Sashe 2
Sakacin Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mambillah, the coolest wheather in Nigeria - (Wikipedia-Britannica) Mambilla ya zama tourist attraction na jihar Taraba sakamakon ni imar sanyi da Allah ya yi wa garin da sauran albarkatun kasa da bazasu lissafu ba. Geographers da yawa sunyi rubutu a shafin wikipidia a kan tsaunin Mambila, haka masu binciken albarkatun kasa (soil scientists) sun tabbatar da cewa akwai Zinare da Shudin Yaqutu (Gold and Blue Sapphire) kwance a cikin kasar Mambilla Plateau, wasu marubutan ilmi kuma sun yi ittifaki a kan garin Mambila wanda sam gwamnati bata maida hankali akan albarkatun sa ba, da cewa; da gwamnatin Najeriya zata maida hankali a kan sa da ya tabbata Heaven on Earth din da ake kiran sa da shi ko kuwa ya zama tamkar kasar Dubai a Najeriya. Hanyar zuwa garin Mambilla kan shi a kan dutse yake, wanda ya taho daga garin Jalingo. Mambilawa wato yan asalin Gembu basu cika ji ko yin yaren harshen hausa ba musulmin su da kiristocin su. They have a very strong Fulfulde accent wanda ya bambanta dana dukkan fulanin Najeriya. Kauyukan da ke yankin Gembu sun hada da; Tunga, Maisamari, Yelwa, Gurgu, Sabon gari da kuma Nguroje. Kafin zuwa garin Gembu sai ka fara isa Numan ta jihar Adamawa, sannan ka dauki hanyar Taraba, tafiyar awanni biyu a tsakani kafin ka iso Jalingo, daga nan ne zaka dauki hanyar da zata kai ka Gembu, tafiyar awanni takwas a tsakani kafin ka samu isa Gembu. Don haka tafiya daga Kano ko Kaduna zuwa Gembu tafiya ce mai nisa ta tsahon awanni 21-22, tafiyar kwana daya kenan cur, idan har ba mutum ya yi transit (matsaya) a garin Jalingo ba. Kasashen turawan yamma sun maida Gembu tourist destination na Taraba, ba ka raba Gembu da bakin jar fata lokaci-lokaci suna daukar hotuna a cikin motocin su masu budadden sama. Ba turawa kadai ba duk ma wanda ya san ni imomi da albarkatun da ke tattare da Gembu kuma ya ke da halin zuwa to kuwa zai so ya kai kan sa yawon bude ido wannan gari namu mai dimbin albarka, don hutawa da karin fadadar ilmi, musamman in ka kasance mai son karin ilmi a kan geographical setting na kasar Najeriya. Gembu na kusa da wata karamar hukuma mai suna Gashaka, inda a can ne Gashaka Gumti National Park ya ke. - GEMBU; Garin da ya tara tsala-tsalan yammata mafiya kyawu a Najeriya - (Saliadeen Sicey). Da zarar ka fara haurawa kan tsaunin Mambila daga wani tsauni da ake kira Mayo Selbe da ke karamar hukumar Gashaka, zaka hangi Tsaunin Mambilla mai tudun gaske lullube da korran ciyayi da wasu irin dogayen bishiyoyi da yayyafin hazon kankara ya yi musu mayafi, don wasu lokutan kankara har zuba ta ke. Dalilai da yawa zasu sa ka son ziyartar Gembu; na farko zaka so ziyartar garin Gembu ko don ka ga tsala-tsalan matan da Allah ya halitta a can, in kai mai son zane-zane ne har ka so ka zana su da alkalamin ka, ka sha fruits nunannu iyaka shan ka (musamman Piya), ka sha danyar madara da nono kindirmo iyaka yunwar ka, ka ji ni imar sanyia jikin ka da zuciyar ka iya ka jin ka, ka ji kamar ba a kasar Najeriya ka ke rayuwa ba, ka kuma amfana da tarin albarkatun kasar da ke tattare da garin, ka kara girmama girma da buwayar karfin ilmin halittar ubangiji. ***** UMMATIN MAMBILLAH! mmati, sunan Kaka ta kenan wadda ta haifi mahaifi na. Sunan ta na asali Saudatu, ni na saka mata suna (Ummatin Mambila), kasancewar ita ta raine ni, daga madarar shanun ta mai dumi da gardi da ta zama makwafin nonon uwa a gare ni a wancan lokacin. Ban taba sanin dumin jikin mahaifiya ta ba sai na Ummati, na san fuskar ta dai a hoto kan wani tsohon farin hoto marar kala daukar zamanin da, da Ummati ta taba nuna min, sai naga ba maraba da tawa fuskar banda kuruciya dana fi ta, duk da cewa sanda aka yi hoton ma da tarin kuruciyar ta don bata cika shekaru ashirin ba. Kuma Ummati ta sha gaya min da kuruciyar ta ta rasu. Sunan Ummati da na lankaya mata tun ina koyon magana shi ya bi ta a bakin ya da jikokin ta, dama jama ar garin Mambila baki daya, ita da kan ta Ummati ta ke kiran kan ta da kanta, Saudatu ya dade da bacewa a bakin kowa. Ita da mijin ta mai rasuwa Malam Dalhatu yan asalin garin Gembu ne, iyayen su da kakannin su sune tushen kabilar Mambila, wato wadanda sune yan asalin garin Mambillan tun daga iyaye da kakannin su, aka kuma haife su a nan, suka girma suka yi aure suka rayu tsayin rayuwar su a nan. Malam Dalhatu Abdullahi Gembu, ya rasu ya bar matar sa Ummati da ya maza guda uku, Gidado da Mamman wadanda shekaru biyu ne kawai a tsakanin su sai suke tamkar