Sashe 23
Sakacin Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
suka ketowa Abba Dr. Mamman Gembu. Omar ya gudu! A dalilin Boddo bata son sa. Kuma yana ikirarin idan har Abba bai janye ba ko bayan shekara ukun da ya ambata ne ba zai dawo ba. Jikin Abba yayi mugun sanyi, ya saki takardar a kasa kawai sai ya juyo, da ni muka yi ido biyu idanuna a bubbude domin na fuskanci abinda ke faruwa Ya Omar ya zabi ya bar gidan mu akan dai Abba ya tursasa ni ga auren sa, kafin na ankara Abba ya yo kaina, ya soma duka na ta ko'ina da hannaye da kafafun sa iri dukan na huce bacin rai. Anti ta sa kuka ta rufu a kaina ta ce "gara kayi mana dukan tare. Yadda Omar ya ke Da a gare ka itama 'yar ka ce mai 'yanci. In shi maraya ne itama marainiya ce. Tana da damar ta auri wanda take so, tsaurin ka ne ya janyo komai, ka san Umar son da yakewa Boddo ba zai bari ya zabi nasa farin cikin akan nata ba. Abba yace "to kuwa bazata zauna min a gida ba, yadda Omar ya bar gidannan itama sai ta bar shi, bazan haifi dan da ban isa in tankwara ba". Kuka nake ina baiwa Abba hakuri na kuma ce zan nemo masa Ya Omar, zan kuma aure shi koda bana son sa..... Wannan kalma ita ta kara tunzura ran Abba, yace "kada Allah yasa ki so shi, ki sani daga yau nima na janye maganar aure a tsakanin ku, kije ki auri duk wanda kikeso Boddo, amma ki tabbata kafin na dawo gidannan kin bar min gida na." "Kada ka yi wa 'yar ka baki Mamman!" Anti ta tunasar da Abba cikin yanayi na rauni, Abba ya ce "ban yi mata baki ba ai, amma na janye nawa kudurin, na janye nawa burin don in samu Da na ya dawo gare ni. Ya fiye min ita sau dubu, kuma lallai -lallai yanzunnan ta bar min gida na". Anti zata kara magana Abba ya rufe idanun sa ruf, ya ce da ita. "Idan kika kara kare Boddo a ido na, ko kika kara nema mata alfarma ko afuwa daga gare ni a bakin auren ki". Wannan magana ba Anti kadai ta firgita ba har da ni. Ina jin sanda fitsari ya kwace min daga tsayen dana ke. Abba ya nuna min kofa da dan alin sa yace "kama hanya ki bar min gida na". A yanayin dana ga idanun Abba sai naji tsoron sake furta wata kalma, na tabbata in yi masa abinda ya bukata daga gare ni shine kawai mafita ta a wannan lokacin. In yaso daga baya idan ya huce na dawo na bashi hakuri. Ni kuka Anti kuka Jamila da Nadiya kuka haka na dau jakar kayan da Anti ta hada min na fito, babu ko sisi a jikina kuma bansan ina na nufa ba. A bakin gate maigadin mu ya biyo ni ganin ina tafe da jaka ina kuka wiwi, ya ce "uwardaki na kada kije ko'ina bada yardar iyayen ki ba, babu wata albarka a cikin sabawa iyaye kuma babu kwanciyar hankali cikin bijirewa umarnin su". "Abba shi yace in tafi Baba Dattijo, biyayya na yi masa zan tafi". "To kada kije da nisa, nemi wani waje mara nisa cikin gidajen yan uwa ki fake zuwa gobe idan zuciyar sa tayi sanyi ki dawo ki bashi hakuri ki kuma bi duk umarin da yayi miki". Na yarda da maganar Baba Dattijo amma ina zani? In ba gidan su Anti ba sai ko gidan su Ko'oje, wannan kuwa matsala ce ta cikin gida da bata bukatar third party, gara kawai in wuce Gembu gun Ummati ko kashe ni zata yi itama tayi, ita kadai ce zata iya shawo min kan Abba. Duk da yakinin dana ke da shi na cewa bazata taba bin bayana ba itama. "Ka taimaka min da kudin mota in tafi Mambila gun Ummati", Baba Dattijo ya sanya hannu a aljihun sa yana lalubawa yana cewa " anyi sa'a jiya Abban ya bani albashi na, gashi duka 'ya ta ki je kafin ya huce, ki kula da kan ki, nasan baki taba zuwa Gembu a motar haya ba, don haka muje in saka ki motar Numan". Shi ya daukar min akwatin ya tare mana drop wadda zata kai mu Jabi park, Baba Dattijo ya saka ni a motar Numan ya kuma gayawa direban ya saka ni a motar Jalingo in an je Numan. Sannan ya ce "daga Jalingo zaki hau motar Gembu amma ki nemi ko gidan mai unguwa ne ki kwana a Jalingo in yaso kiyi asubancin shiga motar Gembu". Nayi wa Baba Dattijo godiya kamar halshe na zai tsinke, kamar yawun baki na zai kafe. Sai yace "yar nan babu komai Ubanki mutumin kwarai ne babu abinda baya yi min nida iyali na tun da ya dauke ni aiki yake faranta min. Allah ya kai ku lafiya, Allah kuma ya huci zuciyar sa". Ya sayo kosai mai zafi da soyayyen dankalin hausa aka kumshe masa a leda da takarda ya miko min ta taga. Baba Dattijo bai bar wajen ba sai da ya ga tashin