Sashe 9
Sakacin Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Ummati ke da kawar ki Siyama hira ake haka? To ga
meat balls
kuna yi kuna taunawa, hira zata fi armashi
. Ta ajiye kyakkyawar roba a rufe a gaban Ummati, na faki idon ta na jefa mata harara, Ummati ta janyo akushin gaban ta ta bude ta dauki kosan naman kaza guda ta luntsuma a baki, dadin sa ya ratsa har kwanyar ta, bata san lokacin da ta ce.
Ai wato zaman nan da kika ga ta yi kamar Rakuma a gabana, ba abinda ta ke yi sai kwashe miki albarka!
Na zaro ido na ce
Ummati ki ji tsoron Allah ce miki fa kawai na yi na yi mata girki
. Sai kuka irin na borin kunya. Kunyar duniya ta lullube ni. Shiyasa na nannade ta da kuka. Ba abinda ya fi a kama ka kana gulma kiri-kiri, gulmar ma ta wanda ya kama ka red-handed.
Anti Wasila tayi wani lallausar murmushi ta ce
ai kafa ta kafar ta zuwa Abuja Ummati, kawancen namu nida ita yanzu ya fara
. Ban san lokacin da na saka kukan da karfi ba ba ina fadin
idan wasa kike yi ki bari, in kin ga na bar Mambila to gidan bakinhadaddenmijin mafarki na zani a wani garin daban, amma ba zani gidan ki ba. Ba wanda zai raba ni da Ummati ita bata takura mun
. Anti ta wani dube ni shekeke! Tace
da wannan annakiyar kazantar taki da gashi fal hammata hadadden mijin zai zo? Lallai fa hadadden miji a mafarki! Ai sai a mafarkin kam! Allah tsinewa uwar mai karya, hatta Umar aka bashi ke a haka an takaice shi, kuma sai na gaya masa ya sayi shavingcream ya ajiye duk sati ya saka ki a toilet ya sullube ki da kan sa
Tashi na yi ina kumburi kamar kububuwa na bar mata dakin don na tsani Anty Wasila yanzu.
Ummati na jin mu banda aika lomar
meat ball
ba abinda take yi, na gama lura Anti ta gama saye Ummati da nau
in kayan dadin ta kala-kala kullum da abin dadin da zata sauya mata na makulashe ashe dama don ta raba mu ne don yanzu haka Ummati ta fi jin maganar Anti a kan tawa.
Da daddare bayan sun gama cin abinci ita da Abba ta kwashe komai ta dawo ta same shi cikin kissa irin tata sai ta ce .
Baban Siyama amma dai da Siyama zamu koma Abuja ko? Tunda Umar ma komawa zai yi gara suna tare yadda suka taso nima kuma in ke jin motsin mutum a kusa da ni don wallahi bani da ra
ayin
yan aiki
Abba kamar Anti ta shiga ran sa ta sosa masa inda ke masa kaikayi don ya gama yanke shawarar kai ni makaranta mai kyau don kamar bana koyon komai a makarantar mu ta nan Mambila, cikakken sentence wannan na turanci bazan iya hada maka daidai ba, kawai yana shayin rigimar Ummati ne.
Anty bata fito fili ta gaya masa dalilin ta na son tafiya da ni ba amma shima Abba ya san wasu, musamman rashin kwaba ta da Ummati bata son yi, sannan Umar yana yawan kokan ta masa abubuwa da yawa da suke damun sa akan irin goyon Kaka da Ummati take min.
Sai Abba ya ce
I thought as much. Amma Ummati bazata yarda ba
Anti ta ce
ka bar komai a hannu na, I assure you zata yarda idan ni nayi mata magana.
Tsakanina da Allah da kuma kaunar da nake maka Dr. nake son gyara rayuwar Siyama, hakika tana bukatar mentoring na uwa a wannan stage din na puberty da take ciki, ka saka a ranka tamkar Siyama na hannun mahaifiyar ta mai rasuwa a zaman da zamu yi tare ni da ita. Allah ya jikan ta da gafara
Abba bai san sanda ya bude ma Wasila hannu ba ta yi azamar shigewa ciki ya rungume ta yana shi mata albarka.
*****
Watakila dai matar nan har tsayuwar dare ta yi wa Ummati ta mallake ta!
. Haka na gayawa Ya Omar cikin kuka da ya tabbatar min Ummati ta amince gobe da Anti Wasila ta cika wata guda a Mambila zamu wuce Abuja tare bakidayan mu har da Abba da ita Antin. A kofar gida na dawo daga islamiyya ya tare ni yake gaya min wai maza in je in hada kaya na da sassafe zamu kama hanyar Abuja.
Da kuka na wiwii na shiga gida domin kuwa a karo na biyu Ya Omar ya sake gwabje min baki wai na raina Anti Wasila da nace ta yi tsayuwar dare ta mallake Ummati.
Kan Ummati na fada da kuka na
Ummati da gaske kin yarda a tafi da ni a raba mu? Ummati nice fa Azumin ki, Boodon ki, Asshenki, Siyamar ki
. Ummati tayi azamar ture ni daga kan kafafun ta tace