← Book details Sakayyah Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 38

Sashe 32

Sakayyah Part 3 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Asma'u dake cigaba da hotuna da wayar Khausar wayar ya ɗauki suwwa ganin sunan Yah Mu'allim na yawo yasa da sauri ta nufi Khausar dake tsakiyar Didi da Momy suna hoto tayi saurin isa gareta kana ta tsugunna zata miƙa mata wayar kasancewar azaune suke haka yasa ta fito a hoton da yayi masifar kyau.
Asma'u kuwa cikin raɗa takai bakinta kunnenta tace.
“Gashi fa Yah Moddibo yana kiran ki”.
“Mu gani”.
Cewar Khausar tana karɓan wayar tare da kaiwa kunnenta tace.
“Assalamu Alaikum Yah Mu'allim”.
Cikin wani irin yanayin na musamman yace.
“Minha kizo ki sameni aɗakina”.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Toh”.
Sai kuma ta miƙe tare da rungume jaririn kai tsaye ta nufi sashen bakinta ɗauke da sallama ta shiga falon nan ta samu Dr Jameel, Dr Zakariyya, Ibraahim,Yah Ali, da Yah Abba da sauran yan uwansa.
Yah Abba na ganinta yayi Murmushi tare da cewa.
“Mai jego kin sha ƙamashi”.
Murmushi tayi kana tace.
“Ai dai kam”.
Kallonta ta mayar kan Ibraahim tare da cewa.
“Ibraahim Yah Mu'allim fa?”.
Da hannu ya nuna mata bedroom ɗin kana yace.
“Yana ciki”.
Ahankali ta nufi bedroom ɗin kwance ta gansa akan gadon yana ganinta ya saki sanyayyar ajiyar zuciya tare da buɗe mata hannunsa.
Cike da begensa ta zauna kusa dashi miƙewa yayi ya haɗa ta da jaririn ya rungumesu ahankali ya riƙa kissing ɗin goshinta zuwa wuyanta da kuma sassan jikinta baki ta ɗan tura tare da cewa.
“Yah Mu'allim ka matsaneni kuma ɗanka ya matse min wajen Theater na”.
Cikin sauri ya saketa kana ya karɓesa ya kwantar dashi tare da jawota jikinsa ya rungumeta sai kuma ya saki sanyayyar numfashi kana ya ruggumeta tsam cike da kulawa da kuma ganin yanayinsa ta shafo sajensa tare da cewa.
“Yah Mu'allim lafiya meke faruwa?”.
Kanta ya tallofo kana ya kalleta ido cikin ido da mamaki take kallonsa ganin yanda idanunsa suka kaɗa sukayi jawur dasu cike da kulawa tace.
“Yah Mu'allim lafiya?”.
Sunkuyar da kansa ƙasa yayi kana ya ɗago ya kalleta tare da cewa.
“Minha na yiwa Abualeey laifi kuma har yayi fushi dani”.
Cikin sauri ta zare idanunta tare da faɗin.
“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un Yah Mu'allim laifin me kayiwa Abualeey?”.
Araunane yace.
“Minha nayi mishi babban laifi naƙin bin Umarninsa”.
Cikin tsoro da kaɗuwa tace.
“Ya Ilahi Yah Mu'allim akan me baza kabi umarnin Abualeey ba?”.
Langwaɓar da kansa yayi kan wuyansa yace.
“Saboda kece ban bi Umarnin Abualeey ba!”.
Cikin sanyi da rauni tace.
“Ya Ilahi bana son jin wannan maganar sam maganar babu daɗin ji Yah Mu'allim Kabi Umarnin mahaifinka shine abinda ya dace kuma shine *SAKAYYAR* da zamuyi masa”.
Cikin rauni da karyewar zuciya yace.
“Bazan iya ba”.
Cike da mamakin shin wani irin abu ne me nauyi da girma agaresa da yasa har ya yiwa mahaifinsa gardama tace.
“Haba Yah Mu'allim ya za'a yi kace baza kayi abinda mahaifinka keso ba shin wani irin abu ne?”.
Cikin sanyi ya kalleta kana ya lumshe Idanunsa tare da cewa.
“Saboda yau yake so a bani mulkin Masarautar Mouley ahannuna”.
Cikin sauri da jin daɗi kana da Jimamin yanayin da yake ciki tace.
“Toh mene Yah Mu'allim mulkin ne baka son rikewa ko me meyesa zaka yi mishi gardama?Kuma ai nikam ma ina son mulkin nan meyesa baza ka karɓi Sarautar ba? Kawai ka karɓi mulkin shine abinda ya dace”.
Kai ya jujjuya tare da juya ƙwayar idanunsa acikin nata kana ya riƙo hannunta acikin nasa tare da cewa.
“Ba karɓan mulkin bane matsala Minha”.
Cikin rashin fahimtar abinda ke damunsa tace.
“Toh ka karɓi mulkin mana kayi mishi biyayya akai”.
Hannunta ya damƙe kana yace.
“Ki bari kiji ko menene”.
Fuska ta tsuke tare da cewa.
“Nikam babu abinda zanji Yah Mu'allim kawai kayi mishi biyayya akan abinda yake so ka karɓi mulki Allah ya tayaka riƙo ya baka ikon Adalci kai masa biyayya ka samu lada”.
Cikin sanyi da rauni yace.
“Cewa yayi an bani mulki bisa sharaɗin za'a bani Auren wata mata ya zama ina da mata biyu!”.
Da wani irin sauri ta dafe ƙahon zuciyarta da yayi wani irin harbawa cikin rauni da fusgar magana tace.
“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”.
Atake jikinta ya fara rawa kar-kar-kar tamkar wacce aka watsawa ruwa ƙanƙara atsakiyar hunturun sanyi kana idanunta suka kaɗa sukayi jawur tamkar garwashin wuta lokaci ɗaya taji numfashinta na Up and down alamar yana shirin barin gangar jikinta jawota yayi ya riƙe ta da damuwa atare dashi yace.
“Kee ki tsaya mana ki nutsu me haka!?”.
Gaba ɗaya ta rikice numfashinta sai fusga yake alamun tana gab da suma saboda tsabar masifar kishi, cikin fusgar numfashi da ficewar hayyaci ta dafe ƙahon zuciyarta tare da cewa.
“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un Yah Mu'allim Aure kuma?,Wata matar za'a Aura maka?,ita?”.
Sai kuma ta tsaya da Maganar jin numfashinta na shirin barin gangar jikinta alamar zata iya rasa numfashinta.
Moddibo kuwa cikin matsanancin mamaki tsoro gami da ruɗu yake kallonta tabbas yasan tana da kishi amma bai taɓa tunanin kishinta yakai wannan matsayin ba.
Cikin sauri ya rungumeta tare da riƙo hannayenta kana yana jijjiga fuskarta yace.
“Khausar Khausar ki nutsu mana ki buɗe idanun ki dan Allah ki tsaya ki fahimci abinda zan faɗa miki”.
Da ƙyar ta iya buɗe idanunta.
Cikin sauri da tsoro ya sake tallafe Fuskarta ganin yanda ta zazzaro idanunta sukayi wani irin ja.
Ahankali ya fara bubbuga kumatunta tare da cewa.
“Dan Allah Minha ki nutsu kiji abinda zan faɗa Miki”.
Cikin rauni murya da bugawar zuciya tace.
“Yah Mu'allim yanzu mata zasu ƙara maka innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”.
Sai kuma ta kife kanta akirjinsa ta saki marayan kuka mai masifan cin rai da zafi kukan data sakene ya temaka wajen daidaiton numfashinta ya tsaya.
Chapter 32 · 0% Book details