“Um-um ai na ƙoshi”.
Ɗan ware idanunsa yayi tare da faɗin.
“Kin tabbatar?”.
Cikin gaskiya da gaskiya tace.
“Wallahi naci Yah Mu'allim”.
Kai ya girgiza yana mai tsirawa cikinta idanu yace.
“Ban yarda ba”.
Raudat dake shigowa ta kallesa tare da cewa.
“Wallahi taci da yawa Yah Moddibo Addah Khausy yau tunda tazo sai tuwo take ta ci”.
Cikin mamaki ya kalleta tare da faɗin.
“Da gaske?”.
Daidai lokacin kuma Momy ta fito daga bedroom ɗin ta cikin shiri wanda da alamu Side ɗin Lamiɗo zata tafi, cikin yin ƙasa da Moddibo ya kalleta kana yace.
“Momy wai dagaske taci abinci?”.
Murmushi Momy tayi tare da gyaɗa masa kai tace.
“Wuuuu ai Khausar yau ko Gara nan ya barta acin abinci ai daga safe zuwa yanzu taci abinci ya kai sau bakwai”.
Cikin mamaki yace.
“Ikon Allah Momy bata cin abinci a gida fa”.
Momy na ƙoƙarin fita tace.
“Aikam haka su Didi suka faɗa amma nan kam tana ciki inaga duk yunwar data tara take sauƙewa”.
Cikin farin cikin daya kasa ɓoyewa yace.
“Alhamdulillahi”.
Bayan fitan Momy yafara cin abinci suna ɗan taɓa hira.
Suna cikin hirar Momy ta dawowa zuwa wannan lokacin already Moddibo ya gana cin abincin har Khausar ta kwashe kayan kallon Khausar yayi tare da cewa.
“Toh mu tafi dare yana yi momy zamu tafi dare yayi”.
Ya ƙare maganar yana kallon Momy.
Ɗan murmushi Momy tayi tare da faɗin.
“Toh Allah ya bamu Alkhairi”.
Kallon Khausar dake zaune yayi kana yace.
“Minha mu tafi ko?”.
Kallonsa tayi tare da faɗin.
“Ba anan zan kwana ba?”.
Yi yayi kamar bai jita ba sake langwaɓar da murya tayi cike da shagwaɓa tace.
“Ayyah ka barni in kwana mana”.
Still yi yayi kamar bai jita ba ya ma Mai da kallonsa kan Momy yace.
“Momy zamu tafi dare yayi”.
Kai Momy ta gyada tare da faɗin.
“Allaj ya bamu Alkhairi ku gaida su Didi”.
Cikin sauri da lumshe ido Khausar tace.
“Dan Allah kabarni in kwana mana”.
Juyawa yayi ya kalleta kana ya kalli Momy da tayi shiru alamar tana son ƴartata ta kwana.
Har ga Allah baison barinta ta kwana amma ganin yanda Momy tayi shiru tana Murmushi yasa shi kallon Khausar data langwaɓar da kai da kuma yanda akace tana cin abinci yasa shi fesar da numfashi tare da faɗin.
“Shikenan zo muje ki rakani”.
Da sauri ta ɗan ware idanunta tace.
“Kenan ka barni in kwana?”.
Kai ta gyaɗa tare da faɗin.
“Eh ba damuwa amma muje in Baki saƙo amota”.
Cike da farin ciki tace.
“toh”.
Kana ta miƙe tabi bayansa.
Cikin tsananin jin daɗi momy ta rakasu da ido domin ta samu cikekkiyar gamsuwa akan mutumunci da kulawar Modibbo da iyayensa akan ɗiyar tata.