motar mu. Muna dagawa juna hannu hawaye sun ki tsayawa a idanu na. "Yau ga abinda ka janyo min Dream Husband, yau ga inda soyayyar gaibun ka tayi da ni; kora daga Abba". Ji nayi na tsani kaina iyakar tsana, na tsani soyayyar da nake masa amma shi din, nayi nayi in tsane shi na kasa. Na dauki alhakin komai na daurawa kaina. Tunda shi bai san ina yi ba. Ba kuma shi yace in ki zabin Abba na ba. Tafiya ta mika mana sosai muka naushi Arewa maso gabashin Najeriya. ****** ai dare muka isa Numan, na rasa yadda zan yi ga gajiya ga yunwa, karo na farko dana shiga motar haya zuwa Gembu don ma dai Direban da Baba Dattijo ya baiwa amanata yayi ta kulada ni har muka iso Numan. Kuma da muka sauka daga motar sa saida ya tabbata na samu wajen da zan kai zuwa wayewar gari wato gidan sarkin Tasha, na kwana a dakin matar gidan, washegari Asubah na yi nayi sallah na yi harama tasa aka rakani na koma tasha aka sanya ni motar Mambila. Hankali na bai kwanta ba saida na fara jin sanyin yankinmu na Mambila a cikin jiki na, na hango tsaunin Mayo-Selbe, na tuna kuruciyata mai dadi a Mambila. Sai na ji rabin damuwata ya yaye ko ba komai watakila yadda na baro Abuja haka na baro duk wani memories dinsa a can. Sai kuma na tuna ai al'amari na da shi ya fara ne tun a Mambila ba a Abujar na samo ba. Wanda ke nufin watakila da soyayyar sa aka haife ni. Babbar damuwata Abba na yayi fushi dani ban san ranar da zai huce ba. Yaya Umar bani da haufi akan sa na san shi din namiji ne, wanda a ko'ina zai iya kula da kan sa kuma ba zai taba kai kan sa ga halaka ba. Ummati na kishingide a falonta tayi shimfidar siririyar katifar da take hutawa a kai, a gefe kwarya ce cike da kindirmo mai sanyi da radio a kunne tana saurare. Ko sallamar dana yi mata bata ji ba kasancewar murya ta ta dakushe iyakar dakushewa sabida yunwa da jigata. Sai gani na tayi a gabanta wurjanjan da ni. Tunda na zube a gabanta na shide na wasu mintoci sabida galabaita da yunwa, salati da sallallamin da Ummati ke yi hade da hamdala shi ya saka ni kara lumshe ido na. Ina ji tana shafa min ruwa a fuska kafin ta dago ni ta rike a jikin ta ta kafa min kofin danyar madara a baki. Kulawa iri - iri Ummati ta shiga yimin saida ta tabbatar na dawo hayyaci na. Ba jimawa kuma sai barci a gadon Ummati. Barcin da ba ni na farka ba sai safiyar washegari. A daren Ummati tayi waya da Abba ta gaya masa gani na zo mata hajaran majaran ko lafiya, budar bakin Abba sai cewa yayi "Ummati sallameta ta kara gaba, tunda ta yi sanadin salwantar min da Umar bata da sauran amfani a gabana itama". Ummati na iya jin irin numfarfashin da Abba ke yi domin a lokacin yana ta neman Umar sama da kasa cikin garin Abuja da wajen ta, ya kuma yi wa Wasila iyaka da magana ta yayi mata togaciya da igiyar auren ta don haka Wasila ta rasa abinda ya kamata ta yi tun bayan fita ta. Daga baya ne Baba dattijo ya kira ta a waya ya shaida mata cewa ya kai ni ya sakani a motar Numan ta yi min addu'ar sauka lafiya. A lokacin ne ta dan samu nutsuwa har ta so bugawa Ummati waya, amma data tuna gargadin Abba dole ta bari, ta koma addu'ar Allah ya kai ni lafiya. Ummati ta ce "ban gane ta zama silar salwantar da Faruku ba" Abba ya ce Ummati doguwar magana ce da bazata yiwu ta waya ba". Tace "to lallai-lallai gobe kuzo kai da Wasila ina neman ku". Sai dare na fara murmurewa, tambayar duniya Ummati ta yi min kan me ya hada ni da Abba ban ce komai ba. Ta tambayeni Ya Faruk da yadda aka yi suka barni na taho nikadai haka nan ma ban tsinka mata ba sai goge hawaye da nake yi lokaci-lokaci don nasan duk wannan kulawar data ke bani itama in taji abinda na aikata kuma na bijirema auren Omar sannan ya bar gida sabida ni, zallar kiyayya zata koma watakila har sai ta fi ta Abba. A haka muka kwana nida Ummati cikin dare ina kallon ta tana ta sallah tana addu'a kan Allah ya kare mata zuri'a ya albarkace su ya cire rabon shaidan daga zukatan mu, don ta fahimci al'amarin duk da ya rabo ni da Abba ba mai dadin ji bane, tunda yau har Abba ke fadin itama ta kore ni kamar yadda ya kore ni. Abba da Anti basu samu isowa Mambila ba sai bayan kwanaki biyu, lokacin har na ware damuwa ta yi min sauki. Na yarda kwanciyar hankali na shine in manta da shi, kamar yadda Omar ya fadawa Abba cikin wasikar sa, "Ba kowanne mafarki ne ya