Sashe 5
Sakacin Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Jira ta ta fito Bashari, na san ta zaga ne, ga nan fura ka sha, bari in dibo Asshe cikin gida na ji kukan ta yayi yawa, yanzu haka Faruqu ke cin zalin ta
Ya saka takalmin sa ya nufi cikin gida da sauri babbar rigar sa na neman tadiye, shi don in da abinda yafi tsana a duniya to kukan Asshe ne.
Bakon da ya kira da Bashari kuma ya kafa fura a kai yana kwankwada don a yunwace yake ainun a matsayin sa na matafiyi, ko ludayin kan faifai din bai saka ba kada ya bata masa lokaci a yunwar da ya kwaso tun daga kasar Kamaru.
Yana sauke kwaryar daga fuskar sa suna hada ido da Yayar sa Jaru. Jaru ta kwalla kara tana fadin
na shiga uku na lalace Bashari furar Gidado ka sha??? Furar da na sakawa guba ce fa!
Yayi daidai da dawowar Gidado tsakar gidan tare da Ummati, ya na dauke da Asshe a kafadun sa. Omar na biye da su.
Suna jin abinda Jaru ke fadi cikin yanayi na rashin hayyaci cewa ya ci gubar data sawa Gidado don ya mutu ta auri Mamman, abin nata kamar kaikayi ne ya koma mata, kasancewar Gidado Malami ne ya dade yana yi wa kan sa da
yan sa tsari iri iri da ba dai mutum ba sai dai Allah.
Ko kafin su farga Basharin ya fara shure shure kumfa na fita daga bakin sa, sai kuma jikin ya saki bakidaya alamar babu sauran rai a jikin sa.
Wannan bakin al
amari da ya faru a gidan Malam Gidado babu wanda bai ji labarin sa a garin Gembu ba, aka saka Jaru a waka, hukuma tayi mata hukuncin da ya dace, Baba Gidado yayi alkawarin ba zai saki mace ba amma Ummati ta saka shi a gaba ta ce sai ya saki Jaru a take in yaso ya yi kaffara, wannan ba matar zama bace.
Wannan shi ya kawo karshen auren Jaru (Hadiza) da Gidado Dalhatu Gembu.
******
MALLAMGIDADO DALHATU GEMBU
akika ya firgita da al
amarin mata wanda ya kai shi ga cewa babu shi babu kara aure har abada, wai a kan kanin sa ta yi niyyar kashe shi, wannan wane irin rikitaccen zamani ne na son zuciya da rashin tsoron Allah Allah ya kawo mu? Da yake Shi fa
aalun lima yuridu ne sai Ya juya abin a kan dan uwan ta.
Shi kan sa Dr. Mamman Gembu da ya zo gari ya samu labarin ya firgita iya firgita, Allah ya tuba ko mata sun kare a duniya ai ba zai auri matar yaya Gidado ba koda mutuwar yayi ta Allah da Annabi. Shi kam! A lokacin ya kara jin tsoron duniya dana kaidin mata. Ya kama Omar - Faruq da Asshe dake zaune bisa cinyoyin sa ya rungume a jikin sa yana nema musu tsarin Ubangiji daga mugun ji da mugun gani da sharrin mutum da aljan. Ya roki Allah ya raya musu su har su aurar da su da hannun su shi da Yayan sa, ya yi alkawari tun a lokaci in har yana raye to Asshe bata da miji sai dan uwanta Omar, Omar baya da mata sai kanwar sa Aisha. Kada su je bare su cutar da su da sunan aure.
Wannan abinda ya faru din ya kara nesanta shi daga kan turbar son sake aure shima, dan sauran hope din da ya fara samu na yin aure bayan kammala digirin sa na uku ya bi ruwa. A lokacin ya cika shekaru talatin da biyar a duniya, sabida kyawun surar sa na
yan Gembu da kamewar sa Allah kadai ya san iyakar matan da ke haukar ya aure su a can jami
ar Jos, inda yake aikin koyarwa.
Lamarin Jaru ya taba Malam Gidado sosai ya kasa barin ran sa, tun daga lokacin kuma sai ya fara shiga ittikafi, yana nemawa
yan sa tsari daga sharrin mutane.
Ya fara fama da ciwon suga kadan kadan da hawan jini wanda a karshe ya kwantar da shi. Mamman ya dauke shi ya tafi da shi Jos don ya ga kwararrun likitoci, sun sha jelen asibiti kafin a samu saukin abin.
Ina da shekaru uku Yaya Omar yana da shekaru goma Allah ya yi wa Baffa na malam Gidado Gembu rasuwa a cikin sujjadar sallahr asubahi.