Mazaunin Driver ya zauna yayin da ta zauna gefen mai zaman banza janyota jikinsa yayi kana ya ɗaura hannunsa akan cikinta tare da faɗin.
“Minha bana son barinki ki kwana awani waje batare dani ba amma yanda kika nuna agaban Momy ba yanda zanyi”.
Cikin sanyi tace
“Kayi haƙuri Yah Mu'allim nayi kewar Momyne”.
Cikin lumshe idanu yace.
“Shikenan ba komai”.
Ya ƙarashe maganar yana ɗaura hannunsa akan cikinta ahankali tace.
“Kayi haƙuri ”.
Kai ya girgiza tare da cewa.
“Bakomai”.
Cikinta yake shafawa kafin ya buɗe tafin hannunsa ya karanta _Ƙulhuwa³ Falaƙi³ Naasi³ Ayatulkursiyyu¹ Amanarrasulu ¹ Laƙadja'akum¹_ ya shafa mata cikinta tare da faɗin.
“Toh Allah ya kare ki ya kare min Babyna saboda banason Maƙwabtakanki da Hajiya Bunayya tsoronta na keji akan abinda tace ta miki”.
Kai ta girgiza tana sake lafewa jikinsa tace.
“Bakomai in Sha Allahu ba abinda zai samemu tunfa addu'o'inka na tare damu”.
Cikin sanyi yace.
“Dan Allah Minha kada ki kwanta bakiyi alwala ba kuma kiyi addu'a Kinga Bama tare bare inyi miki”.
Cikin shaƙar ƙamshin jikinsa tace.
“In sha Allah zan yi kuma Momy nayi min yadda kake min”.
Cikin jin gamsuwa yace.
“Ayyah Mommy Allah ya bar mana su ”.
Amin. tace tana shafa sajenshi.
Bayan sun sake taɓa hira ya rakata har ƙofan Falon Momy sai da ta shiga kana ta juya ya koma.

Ita kuwa Momy hannun Khausar ta kalla.
Ummmmm tace saboda ganin ba wani saƙo kawai so yake ya kebe da matarsa fahimta haka ya sata mgnar.
“Uhmmm kaddai in shiga haƙƙinshi shi da matarsa”.
Sai kuma ta kalli Khausar dake matsar da Raudat gefe tare da kwantawa kusa da Momy tana cewa.
“Yau dai ke zaki koma gefe ni zan kwanta kusa da Mommy na”.
Murmushi Momy tayi tare da cewa.
“Je kiyi alwala tukun”.
Toh tace kana taje tayi alwala kana tazo ta kwanta nan sukayi ta hira.

Washe gari bayan an idar da Sallar Asbah duk su Abualeey sun koma gida.

Moddibo kuwa karatun ƙur'ani ya fara daga bisani yayi Azkhar.
Takwas dai ya miƙe ya nufi gida.

Har ya nufi bedroom ɗinda sai kuma ya fasa key ɗin motarsq dake kan Dinnin table ta ɗauka, kana ya fito kai tsaye mota ya shiga.

Tare da nufan gidan Momy haka nan yake ji yayi mugun missing ɗin ta ji yake kamar ya ɗauki wasu kwanaki bai ji ɗumin baby nai ba.

Yana Parking motar aharabar gidan ya hango Haiydar da Bashir wanda yanzu ya dawo gidan da kwana saboda baƙin da suka cika gidansu.
Suna ganinsa suka isa wajensa tare da cewa.
“Yah Moddibo Barka da safiya”.
Cikin sakin fuska yace.
“Yawwa Haiydar Barka dai”.
Su Haiydar ne sukayi nasa jagora zuwa Falon Lamiɗo bayan sun gaisa Lamiɗo yace.
“Nima yanzu nake shirin zuwa wajensu Abualeey”.
Anutse Moddibo ya ɗan sunkuyar da kansa ƙasa tare da cewa
“Ayyah ai suna na tare da Abban Jameel ma da Malam Ahmad”.
Kai Lamiɗo ya gyaɗa tare da kallon su Haiydar kana yace.
“Ku isa dashi”.
Kai suka gyaɗa tare da fita kana ya miƙe yabi bayansu.

Dai-dai lokacin kuma Momy na kitchen.
Yayin da Khausar ke kwance kan 3sitter.
Suna isa bakin Falon Haiydar ya kalli Moddibo tare da faɗin.
“Yah Moddibo ka shiga ”.
Kai ya gyaɗa kana yace .
“Ok”.
Sai kuma ya kalli Bashir tare da cewa.
“Ina zakujo”.
Cikin shaƙuwa Bashir yace.
“Adda Asma'u ce ta matsa mana da kira wai muje mu amso mata ɗinkunanta”.
Kai jinjina musu, daga nan ya nufi cikin ɗakin.

Kana suka juya da alamu aikan zasu tafi.

Ahankali Moddibo ya shiga Falon bakinsa ɗauke da sallama.

A hankali ya lumshe idanunsa kana ya buɗesu sabida hango Khausar kwance bisa 3 sitter. Falon shiru ba kowa sai sassayan ƙamshi da sautin TV can ƙasa da ake addu'o'in azkar.

A hankali idanunsa suka suke yawo a kanta tana bacci cikin kwanciyar hankali wanda ga duk kan alamu tana jin dadin bacci..
Sai kuma plate dake gabanta da cup wanda ke da guntun tea a ciki sai plate ɗin dake da alamun indomei ne taci a ciki kafin tayi baccin.
Chapter 12 · 0% Book details