← Book details Sakacin Waye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 28

Sashe 4

Sakacin Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yi hakuri ka karbi kyakkyawar kyautar
yar da Allah yayi maka ka ji!
Ya mace ce ba namiji ba. Idan ka yi mata kyakkyawan raino watarana zata ji kan ka kamar mahaifiyar ta
Haka Abba ya karbe ni cikin yanayi na dimauta da yankewar buri gabadaya ya fito waje neman Ummati, can ya gano ta inda ya bar ta tana tahiyar sallame sallahr walha a inda ya bar ta tun safe kenan tana rokawa Ashe sauki a cikin tahiyar ta, ya karasa gabanta ya ajiye mata jaririyar a saman cinyar ta sannan ya koma gefe ya saka kai cikin kafafuwan sa ya saka kuka.
Kukan da tun kafin ta san dalilin sa Ummati ta tabbatar itama Asshe maraya ta bar mata, marayun sun zame mata biyu, Ya ilahi, sai ta sallame sallahr ta ce masa
ka ce Innalillahiwa
innailaihiraji
oun Muhammadu, shine kawai abinda zaka yi Allah ya yi farin ciki da kai a wannan yanayin. Ka kuma karbi
yar ka ka yi mata huduba da sunan mahaifiyar ta.
Ka yi fatan Allah ya baku tsahon rai ku ku raine su, ka je ka daukota mu tafi ka wanketa da hannun ka ka yi mata suttura ka kai ta makwancin ta da kan ka shine babbar soyayyar ka gare ta a yanzu, ka cigaba da nema mata aljannah
aga Jalingo kai tsaye suka yi shatar mota zuwa Manbila aka yi wa mahaifiyata sutturah. Mutuwar Inna Asshe ta fi taba Ya Omar fiye da kowa a gidan don shi bai san cewa ba ita ta haife shi bama.
Omar bai san maraicin uwa ba sai da Inna Asshe ta rasu, kulawar mu ta koma hannun Ummati, duk da Ummati bata raga mana komai ba na kulawa da tarbiyyah amma Kakar mu ce kuma tsohuwa ce. Kulawar Kaka daban kulawar uwa-mahaifiya daban, idan ka hada duka biyun zaka fi kowa morewa, uwa ta kwabe ka har da bulala Kaka ta lallashe ka da tuwo da koko, tunda dai Kaka da sangarta jika aka san shi.
Mafari kenan da raino na ya koma hannun Ummati, muka shaku wata irin shakuwa da Kakata Ummatin Mambila, kakkarfar dattijiya, doguwa fara mai kyawun surah wadda bata daukar kowanne irin wargi ko raini a kan jikokin ta, zaka yi mata komai ka kwana lafiya amma kada ka taba Aisha da Omar. Da ganin Ummati zaka san an zuba zamani kuma an zuba kyau an juya miji a lokacin kurucciya.
Abu na farko da ya assasa shaquwar mu zuwa shakuwar da ta zarta ainahin wacce ke a tsakanin Kaka da jika ta zama ta mahaifiya da tilon
yar ta, ya sanya kuma ta dora min soyayyar duniya shine kasancewar ita bata taba haihuwar diya mace ba, na biyu ita ta shayar da ni daga madarar shanun ta, kuma na ci sunan mahaifiyata wadda tayi mata biyayya sosai.
Baba Gidado yayi aure da jimawa da Jaru, matar wani marigayin abokin sa, bayan tsayin lokacin da ya dauka babu aure, don ya tabbata ba zai sake samun mace tamkar (Ummu-Faruqu) ba kamar yadda ya ke kiran Hassu har gobe, amma ko kadan baya jin dadin ta, haka dai ake zaman da dadi ba dadi.
Ya riga ya saba da matar sa Hassu mai addini, mai hakuri da kuma godiya da duk abinda ya kawo mata, mai yakanah, wadda ko kara ya ajiye ya ce kada ta tsallaka bazata tsallaka ba, wadda in ya ce farin yadin nan baki ne zata ce da shi
bakikkirin kuwa
, amma Jaru? Akasin Hassu ce a komai.
Ya yarda hakika Allah ba ya barin wani, don wani ya ji dadi. Da bai dauke masa Hassu ya hada shi da Jaru ba, da bai raba Mamman da Aishatu ba sabida wadannan matan guda biyu tamakar Hurul
eenin duniya suke ga mazajen da Allah ya baiwa su;
Ga kyau ga kuma kyan hali. Ga addini da nasaba mai tsafta. A hakan dai suke zaune shi da Jaru; yau fari gobe tsumma, sabida ya yi alkawarin ba zai taba sakin mace a rayuwar sa ba, sai dai ta bizne shi ko ya bizne ta.
Babbar damuwar sa da Jaru shine ta ki jinin Omar Faruq, ba dama ya zo sassan su goye da ni zata kora mu da tsawa da bulala, daga sanda ta fahimci Omar dan sa ne na cikin sa ba na kanin sa ba tsanar da ta ke ma Omar ta karu, sabida kanin nasa (wanda ta fahimci a Jos yake zaune zuwa yake yi ya koma), kullum ya zo tsarabar sa ta Omar-Faruq ce baya ko ta kan tashi
yar da ya haifa a cikin sa sai Omar, Omar dai Omar dai ko
ina ka shiga sunan sa ne a bakin jama
ar gidan alamar ya gama mamaye zukatan su.
