Sashe 3
Sakacin Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
a jami ar Jos ya fito, ya tattara ya tafi Jos ya bar Asshe tana goyon Omar-Faruq a gaban mahaifiyar sa Ummati. Sai da Omar ya shekara bakwai cikin ikon Allah buwaya gagara misali rana daya (bayan ta riga ta fidda rai), sai gashi Allah ya dubi hakurin ta da zumuncin ta a kan maraya ya bata nata rabon, wato ta haife ni. Lokacin da na fara tasawa sai mutane ke cewa ai babu wanda nake kama da shi duk cikin iyayen mu, Ummati da ma dangin mu na wajen uwa dake Gashaka sai da Omar kadai. Dukkan mu kuma da iyayen mu mata muke kama don haka jama a da yawa da basu san tarihin mu ba sun dauka uwa daya uba daya muke, musamman yadda Omar yake taya Asshe raino na tun ina mitsitsiya ta ya ke goya ni, yaje makaranta da ni goye a bayan sa. Tun ana korar sa kan ya mayar da ni gida ya dawo, sai malamin ya ga ya tsaya a bakin tagar ajin su ya ki tafiya yana leke yana sauraron karatun daga bakin taga, dole malamin su yake jin tausayin sa ya kyale shi yake zuwa karatu da ni. Don ya lura kaunar da Ya Omar yake min tana da yawa. Wannan ya faru ne a sanda na fara wayo. Wani abun jimami da ya biyo bayan murnar haihuwa ta shine tun bayan haihuwar Asshe ke fama da matsalar zubar jini, an yi yawon neman magani iri-iri har babban asibitin jihar Taraba inda likitoci suka tabbatar da cewa magunguna masu karfi data yi ta sha na gargajiya don neman haihuwa su suka lalata mahaifar ta, Allah ne ya rubuta zan shaki iskar duniya shiyasa har ta iya ta haife ni. Aka saka ranar da za a yi mata aikin cire mahaifa don a samu zubar jinin ya tsaya ta huta ta samu lafiya gabadaya amma babu batun sake haihuwa. Da ranar ta zo aka yi komai lafiya aka gama lafiya, ana ta murna wahala ta kare, ashe kuwa da gaske babbar wahala ta kare domin kuwa Inna Asshe, bata farfado daga allurar anaesthesia ba. ****** MAMMAN Kina nufin Hassu da Asshe duka sun shigo rayuwar mu ne ni da Yaya Gidado halan don kawai su haifa mana marayun ya su bar mu da kananan marayu su koma? Me kike nufi da cewa ta zarce a cikin allura?? Kina nufin, nima ni kadai zan raini dan nan/'yar nan kamar yadda Yaya Gidado yake rainon Omar Faruk shi kadai??? To shin da wanne nonon kike nufin zan raine shi/raine ta? Ai gara Umar ya sha nonon uwa har na tsayin shekaru biyu ko ba komai ya san dumin jikin uwar sa, ki ji tausayin halittar Allah baiwar Allah ki fada min gaskiya cewa wasa ki ke .. k ice min mata ta Asshe barci take yi a cikin allurar yanzunnan allurar za ta sake ta ta tashi mu tafi gida ta shayar da Dan ta . Sai hawaye wasu na korar wasu suka biyo bayan maganganun da zaka tabbatar cikin fita hayyacin sa yake yin su. Abinda Baba na ya fadawa Nos din da ta gaya masa rasuwar mahaifiyata kenan kafin hawaye su cigaba da tsinke masa, ya kuma kasa karbar jaririn da take ta faman bashi kamar ya ce mata "ki musanya min shi da mata ta Asshe. Zata iya kara haifa min wani, amma ita bazan kara samun kamar ta ba!!!" Nos dai bata gane sambatun wannan mijin mai tsananin son matar sa me yake nufi ba, ta dai san zafin mutuwar matar sa ne ke bugun sa ya kuma fidda shi a hayyacin sa, sai hakuri take bashi. Tana tuna masa ayar Ubangiji da ta ce Kullu Nafsin Za ikatul Maut Ta kuma miko masa ni nannade cikin zanin atamfar mahaifiya ta tana fadin,