← Book details Sakacin Waye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 28

Sashe 27

Sakacin Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

ababen debe kewa, ababen saka nishadi, hotunan sa kuma suka cika wayata fam. Wadanda nake sauke su daga shafukan sa na yanar gizo. Murmushin sa kadai mai kokarin narka zuciya ta ne, wanda ke tafiyar da numfashi na na wucin gadi. Na yarda ba abinda ya kai soyayya dadi a zuciya da ruhi. To ina ga inda take samun martani daga wannan masoyin?Gare ni dai, ni kadai nake ninkaya a koramar da zakin ta yafi na zuma, gardin ta yafi na madara. Koda Aunty Wasila ta aikowa da Young Abba sakamako na na WAEC da NECO babu wani abin a zo a gani a cikin su ban damu ba, a yanzu kam ko diyar Qaruna bana jin ta rufa bayana a kwanciyar hankali da samun contentment na rayuwa. I'm feeling myself on top of the world of happiness and excitedness. Tunda kullum idanuwa na na kallon abinda suke so, kunnuwa na na jin sautin mutumin da suka fi son ji a duniya bakidaya, wani abu wai shi karatu na rantse baya gabana idan ba yadda zan mallaki Hamzah ba. Uwar dakina Nasara Alkali, ta dade tana lura da sabuwar rayuwar dana fada, kamar bana cikin tamu duniyar, kamar a wata duniyar nake rayuwa nikadai, na zama addicted ga wayata ko bandaki zan shiga da wayar nake shiga, idan kuwa akan masai nake zaka sameta like ga kunnuwana ina sauraron Hamzah - Mawonmase. Duk abinda nake ciki ashe aunty Nasara na lura dani. Yau da Young Abba ya fita aiki sai ta shigo daki na cikin shiri, a daidai lokacin da Hamzah ya kammala shirin sa na safe wanda yayi akan janyewar yajin aikin jami'o'i na kasar Najeriya.
Chapter 27 · 0% Book details