Ita kuma Jaru sai wata jarabta ta same ta; nan duniya babu namjin da yake burge ta irin Mamman sabida gayun sa, bokon sa da tsaftar sa, ya fita daban da mutanen garin Mambila domin a lokacin yana aikin koyarwa a jami
ar Jos matsayin Lecturer, a lokaci guda kuma yana hada digirin sa na ukku a can jami
ar Jos din.
Lokaci - lokaci ya ke zuwa Gembu kuma in ya zo din baya jimawa bai fi yayi sati ko kwana uku ba ya koma, kasancewar dukkansu a gidan gadon su suke zaune har zuwa lokacin illa kowa da sassan sa, sassan Ummati da jikokin ta daban wanda yake daga can karshen gidan, nasu ita da Gidado daban a tsakiya sai na Mamman din a farkon shiga gidan wanda kullum yake a rufe sai idan ya zo garin Omar yake budewa ya share masa ya shigar da kayan sa.
A babban zauren gidan kuma dakin Baffan mu Adamu ne wanda a wannan shekarar Abba (Mamman) sunan da na mayar masa kenan tunda na soma baki, shi kuma Baffa Gidado in ce masa Malam, Abba ya samar ma Baffa Adamu tagomashin tallafin karatu daga (federal scholarship board) zuwa kasar Algers inda zai yi karatun degree akan Diplomasiyya.
A wancan lokacin su Abban mu sune manyan
yan bokon da kasar Najeriya yankin arewa maso gabas ke ji da su da kuma alfahari da su, yana daga cikin pioneers (sahun farko) na malaman tsangayar tsimi da tanadi ko kuwa tattalin arzikin kasa (department of economics) lokacin da aka fara darasin a jami
ar Jos, suna da damarmaki masu yawa a kan scholarships, ya baiwa samarin Mambila da dama tallafin karatu da scholarship zuwa Algers kasancewar a zamanin ba duka ne suka yarda suka karbi ilmin bokon ba a sanda ya kutso Taraba ya isko Manbila sai daidaiku irin su Abba, don haka su suka fi kowa cin gajiyar shi a zamanin da ake ciki yanzu sanda kai ya fara wayewa samarin Mambila na ta rububin shiga karatun.
A kan Mamman Jaru ta raina Gidado take kuma ganin ta yi rashin dace da auren sa, da ta san da kanin da bazata auri wan ba, har fata take ya mutu don ta samu damar auren kanin sa. Ita kam dama ba
yar asalin Mambila bane bakin haure ne daga yankin kasar Kamaru, tsautsayi ya kai shi ga auren ta kasancewar tsohon mijin ta mai rasuwa Malam Jibo aminin sa ne kuma bata taba haihuwa ba, a tunanin sa rashin haihuwa da bata samu ba da Jibo, tsahon shekaru goma sha biyar da suka yi tare da shi zai sanya ta so tilon dan sa Faruku, ta taya Ummati kula da su shi da kanwar sa.
Ba da jimawa ba ya fahimci ba wanda ta tsana a duniya irin Omar din. Abinda ke ran ta a kan kanin sa Mamman ne bai taba sani ba kuma tunanin sa bai taba bashi ba. To ta ina ma zai taba tunanin matar sa kanin sa take so?
Har zuwa wannan lokacin da ya amsa sunan Dr. na ilmi, Mamman Gembu, bai yarda yayi aure ba, fada da nasiha da tsoratarwa babu irin wanda Ummati bata yi masa ba amma ya ki. A karshe Jaru ta ga babu mafita gareta ta samun damar auren Mamman in har Gidado na raye, sai ta soma tunanin hanyar da zata bi ta kawar da Gidado.
Duk abinda ta yi tunanin yi, sai ta ga cewa za
a iya gane ta, a karshe ta nemi guba mai tsinka hanji ta saka mishi a cikin fura. Ta zauna jiran dawowar sa.
Tun tana gadin dawowar sa, ta saka furar da abincin a gaba tana ta kiyasin gobe I yanzu tana cikin Takaba, wata uku masu zuwa sai ta maye gurbin wan da kanin, ko da tsiya ko da arziki (ko da ta asiri ne), tana nan zaune tana wannan saka da warwarar har wani mugun kashi ya zo ya matse ta.
Da fari ta yi kokarin danne shi musamman da yake lokacin dawowar Gidado ya yi amma bayan gidan nan ya ki yarda da hakan, neman fitowa kawai yake yi ko ta halin kaka. Sai ta ga cewa zata iya zuwa tayi kashin ta dawo ba tare da ya dawo ba ko wani ya shigo.
Ta ajiye masa a inda ta saba ajiye abincin sa ta koma sashen ta ta shiga bayan gida kenan Gidado ya shigo tare da wani saurayi.
A nan falon sa suka zauna suna hira ya dauki furar ya baiwa bakon yana fadin.
Chapter 4 · 0% Book details