******
asuwar dan uwan sa Gidado ta kassara shi har fiye da rasuwar matar sa uwar
yar sa, Asshe. Na ci sunan mahaifiya ta ne wato Aishatu, Baban mu ke kira na SIYAMA kasancewar an haife ni ne a cikin watan azumin Ramadhana, Ummati kuwa Azumi take kira na. Yayin da a bakin Yaya na Omar nake
Boddo
. (Boddo na nufin kyakkyawa da harshen mu na Mambilla).
Kowa kenan da sunan da yake kirana da shi a gidan mu. Wani ba ya taba aron na wani.
Dr. Mamman Gembu a lokacin ya bar jami
ar Jos ya koma aiki da
Economic Communiy of West African States (ECOWAS), sai suka maida shi aiki a babbar hedquatar ECOWAS ta kasar Najeriya da ke Birnin Tarayyah. Still Abba ya na nan a gwauron shi. A ruwayar Ummati ta ce wai
aljana ce ta aure shi shiyasa ya ki aure, kuma da zaman sa a haka ai gara mata da ya auri jinsin jinnun
A Duk ranar da tasa Abba a gaba tana gaya masa hakan mun yi ta sheka dariya kenan ni da Ya Omar, har sai Abba ya yi kwafa ya fita ya bar mata gidan zai huta da sharrin Ummati.
Shi kuwa Uncle Adam (Young Abba) sunan da na ke kiran sa da shi kenan tun ina karama sabida dasawar mu, ya dade da gama karatun da yake yi a Algers, tun kafin ya dawo ya samu aiki duk ta sanadin Abba da U.S Diplomatic Mission.
Ya auri wata abokiyar karatun sa mai suna Nasara Alkali
yar asalin garin Katsina, tushen unguwar Alkali, wadda suka yi karatu tare amma ba'a fanni guda ba, ita Nasara aikin jarida ta nazarta.
Da yake sarkin raha ne autan na Ummati idan Ummati ta saka shi a gaba tana masa ciwon bakin ya rasa inda zai yi aure duk kyawun matan Manbila amma ya tsallake su ya je ya a
uro bakar bahaushiya sai ya yi maza ya daga mata hannu ya ce.
Allah sittiri bukui Ummati ba zan auri
yan Mambila ba tunda matan duniya basu kare ba, kada su mutu su bar ni da goyon 'ya'ya in kasa sake aure, ko in sake aure su saka min guba a abinci.
A duk sanda Ummati ta yi masa korafin ya ki auren gida abinda yake gaya mata kenan ya kashe bakin ta, ita kuma sai ta ce
a'ah Adamu, kayi maza ka tuba tam, to dai ba
a yi wa Allah wayo kuma mutum ba ya tsallake kaddarar sa!
Sai kuma ta tuno Gidado, sai ka ga ta sa habar zani ta rufe fuska ta yi ta shara kuka a gaban mu tana fadin.
Ya Ubangiji na binne mahaifin su, na binne babban su da hannuna, (tana yi tana daga tafin hannun ta), na bizne matayen su bakidaya, ina rokon ka Ya Allah, sauran biyun nan ka bar min su su binne ni da hannayen su ya Allah in samu masu yi min addu
a (Allah wadu ta mi meta irugo
bikkoi
am seni be irami). Wato (Allah ka sa kada in kara binne
ya na sai dai su su binne ni)
A yanzu haka shi Young Abba ( Baffa Adamu) da matar sa Anti Nasara a jihar Lagos suke zaune inda Diplomatic office na kasar Amurka ke tafiyar da ayyukan su tare da shi.
******
HERE COMES
WASILAH
(MY LIFESTYLE INFLUENCER).
asu iya magana kan ce
Rai dai
ba ya rabuwa da rabo sai dai idan ya kare
. Ko su ce "komai lokaci ne" musamman aure lokaci gare shi kuma kamar habo ya ke idan lokacin da aka kaddara ma dan adam yin sa ya zo. Abin mamaki a wannan zuwan da Abba ya yi Mambila ya zo ne da zancen da ya bai wa kowa mamaki, wato ya samu matar da zai aura a can Abuja, diyar shugaban wajen aikin su.
Ummati ta bantari goro ta tauna kafin ta kura masa ido da son gane yana ciki hayyacin sa? Ko kuwa wannan matar asiri ta yi masa? Don an ce abinda matan barikin suka fi kwarewa a kai kenan in sun ga mazan da suka yi musu. Bata ga komai a tare da shi ba sai wata irin nutsuwa, da murmushi mai kwantar da rai, wanda ya nuna bayan cikin hayyacin sa yana cikin tantagaryar soyayyah kuma.
Matan Gembu da na kabilar Mambila sun kare ne?
Cikin izgili da tauna goro Ummati ta tambaya.
Cikin lallashi da kwantar da murya Abba ya amsa mata da cewa.