← Book details Sakacin Waye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 28

Sashe 26

Sakacin Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wani shiri na tafiya tare da su a cikin alfarmar iyalin sa. Ranar wata Litinin babbar rana muka sauka a birnin Washigton D.C din Amurka, inda acan ne headkwatar US Diplomatic Mission yake. Gidan Young Abba bashi da nisa da ofishin su. Tun saukar mu a kasar Amurka na samu nutsuwar data yi min karanci, Aunty Nasara kuma ta maida hankalinta kacokam kan zaryar asibiti akan matsalar haihuwar ta don ita ke da matsalar ba shi ba. Ta kan ce a kullum in yi mata addu'a Allah ya bata haihuwa ko guda daya ne, idan Young Abba yayi mata kishiya mutuwa zata yi sabida kishin sa. Kalaman ta na bani dariya a yawancin lokuta, sai kuma in ga in nice nima hakan ce zata faru dani, muddin wanda nake so na aura kamar ta. Sau tari ni kadai nake wuni a gidan, ba da jimawa ba Young Abba ya mallakamin wayar hannu, yace sabida su dinga jin halin dana ke ciki idan basa gida. Wato kadaici da kwanciyar hankalin dana samu sai ya dawo da bara bana. Na koma mafarkaina da shi, abin har yayi ta'azzarar da ya zarce na baya. Na kuma fi jin closeness dina da shi cikin zuciyata a garin Washington fiye da gida Najeriya. Saina koma nemawa kaina hanyoyin debe kewa da zasu rage min feelings din dana ke ji a kan sa, na abokantaki Talbijin a halin yanzu. Na zama mai bibiyar VOA TV: AMURKA. Kullum ranar Allah sai na kalli labaran VOA TV har Aunty ta canza min suna zuwa Siyama-VOA, don tace ta ga alama ina yin su sosai. Na sha kona mana girki akan kallon TV Programmes na VOA. Har ta kai ta kawo Aunty Nasara ta daina bar min girki yanzu, ban san abinda ke fizgata ga son sauraron su da kallon su ba. Face wani abu tamkar magnet dake jan zuciyata yake fizgata akan gidan talbijin da radio na VOA tunda na tabbata bana raba dayan biyun a can ne na fara jin real sautin sa a radion Abba na. ******* SILENT ENCOUNTER imanin watanni takwas kenan da dawowar mu birnin Washington. Na gyagije na zama goyon 'yar gayu Aunty Nasara na yi tsaf da ni kwanciyar hankali ya wadace ni. Weather din birnin Washigton ya ratsa fatar jiki na. A yau shirin da VOA suka sako a safiyar yau is a Live TV Programme. Kwance nake a cikin sofa-bed ina cin gugguru, ina kuma kallo, a gefe ga hot coffee na hada sai turiri yake. Na mike zaune ina kurba ina cin gugguru kafin kuma na maida hankali na ga makekiyar talbijin din dake manne jikin bangon daki na na gidan Young Abba. Kimanin watannin mu takwas da zuwa Washington kenan. And there was where it all happened. Today I saw HIM!!! Bayan sallama ga masu saurare, tare da gabatar da kan sa a matsayin sa na Broadcastern VOA mai amsa sunan "Hamzah Almustapha Mawonmase". Sai ya fara gabatar da shirin sa LIVE na vedio tare da mara lafiya "Adam Toobin" mai fama da lalurar Celebral Palsy...... cikin harshen turanci daga sashen turanci na VOA. Hamzah ya cigaba da kwararo bayani kan lalurar Toobin..... "....... OVERCOMING OBSTACLES.....". Taken shirin sa kenan. -"LIVING WITH CELEBRAL PALSY.....!!!". Shine shirin da Hamzah yake gabatarwa kai tsaye (live) tare -da mara lafiya Adam G. Toobin wanda ke