← Book details Sakacin Waye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 28

Sashe 10

Sakacin Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Allah yasa Sabira ce ba Siyama ba. In kin zauna wace tsiyar kike taimaka min da shi? Banda ki nade kafa a gado ki ci ki tashi hatta kwanon da kika ci abinci sai ni zan dauke miki, idan kuwa kashi kikayi sai dai in kora miki, hayya ratata Allah ya raka taki gona, Wasilar ce abin tausayi ba ke ba, sabida yadda zaki je ki maida mata daki matattarar kazantar ki. Faruqu kawai zan yi kewa
Gefe na koma na saka kai cikin cinyoyi na na soma gunza kuka, na ki hada kayan na ki yin komai, maganganun Ummati sun bakanta min ba dan kadan ba, sai ga Antin ta yi sallama tana tambayar Ummati wai na kammala hada kayana? Abba ya na jera su a trunk din mota ne tun yanzu da daddare, don da assubah zamu kama hanya sabida sai mun kwana a hanya.
Ummati ta ce
gata nan sai kuka take wai bazata bi ku ba
Anti ta karaso inda nake ta tsugunna cikin lallashi tana cewa
Oh ni Wasila bakin jinin nawa har ya kai haka gun Siyama?! To ki sha kurumin ki duk hutu da kaina zan kawo ki Mambila ki yi hutun ki tare da Ummati
Na dago idanuna jajir, jagab dasu da hawaye na dube ta
kada ki kara tube min zani, babu kyau wani ya ga tsiraicin wani, in kin ce in yi ko menene zan yi, sannan don Allah kada ki kara saka ni girki
Anti tace
kece kika yi gardama in da kin yi salin alin ba zan yi miki da kai na ba, girki kuwa sunnar kowacce mace ne
. Na yi sharbe na ce
ai ba dole bane, tunda ni din bana so, kuma kada ki kai ni makaranta, bana so bana son karatu wallahi
Anti ta yi dan jim! Kafin ta ce
ban yi wannan alkawarin ba, sabida ba ni ke iko da ke ba, alkawarin da zan yi shine ko iya sakandire kika yi zan roki Abba ya kyale ki ba lallai sai kin je jami
a ba, sai ku yi auren ku da Omar ki yi ta sullubowa Ummati kyawawan tattaba kunne
Ummati mikewa tsaye ta yi don lallashin da Anti Wasila ke ta faman yimin ya fara bata haushi tace
da ke da mijin naki da tattaba kunnen naki da Antin naki duk ku tattara ku bar min daki kafin in miki tabon sallama da Mambila a kan farar fatar ki, ki koma birnin da dabbare-dabbare, kin san dai ban taba gwada kai hannu na jikin ki ba kada kisa mu yi sallama da shi yau (duka)
Anti tace
yi hakuri Ummati, kukan sallama take miki, bari in hada mata kayan da kaina
Anti ta shiga dakina tana hada min kaya amma ko nisa bata yi ba da ta ci karo da wanduna masu busashshen menses a jiki ta watsar ta fito tsigar jikin ta na tashi, tana ce da Ummati.
A tattara kayan Siyama duka a wanke a bada sadaqa Ummati
to me zata saka in kuka tafi?
Ummati ta tambaya cikin mamaki, sai Anti tace
babu matsala zan diddinka mata wasu
Shi kam Ya Omar sosai yake murnar komawar sa Abuja sabida jami
a da zai fara a can, nikadai nake bacin rai na da fama da kuncin zuciya. Da asubah muna idar da sallah muka kama hanyar barin Gembu, Gembun Mambila, Gembun da ta tattara duk wani dabdalar kuruciya ta. Zuwa birnin da ya bude sabon shafi na rayuwa a gareni, wanda mafarki na na shekara da shekaru ne yayi min sanadin sa.
Da gaske Aunty Wasila has become my lifestyle influencer
. ta yi nasarar mai da ni MUTUM!
Na farko ta raba ni da rayuwa mara ma
ana dana ke yi a baya. Amma da na san actualizing mafarkin dana ke faman yi shi ke jira na a birnin da ko kusa ban yarda na bi Wasila ba, gara na dauwama a dakin Ummati na, cikin kwarkwata da amosani da kirci, doyi da hamami na da gashin hammata ta. Hausawa suka ce wai zama lafiya ya fi zama dan sarki ta kowanne fanni.
Abu daya nake tunani akan hanyar mu ta zuwa Abuja yake nutsar da bacin raina na rabo ni da Mambila da Wasila ta yi; watakila in hadu da shi
Watakila silar haduwar mu kenan da mijin mafarki na, tunda na tabbata ba a Mambila yake ba, da a can yake, da tuni na ganshi a tsayin shekarun dana dauka ina mafarkin sa.
Bai yi kama da Mambilawa ba ya fi kama da 'Black-Nigerians', don haka kila kaddara ta da shi ita ke sarrafa kanta a kaina. Na kuma tabbata kaddarar ce har ila yau ta sa Wasila fizgoni daga mahaifa ta zuwa birnin gamayyar
yan Najeriya. Domin na yi amanna da cewa Allah na nufin wani babban al
amari a tsakani na da shi wanda ba
a mafarki zai kare ba.
Wanda kuma ban san farkon sa ban san karshen sa ba. Addu
a ta guda daya bazat
a taba canzawa a kan sa ba ta Allah ya bayyana min shi. Ya hada fuskokin mu ko da sau daya ne in gan shi a zahiri don cire kishirwar ganin sa da ke addabar idanu na dare da rana, in gaya masa tsahon shekarun dana dauka ina mafarkin sa
da mafarkin zamowar sa miji a gare ni. In kuma gaya masa cewa ba zan iya rayuwa ba tare da shi ba.
Hakika an halicci zuciyata sarqafe da tasa ta yadda na ke da assurance na cewa zukatan mu are undoubtedly connected, an yi min jarrabawa mai girma a kan sa tun kan in gan shi, tun kan in san shi, tun kan in mallaki hankalin kai na.
******
Chapter 10 · 0% Book details