← Book details Sakacin Waye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 28

Sashe 14

Sakacin Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

shin Abba da gaske kake wai? Ni fa duk maganar auren Ya Omar da kake yi min tun ina karama na dauka wasa kake yi. Abba ba zan iya auren Yayan da na tashi a hannun sa kamar shi ya haife ni ba. Wallahi Abba ba zan iya ba (because i respect him). Kayi hakuri don Allah Abba inada wanda nake so tun ban san so ba!
Daga Abba har Anti Wasila, zaro ido suka yi cikin kidima suna kallo na, Abba harda waiwayawa yana addu
ar Allah ya sa Omar baya falon, yayi ajiyar zuciya da ya tabbatar Omar bai ji ni ba. A wannan karon Abba ya nuna ni da dan yatsa idanun sa sun kada sun yi jajir ya ce.

Boddo kike ko Azumi ko Siyama ki kiyaye ni, mugun kiyayewa, wallahi bani da kyau, a fuska ne na ke da kyau, ban taba nuna miki other side dina ba sai na Uban da ke son
yar sa, sai dai ki sani wannan uban " ya fi son zumunci fiye da
yan sa".
Ni da dan uwa na Gidado bayan kasancewar mu ciki daya iyayen ku mata ma cikin su daya, ki gayamin akwai wanda zaki aura ya rike ki da daraja da ya kai Omar? Don haka ki duba wannan kusancin ya wuce duk yadda kike tunani, babu inda zan kai ki sai hannun Omar sai idan bana raye, zan tabbatar kuma kafin na mutu na barwa Ummati wasiyyar ko kin mutu a fara kai gawar ki gidan Omar kafin a zarce da ita makwancin gaskiya
Daga haka ya tashi ya bar falon yana jin wani irin bakin ciki a ran sa, sakayyar da Siyama zata yi musu shi da Omar kenan? Lallai dan yau ba'a taba ci masa alwashi.
******
a zan iya tantance how I reacted ga maganganun Abba na ba, bayan wucewar sa saman bene, abinda na sani kawai shine Abba da gaske yake yanzu kam, kan hada mu aure ni da Ya Umar, wanda ke garin Calabar a halin yanzu yana kammala hidimar kasa bayan kammala digirin sa da (first class result) kamar yadda Abba ke masa buri. Na tattara warning din Abba na jiye a gefe don ban dauke shi a matsayin abinda zai dame ni har ya hanani kwanciyar hankali ba, yadda nake da tabbacin Abba na so na kamar yadda yake son kan sa, na tabbata ba zai taba yi min auren dole ba.
Idan na kafe akan ra
ayi na nan gaba inada yaqinin Abba zai janye nasa, musamman inna tsaya akan baka na na cewa ba son sa ne bana yi ba, girman sa da nake gani ne yasa bazan iya auren sa ba, ai Ya Omar bai yi kama da mazan da suka rasa matar aure ba, farin jinin sa kamar na Abba yake lokacin da yana jami
ar Jos, su ake cewa ana so ba su suke cewa suna son matan ba sabida kyawun surar da Allah yai mana.
A gani na Ya Omar ya fi karfin ya auri matar da bata masa so na soyayya, wannan kwaruwa ce a gare shi ba kadan ba. I have ambitions, i have plans, na yin rayuwar soyayya da mijin aure na kamar ba abinda muka zo yi a duniyar sai bautar Allah da kuma SOYAYYAH! Kasancewar Allah ya halicce ni da zuciyar da bata son komai daga mijin auren ta sai soyayyah.
Shakuwar mu da Omar tayi karfin da ba zan iya rayuwar aure da shi ba, meye bai sani ba nawa? Me zan yi ya burge shi?
There
s nothing special
da zan yi in ja hankalin sa da sunan soyayya, haka shima. (A tunani na).
Mutumin da ya gama goya ni a gadon bayan sa ya kuma gama yi min tsarkin kashi da fitsari! Na fara kirgan dangi da haila akan idanun sa. Ya sanni a sanda nake
yar sama tsami tsaka tsami na, wallahi ba zan yi kaffara ba in nace ban iya auren Ya Umar. Idan na yarda na aure shi zan kware shi kuma zan kwari kaina don ba zan iya hada shimfida da shi ba.
A daren yau na yi mafarki da DREAM HUSBAND dina, irin mafarkin da ban taba yin irin sa ba tunda na fara mafarkai na a kansa; na gan mu ne a wata alkarya da tafi kama da korran ciyayin tsaunin Mambilla, cikin wata irin rayuwa ta soyayyahr da ke tsakanin mata da mijin ta kadai, wadda ma
aurata kadai ke tsintar kan su a cikin irin ta.
Lamarin da ya tsorata ni ya firgita ni har ya saukar min da zazzabi-zazzabi. I can hear his voice clearly kuma yau na haddace ta kamar karatun sallah a cikin kai na.
Koda na farka daga barci amon accent din sa wanda ban taba jin mai irin sa ba sakamakon tangardar harshe da yake da shi, kuma kamar harshen Hausa naji yana yi cikin 'yar sassarfa ta magana da yake fama da ita, amon muryar sa irin na Asians bai bar amsa-kuwwa a kunnuwa na ba, yana maimaita kiran suna na cikin shauki na soyayya wanda miji kadai zai iya yiwa matar sa magana cikin wannan yanayin da na gan mu cikin sa.
Na kasa fita in taya Anty hada breakfast yau kamar yadda na saba a dalilin zazzabin da ya ci karfi na ya rafke ni a kan gado, na koma cikin duvet na cigaba da kwanciya ina kakkarwa. Na kuma tabbata a yanayin dana samu kaina wankan janaba ya kamani, janabar da na san ban aikata ba. Shin ko dai aljani ya aure ni ne wanda nake jin ana cewa haka suke auren bil adama? Sai gani yau ina kuka rurus ina neman agajin Ubangiji a kan wannan Jinnul Aashiq.
Tsoro mai tsanani ya shige ni. Ina wankan ina jin kunyar hakan kamar na aikata zunubin da gaske. Maimakon in yi addu
ar Allah ya raba ni da shi sai na bige da addu
ar Allah ya bayyana min shi kawai muyi aure, ko aljanin ne INA SON SA HAKA!
Da farko Anti ta kyale ni bata neme ni ba don itama a kule take da ni kan maganganun dana gayawa mahaifi na jiya wadanda ita kadai ta san cewa basu bar shi yayi barci ba.
Yau din ta kasance Lahadi kuma ta kama rana ce ta hutun Ma'aikata (international worker's day) daga Abba har Anti duk suna gida, data ga shiru - shiru bata ji motsina ba har ta gama hada abin kari sai ta biyo bayana tana tambayar.
"Lafiya dai ko Siyama?
Daga kwancen da nake dukunkune cikin Duvet na bata amsa.

Anti kai na ke ciwo da zazzabi
maimakon ta tausaya min kamar yadda na san ta da tausayi akan ciwo, sai ta kyabe baki ce
sabida an tuna miki maganar da tun haihuwar ki kin san da ita, tuna miki kawai aka yi ba sabuwa bace, shi ne kika sakawa kan naki damuwar data haifar miki da ciwo? To Allah ya sauwake, inda alkawari dai ruwa bazai dafa kifi ba!
Tasa kai ta yi ficewar ta ta barni da tunanin ma
anar Karin maganar ta..
Chapter 14 · 0% Book details