kwance cikin wheelchair mutumin kasar Amurka ta kudu, wanda ke rayuwa shekaru talatin cikin cutar 'Celebral Palsy' ba tare da motsi ba. Baya motsi (movement) kamar kowanne dan adam bai kuma taba sanin menene lafiya ba, amma yana magana daga cikin kujerar sa, yana kuma gayawa duniya yadda yake rayuwa cikin wannan larura, yake kuma tafiyar da al'amuran kamfanin sa a haka, tare da koyar da ma'aikatan kamfanin yadda zasu tafiyar da al'amuran kamfanin, yana gaya musu hanyoyin magance matsalolin da suka taso wa kamfanin in oral form. Hamzah na tattaunawa da shi yana bada feedback yana kuma daukar sa a hoto da vedio din sa. (Shi ba fari bane, baki ne cikakken dan Najeriya, dogo haka siriri mai zankadeden dogon karan hanci, wanda ya tafi ya dan rankwafa kadan a saman bakin sa sabida tsayin sa). Mutumin nan ne mai tarin gargasa a fuska da saman giran idon sa, mai murya irin ta Asians mai sassarfar magana, maimakon Hausar dana san shi da ita yau turanci yake yi zallah. Bashi da kauri kuma babu annuri a fuskar, a lokacin da yake gabatar da shirin "....... OVERCOMING OBSTACLES...., LIVING WITH CELEBRAL PALSY.... !". Tamkar yana taya client din sa Toobin alhini da juyayin halin lalurar rashin lafiya na har abada da yake ciki. Yana sanye da farin siririn gilashi na kara karfin gani. Wanda na tabbata yawan duban camera ne ya yi mujazar lalaurar idanun nan. Sanye a jikin sa 'Black - Grey Japanese Suit' ne, ya matse wuyan sa daga ciki da tsukakken neck-tie fari sol. Exactly yadda nake ganin sa cikin MAFARKI na, exactly yadda nake ganin sa a IDO BIYU na, wato inimaginations... haka exactly yadda nake picturing din kasancewar sa! Sannan muryar bata canza daga yadda na santa na kuma haddace ta ba. Wannan shine HAMZAH ALMUSTAPHA ........ da na dade ina baku labari, wanda na rayu shekaru rututu cikin mafarkan sa, wanda na taba tsinkayar muryar sa a kunnuwa na daga gidan rediyon VOA watanni masu yawa a baya. Yau dai ga Hamzah na gani cikin idanu na, Hamzah a kan screen din talbijin din daki na, a kan allon talbijin dina.... In reality ba'a mafarki ba, ba kuma a sautin murya ba. Yau na ganshi ne ganin idanu na. Ina kallon sa ina kuma jin sa. Kwarai sunan da ya ambaci kan sa da shi a wancan lokacin ma da na kasa tunawa kenan HAMZAH ALMUSTAPHA MAWONMASE....!!! Amma a wancan lokacin kidima da ikon Allah basu bani ikon rikewa ko tunawa ba!!! Wani abu tamkar zubar kankara ya bi ilahirin jikina ya sankarar da ni a inda nake kwance. Zuciya ta tamkar ta fito ta baki na. Yawun baki na ya kafe rayas. Nayi kokarin hadiyar miyau don jika makoshi na da ya bushe kamas, amma na gagara yin hakan saboda kidima. Sakamakon haka na jin numfashi na na shirin barin gangar jiki na. Ko wanene wannan shine 'dream man' dina, da ya hana rayuwata sukuni, ya rabo ni da gidan mu da iyaye na, ya raba ni da Ya Umar, ya jefa rayuwata cikin kaka-nikayi, shine mutumin da ke zuwa min kullum cikin MAFARKI KO A IDO BIYU! Shine wanda Ubangiji ke nufin al'amura da dama a tsakani na da shi tun ban san kai na ba, wadanda ban san farkon su balle karshen su ba. Iya abinda na iya tunawa kenan sai na shide cikin emotion, kowacce gaba ta sassan jikina na maimaita kiran