← Book details Sakacin Waye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 28

Sashe 8

Sakacin Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Azumi, me na ji kin ce? A kul! Na kara jin wannan bahaguwar addu
a a bakin ki. Yau nake jin lalacewa wace irin addu
ar banza ce wannan?
Na kuwa cunno mata baki ina kunkunin cewa
ina ruwan ki da addu
a ta? Daga ranar sai nake addu
a ta a zuci kada wani ya kara ji ya yi min fatan rashin karbuwar ta.
Ko sati biyu Anty Wasila bata rufa ba a gidan mu kasancewar ta caring a kan lamarin kowa na gidan ta gano wacece real Siyama; irin rayuwar tabarar da nake yi a gaban Kaka ta ta babu shan rana babu hantara sannan babu aikin wahala, domin ko firar dankali ta bani in yi mata zan fara amma tana kaucewa zan aje mata abinta in zura in gudu sassan Ummati. Gashi bata zo da mai aiki ba ayyuka suna mata yawa don bata rabo da girke girke kai kace (food and nutrition) ta karanta.
Amma sam ko wankin cokali bana taya ta, ta lura ba ita kadai ba ko Ummatin ma bana tayawa kuma Ummatin bata damuwa, sannan bana son karatu ko kadan bana assignment bana homework iyakaci a dake ni in ban yi ba to jikina kam zuwa yanzu ya saba da dukan malaman makaranta har bana jin zafin sa, ya fi min sauki a kan wahalar karatu.
Yadda nake ta munanawa Anti Wasila zato sai na samu akasin haka a dan zaman da tayi tare damu, bilhaqqi take son Abba da duk wanda ya dangance shi. Kullum sai ta zo ta sharewa Ummati daki ta wanke mata hijabanta ta shanya da yake Ummatin bata barin ayyuka su tarar mata kullum cikin aiki take shiyasa babu ayyuka da yawa a dakin nata.
Da ta shiga daki na kuwa sai da ta toshe hanci, panties dina masu menses a jiki tun na wancan watan na cukuikuiye su na saka a wardrobe kana budewa wani hamami zai buge ka, babu shara babu mopping a dakin kaca-kaca da shi, ko
yar aikin gida bazata bar dakin ta haka ba, undies dina kamar tsummokara dukundukun dasu sai
yan dukununun uniform dina na boko da islamiyya duk sun ji jiki kasancewar bana goge su, littattafaina na makaranta kuwa da ta buda sai da ta kusa kuka. Shin ko wannan shine maraici na UWA-MAHAIFIYA A TARE DA DIYA MACEN DA TA BALAGA? Take neman uwar da zata ja ta a jiki ta nuna mata komai na tsaftar jikin 'ya'ya mataat puberty stage? Wasila ta tambayi kan ta cikin tausayin Siyama. Amma kuma bata cewa Ummati komai ba kan abubuwan data gani don ta lura da wani abu; ba
a fadar laifi na a gaban Ummati. Saidai daga wannan ranar Wasila ta dauki aniyar canza rayuwar diyar mijin ta Siyama.
Rannan da gangan ta saka ni girki wai kanta ciwo yake. Ta shige daki kamar mai ciwon gaske ni kuma kamar abin arziki na tafasa ruwa daganan kuma na rasa me zan yi? Don wallahi ko dafa kwai ya dahu daidai ban iya ba sai ka samu ruwa-ruwa a cikin sa wato bai dahu gabadaya ba.
Sai na ce tunda ta shige daki bari kawai in gudu iyakaci gobe ta ki kula ni, to sai me in ta ki kula nin? Na zo ficewa ashe-ashe ta kulle sassan da mukulli ta kuma zare mukullin ta tafi da shi dakin ta. Na rasa inda zan sa kaina don takaici na koma kicin na hau safah da marwah, a karshe nace bari kawai in mata wake da shinkafa ta ci da mai da yaji tunda shi ba sai an yi miya ba.
Na hada waken da shinkafar na zuba a tukunya na antaya ruwan zafi a kai. Suna tsotsewa na kashe na hau kwashewa a sabuwar warmer dana taka island din kicin din na daukoa cikin kwalin ta, ni da kaina daga ganin abincin a ido na san tsoro kawai na bashi wato bai dahu ba. To amma yafi ta zo ta ga ban yi komai ba ta dauke ni wata bi ta can, in yaso in bai mata ba sai ta kara dafawa da kanta.