tagwaye a idon mutane, sai kuma autan Ummati wato Baffa Adamu wanda suka baiwa ratar shekaru kusan bakwai. Wadannan zaratan ya maza guda uku na Ummati duka sun tashi sun girma tare karkashin kulawar ta da jajircewar ta a kan kiwo da sana ar saka da ta ke yi don ta tallafi maraicin su a bayan ran mahaifin su. Ban taba ganin jarumar uwa irin Ummati ba. Wadda ta tsaya tsayin daka wajen hada kan yan ta da daukar dawainiyar su ta yadda basu taba kukan basu tashi tare da mahaifi ba. Lokacin da ta tashi yi wa Gidado da Mamman aure sai ta yi takakkiya ta tafi har makwabtan su garin da ake kira kauyen Gashaka, ta nemo musu auren Yaya da kanwa yan asalin Gashaka masu nasaba mai girma sabida tsoron ta na kada mace ta raba mata kan su. Asshe da Hassu yan wani attajirin bafillace ne a Gashaka, in aka ce miki attajirin mutum a Mambila to fa ba tsabar kudi ko tarin dukiya ya bashi wannan sunan ba, a ah; yawan dabbobin ka da gonakin ka na gado sune arzikin ka a Mambila. To ita kam Ummati ba ma wannan ta duba ba wajen aurawa Gidado da Mamman Aisha da ake kira (Asshe) da Hafsatu da ake kira (Hassu) illa duk fadin garin Gashaka su ne yaran da aka tabbatar sun sauke Al qur ani sun kuma haddace shi kafin su cika shekaru goma-goma. Hassu da Asshe yan biyu ne masu kamanni daya basu taba yin karatun boko ba sai na addini. Wanda ya sanya suka zama yammata masu nutsuwa da tarbiyyah ababen rububi a wajen samarin Mambilla, kowanne uba da kowacce uwa fatan su a auro musu zuriyar Muhammadu Jauro, ga kuma kyawun sura da Allah ya basu. Gidado da Mamman ra ayi ya banbanta a kan abinda suke so a rayuwa, yayin da ilmin boko ya kunno kai a Manbila wasu sun karbe shi da hannu bibbiyu musamman kiristocin cikin su, wasu kuwa musaman musulmi suna tababa a kan amsar shi, wasu da yawa sun yi hannun riga da shi ne da cewa sakon missionaries ne. Mamman dai ya karba da hannu bibbiyu ya shiga makaranta yayi firamare da sakandire yana kuma hadawa da kiwon shanun su na gado da noma duka bai bar Gidado da wahala shi kadai ba, Gidado ya yi wa kansa Allah ya kiyaye da boko ya maida hankali wajen kula da mahaifiyar su, daga noman da kiwon babu wanda ya dame shi ya fi gane ya tara yara a a zaure yana koya musu karatun Al ani, a kowanne karshen sati iyayen su su bashi sadakar kudin Laraba. Da haka ya zama malami sosai har manya yake karantarwa littafan addini a Alhamis da Juma ah. Dan autan Ummati kuwa wato Baffa Adamu har ya fi Mamman son boko, Ummati kuma ta basu dama kan kowanne ya yi abinda yafi so in dai ba sabon Allah bane. Ta sadaukar da shanun gadon su masu yawa kafin a bawa Gidado da Mamman auren Asshe da Hassu. Gidado ya auri Hassu, Mamman ya auri Asshe. Gidado shi ya fara samun rabo shekara na zagayowa Hassu ta haifa masa Umarul-Faruq. Yaro tamkar khaki (photocopy) na mahaifin sa Gidado. Asshe kuwa shiru, tun ana saka rai har an hakura, da abin ya dame ta duk inda ta ji mai bada maganin haihuwa sai ta je a boye ta karbo sassake don idan ta bari Gidado ya sani zai sata a gaba ne yana mata wa azin Allah kadai ke bada haihuwa, ta yarda Allah ke bada haihuwa amma shi ya ce tashi in taimake ka. Lura da damuwar Asshe da Ummati ta yi a kan haihuwa. Da Faruq ya isa yaye sai Ummati ta dauke shi ta baiwa Asshe. Don farin ciki Asshe saida tayi kuka a lokacin ita Hassu goyon ciki na biyu take yi. Asshe ta dauki Umar ta rike da dukkan kaunar duniya da kulawar data fi wadda yake samu a gun mahaifiyar sa. A wajen haihuwar na biyun ne sai ya zo da karar kwana Hassu ta rasu tare da abinda ke cikin ta. A wancan lokacin zautuwa ne kawai Malam Gidado bai yi ba sabida mutuwar matar sa uwar dan sa abokiyar rufin asiri, Hassu. To kuma ina ga yar uwar ta da suka fito daga mahaifa guda suka yi yarinta da kuruciya da aure tare? Da kyar da kuma rokon Allah har da rubutun dangana Ummati ta samo kan sa, ya koma karantarwar sa kmar yadda ya saba. Malam Muhammadu Jauro wato mahaifin su Hassu ya ce inama ina da wata diyar! Da na baiwa Gidado, domin ban taba yin surukin da ya san darajar mace kamar sa ba, amma duka na aurar da su Tun daga lokacin Baba Gidado ya dauki soyayyar duniya ya dora a kan Ya Umar, Inna Ashe kuma ta goya Umar - Faruq goyo na amana bata da lokacin kan ta sai na Faruq, bata da hidimar kowa sama da tasa ko mijin bata bashi lokacin da ta ke baiwa Faruq, koda yake ai dama Dan ta ne tunda kuwa shaqiqiyar ta ce ta haife shi. Wadda har ta rasu tana gaya mata a kullum ke na haifawa Umaru dan ki ne halak malak Auren Asshe da Mamman ba jimawa gurbin karatun sa da ya nema