sunan "Hamzah Mawonmase!" Don kada in kara mantawa ko ya kara bace min in sake shiga halin ha'u'la'i. To amma sanin da na yiwa Hamzah a yau bashi da wani amfani tunda dai ba zan dauki kafa a matsayi na na diya mace bafullatana mai daraja in tafi ofishin VOA neman sa ba, in ganshi in ce masa me? Ai sai kima da daraja ta na diya mace su fadi. In nayi haka na siyar da mata, na siyar da fulanin Mambilah wadanda ko a cikin fulani daban suke. A hakan dai zan cigaba da kwankwadar azabar soyayyata ni kadai, har zuwa ranar da numfashi na zai kare da sunan Hamzah Almustapha a cikin sa. Ko babu komai yanzu zuciyata ta samu sa'idah, na cewa Hamzah mutum ne bil adama, yana rayuwa ne a gidan radiyo da talbijin na VOA. Kuma muna cikin kasa daya. Kuma Allah ya nufa na gan shi in a silent way. Zuciya ta ta yarda shine mutumin mafarki na dana rayu da shi tsayin shekaru kusan goma a zuciya da kwakwalwata. Koda wannan kadai na tsira ya ishe ni kwanciyar hankali har karshen rayuwa ta; HAMZAH ALMUSTAPHA is a human, living in America. ******* EMOTIONS ai ya kasance tun daga ranar dana gan shi a talbijin nake bibiyar sa, nake bibiyar komai nasa da wani irin emotion, yawanci na kan ga hotunan sa tare da sauran VOA TEAM na talbijin ko na radio, na kuma fahimci ba'a bangare daya yake broadcasting ba, yana yi a sashen hausa, yana kuma yi a sashen vedio na turanci. Wata irin walwala ta same ni a kwanakin nan, ba abinda ke bani nishadi irin kasancewar Hamzah mutum ne a raye ba aljani ba ba jinnul Aashiq ba, na koma bani da abin yi muhimmi irin na dinga bibiyar shirye-shiryen sa. Kullum da sabon shirin da zai kawo mai matukar muhimmanci da kayatarwa. Daga yadda yake gabatar da muhimman shirye-shirye a gidan radiyon da talbijin na VOA zaka fahimci dan gaban goshin su ne. Kusan duk wani shiri mai muhimmanci shi yake gabatar da shi. Watakila wannan ba zai rasa nasaba da zazzakar muryar da Allah yayi masa baiwar ta ba, mai wata irin sassarfar magana wadda ke karawa shirin sa armashi da jan attention din al'ummah, murya ce mai taushi da sanyawa dan adam nutsuwaka saurare shi koda baka ra'ayi, sassarfar ta kuma bata hana a gane me yake cewa cikin dadin rai. Sai take kara mata wani irin armashi. Hamzah na tafiya da zukata da dama ba tawa nikadai ba, na gane hakan ne ta hanyar comments da yake samu na miliyoyin mutane a shafin sa na Twitter da na Instagram a duk lokacin da VOA suka saki shirin sa. Babu cikakken bayani a kan sa a google amma akwai cikakken bayani na aiki da profession din sa a shafin sa na LinkedIN. Matakin Digiri dai-dai har guda uku reras yake rike dasu akan aikin Jarida daga Jami'ar 'Sussex'. He's a Chevening Scholar wato wanda yayi karatun sa na Masters daga tallafin 'Chevening', yayi Ph.D daga tallafin 'Commowealth Scholarship', cikakken dan Nigeria daga jihar Filato (Jos). Ya yi aiki na lokaci mai tsaho da British Broadcasting Corporation, yayi da Radiyon Jamani (Deustche Welle) kafin ya bari duka ya dawo uwar su VOA. Wadannan sune muhiman bayanan dana samu a kan Hamzahn da zuciyata ta ki hutawa a kan sa, daga shafin sa na professionalism wato LinkedIn. Suka zame min ababen taya hira,
Chapter 26 · 0% Book details