Anti Wasila ta shigo tana hamma wai ta tashi daga baccin data samu, ta ce
Siyama na ji dadin kan nawa yanzu dana yi bacci kadan na sha paracetamol, zubo mana abincin nan muci a kan leda bana jin hawa tebir din nan ga shi yunwa nake ji sosai
Iyakacin takurawa Anti Wasila ta takura min yau na rasa dalili, buri na kawai ta bude kofa in fece wajen Kakata amma ta ki, na zubo abincin a faranti mai fadi sai cin magani nake yi tayi kamar bata ganni ba, don kuwa cewa ta yi
sako cokula biyu yau tare zamu ci
, na bi umarnin ta, bayan na antaya mai da maggi da uban yaji na kawo kan ledar data shimfida, ta hau juya abincin da cokali amma ta ki kaiwa bakin ta, tana jira ni in fara kai loma.
In kaga fuska ta a lokacin yadda ta yankwane kamar zan fashe da kuka don na gane Anti Wasila kamun kazar kuku tayi min yau, na dade ina guduwa in ta saka ni wani abu da ya shafi aikin gida ko na abinci. Ni kuma ba zan iya ce mata ban iya ba, na san a shekaru na goma sha biyar ba karamin abin kunya hakan zai haifar ba ko kuma ma ta raina ni.
Dana ga ba sarki sai Allah dole na kai abincin baki na, na kuwa runtse ido na ki hadiyewa. Tsahon mintuna biyar Anti na bin karatun Qur
ani a wayar ta tana jujjuya cokali a abinci, cikin ginshira tace.
Yau sai kin cinye abincin nan Siyama, don ki tabbatarwa kan ki irin sa zaki dinga baiwa mijin ki Umar nan da shekaru biyu ko uku
Ido na fal hawaye na furzo na baki na nace
Anti ki yiwa Allah da Annabi ki kyale ni haka
ta yi dariya ta ce
zan kyale ki ki fita in kin cinye, ko babu dadi ne?
Na fara hawaye na ce
wallahi Anti bai dahu ba, zai bata min ciki, ko taunuwa ba ya yi
shi mijin ki da zaki dinga baiwa wannan ba zai bata masa ciki ba?
Anti ai banda mijin tukunna ki bari sai nayi auren sai ki koya min
Anti ta ce
don tuwon gobe ake wanke tukunya ba sai an zo amfani da ita ba, zan kyale ki only in kin nuna min hammatar ki da cikin wandon ki don ban yarda bama kina yin shaving dasu wanke baki. Look at your teeth (kalli hakoran ki) yadda suka koma yellow kamar kin shekara baki basu maikilin ba
Jin abinda tace wai in nuna mata hammata ta da cikin wando na na soma tababar ko matar nan bata da hankali ne? Ko kuma shaye shaye take yi? Ban furta ba amma kwayar idanuna sun gaya mata abinda nake tunani a kanta. Ko a jikin ta sai ma dora kafa daya da tayi kan daya, tana jiran in cika umarnin ta ko in kwana nan a dakin ta.
Jin Anty Wasila ta yi rantsuwa sai na nuna mata hammata ta zata bude min kofa, na dinga kuka ina kankame jiki na.
Ummati ki zo ki cece ni, na shiga uku, kina ina ne za
a tube ni yau, Ummati!?
Anti na gintse dariyarta ta ce
tara kika shiga ba uku ba, sama tsami tsaka tsami matar Umar
sai na bar kiran Ummati don na tabbatar ta yi nisa bazata ji ni ba, na hau kiran Ya Umar shima, ta ce
ai gara ya zo don ya ganewa idon sa irin kazamar matar da Abban sa ke masa tanadi
Ba shiri na yi shiru. Har da toshe bakin. Na hadiye gunjin kuka na don nima ba zan so ko kusa Ya Umar ya ga kasan hammata ta ba.
Haka Anti ta tasa ni a gaba muka shiga toilet dinta ta aske ni tas da (shaving cream) mai santsi, ta ce kuma kaina ma askewa zata yi kwalkwal zata min idan har ban yarda ta wanke min shi da kanta da sheltox da kalkashi ba. Yau ni Siyama na ga ta kaina, har tara na shiga a wurin Anti Wasila hatta baki na sai da ta wanke min shi tas da maclean dinta mai karfi na Longrich sannan ta kyale ni. Na kuwa fice da gudu sai dakin Ummati ina nishi kamar wadda tayi gudun famfalaki.
******
a bararraje na gwaggwafe kafafu a kasa ina baiwa Ummati labarin yadda na shiga uku hannun Antin Abba yau, na ce
wato Ummati Anti Wasilan nan ba karamar muguwa bace ta bugawa a jarida, kina ganin ta wata sumui-sumui muguntar da ke kunshe cikin bakin ta ta fi bakin ta girma.
Ummati baki na yau har jini ya yi, sabida dirzar muguntar da ya sha a hannun ta
Sai na ji gyaran muryar ta tana tahowa ta ce
UMH! Sai kuma ta daga labule ta shigo kamar dama tana labe a kofar dakin, ta ce.
Chapter 8 · 0% Book details