Sashe 12
Sakacin Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Oh! Ummati ban taba sanin haka tsafta yake da dadi ba, ashe da ba karamin cutar kaina na ke ba da nake zama cikin kazanta, ko'ina na tsami, yanzu fa Ummati da zan wuce ta gaban ki bazaki gane ni ba, gashi ke wayar ki Raka-ni-kashi ce (nokia) balle in yi hoto in turo miki ki ganni, ki ga yadda na koma, in kin ji irin kamshin dana ke yi kamar a kasar da ake sarrafa turare (Paris) din Faransa aka ahaife ni. Kai Allah dai ya yiwa Aunty Wasila albarka, ashe da can ni tantagaryar kazama ce ban sani ba Ummati?
Ummati dai sai dariya take tana jin dadi a ranta. Na cigaba da fada mata.
"Ashe Anti Wasila ba takura min take yi ba so na take yi da alkhairi kamar yadda Ya Umar ke yawan cewa? Ummati don Allah kullum kika yi sallah ki ke yi mata addu
a kin ji? Kice Allah ya bar ta da Abba na, Allah yasa ta haifa min kanne masu yawa
Kafin Ummati ta samu zarafin amsa min na ji tafi raf-raf a kaina. Daga kan nan da zan yi sai nayi ido hudu da Anti da Abba a bakin kofar shigowa suna kallo na suna tafa hannayen su, da alama sun gama jin duk abinda na gama fadawa Ummati na. Kunya ta kama ni, nayi saurin rufe fuska da tafuka na. Nace.
"Abba da Anti, Allah ya hana labe".
Dariya suka yi su duka. Abba yace
mu bamu labe ba shigewa zamu yi muka ji ana ambatar mu.
Sai in ce "Aamin to all your beautiful Du
as Siyama. Get ready for school tomorrow. Anti Waseelah zata sauke ki a Regent, kafin ta wuce nata aikin
Na rasa murna zan yi yau ko bakin ciki, don dai na san a da can na ki jinin karatu kamar yadda na ki jinin mutuwa ta, amma wallahi yanzu ji nayi ina shawagi tsakanin farin ciki da doki, wadanda duka suka taru suka mamaye ni duka a lokaci guda. Na soma jerowa Anti tambayoyi.
"Amma dai makarantar basa duka ko Anti?"
Cikin rashin damuwa tace
in kin yi laifi me zai hana a duke ki?
Nace
ai ni matsala ta da makaranta Anti guda daya ce kin sani. Assignment/Homework da classwork, idan babu su to komai zai tafi lafiya kalau.
Idan kuma kin yarda kullum na dawo gida zaki dinga yi mini da kan ki shike nan
. Anti ta dubi Abba tana fadin "saidai Abba yayi miki ya fi ni iyawa". Abba ya girgiza kai ya wuce sama yana fadin
Siyama har yanzu da sauran ki, bansan yaushe zaki girma ba
Washegari Anti ce ta taimakamin na shirya tsaf cikin sabon uniform dina na daliban Regent, nayi matukar kyau kamar ba ni ba, na kawo mini hijab kalar uniform din na dora a kai, kai bazaka taba cewa nice wadda ta zo daga Mambilan nan firgai-firgai dani watanni ukku da suka wuce ba.
Anti ta kai ni har makaranta ta karasa cike - ciken takardun da ya saura ba'ayi min ba, tukunna ta tafi ta bar ni cikin dalibai 'yan uwa na, wadanda duka 'ya'yan manyan ma'aikatan Abuja ne.
Na lura daliban makarantar kabilu sun fi hausawa yawa, hausawan kuma wadanda sune (minority group) duk
yan girman kai ne, don babu wacce ta kula ni, basu san ni nafi son hakan ba, don dukkan su da lafiyayyen turanci suke magana, wanda ko come din su bana ganewa sabida yadda suke furtawa a gwanance, nikuwa ko sentence guda daya kwakkwara mai kyau bazan iya hada miki a wannan lokacin ba. A hakan kuma wai na gama juniorclass a garin Gembu, nan kuwa a aji biyu na sakandire aka barni wato an maida ni baya.
Ana gab da tashi wata yarinya ta zo kaina ta tsaya tana min magana, da muryar ta mai sanyi, in zan girmeta to bazai fi da shekara daya ba.
Ke ya ba kya note?
Ta tambaye ni da Hausa, jin ta yi min husa sai naji dadi, na bata amsa da tawa hausar da ba fita take sosai ba,
shai gobe jan yi?
Shaboda me? (Itama ta kwaikwayi baki na). Bata jira amsata ba ta cigaba da cewa "Idan Mr Kehinde yazo karbar Assignment gobe baki yi ba zai baki punishment
me ye kuma punishment?
Na tambaye ta, babu girman kai babu raini ta amsa min tace "horo, zai saki shara ko wankin toilet din sa, ba ruwan sa da ko ke 'yar waye a garin nan
Ban san sanda nace
ai gara min punishment din da wannan uban rubutun, hannu na ciwo zai yi, baya na ma qagewa zai yi, na dade ban yi rubutu ba gaskiya
na bata dariya sosai ganin yadda nake magana da iyakar gaskiya ta, ta ce,
da alama ke 'yar auta ce
nace
ba wata auta fa, don kuwa Anti na tana da ciki yanzu haka. Kuma ta yi min alkawarin samun kanne duk shekara
na kara bata dariya tace
ya sunan ki don Allah? I like you
sunana Aishatu Mamman Dalhatu Gembu
ni kuma suna na
Azima Salim Ko
oje. Mu 'yan Sokoto ne. Kina iya kira na Ko'oje. Aisha can we be friends?
Ta fada tana miko min hannun ta, na mika mata nawa muka yi musabaha irin ta muslunci, ta samu wuri gefe na ta zauna tace.