Sashe 11
Sakacin Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
TAFIYA MABUDIN ILMI
un ina karama nake jin Ummati na yawan fadin wannan zancen na hausawa, "tafiya mabudin ilmi" ban taba yarda ba sai yau da na fito daga alkarya ta ta ainahi wadda ban taba barin ta ba tun haihuwa ta, na ke keta garuruwa da jihohin Arewa maso gabashin Najeriya cikin lafiyayyar motar Abba (4-Matic) baka wul. Sanyin A/C ya addabe ni sai da na roki Ya Umar da ke tukin motar akan ya rage, Abba ne zaune a gefen sa yana karatun Al
ani ni da Anti muna kujerar baya. Anti na ramuwar barci ni kuwa idanuna tangaran ko son kiftawa bana yi kada a wuce wani garin ban tambayi Ya Umar sunan sa ba. Shikuma baya gajiya da gayamin har da karin bayanin karamar hukuma ce ko kuwa jiha. Da sunan gwamnan garin mai ci idan ya sani. Tafiya sosai ta kwana guda da yini guda kafin mu isa FCT Abuja. A hakan ma mun tsaya a Kano ne mun kwana a wani gidan saukar baki (Tahir Guest Palace) washegari da safe muka dauki hanya.
Tunda aka haife ni ban taba fita daga garin Gembu ba sai wannan karon, hana rantsuwa na je Gashaka tare da Ummati wajen dangin mahaifiyata ba sau daya ba ba sau biyu ba dana yi wayo, don haka yau da na rinka ratsa jihohin arewa bude ido nayi kawai na yi ta shan kallo ina mamakin wasu gine ginen wadanda ban san da irin su a Najeriya ba.
Da muka shigo Abuja kuwa manyan titunan ta masu fadi da gadojin sama da kasa su suka fi daukar hankali na domin cigaban dana tarar ya kai ya kawo. Sai yamma lis muka shiga wata kebantacciyar unguwa wai ita Jahi, inda anan gidan da Abba ya saya yake, gidan na mu ba wani babba bane kwatakwata (three bedrooms duplex) ne, dakuna uku kacal ke da gidan biyu a sama daya a kasa sai BQ inda anan Ya Umar zai zauna. Amma tsari da ilmin da aka zuba wajen tsara komai na gidan abin burgewa ne matuka. Ana kiran wadannan gidajen duplex, wadanda duk kusan iri daya ne cikin estate din, an kwaikwayo su ne daga gidajen kasar Sweden.
Dakin kasa Anti ta bar min, inda a can babban falon gidan yake, da main kitchen, ita da Abba suna sama, Ya Umar na daga waje shikadai a BQ sai maigadi a nasa dakin can a jikin gate din shigowa.
Kwana biyu kawai Anti ta bar ni na huta daga gajiyar mota daga ranar kuwa a gabanta nake wanka ina kuka ina komai ba ruwan ta, komai koya min take kamar ta samu katuwar jahila, tun daga alwallah har wankan tsarki, da wankan sabulu da yadda ake gyaran gashi, ta sayo min hand dryer ta koya min busar da gashi inna wanke, ta saya min shampoos ds conditioners samfurin Dr. Teal
s, komai na amfani na har man shafawa da bath foam dina samfurin (Dr. Teal
s) Anti ke zabar min, sati daya da zuwan mu ta kai ni H-MEDIX inda acan ta hada min set din su, daganan sai Grandsquare inda ta saya min undies farare sol sol da kayan barci kala biyar da dogayen riguna suma biyar biyar, Egyptian Jilbaabs kala-kala don zuwa islamiyya, maclean kuwa daga ni har ita dana Longrich muke amfani.
Zuwa sati biyu na fara da rage kin shiga kitchen don kuwa Anti bata bari na in yi zaman banza irin wanda na saba a falon Ummati ina kallon talbijin, idan har zata shiga to dole ta biyo ta daki na ta sako ni a gaba, tare muke shiga safe, rana da yamma mu yi girki sau uku a rana.
Aunty bata raga mini, ba ta sassauta min sai ta ga na yi komai daidai kamar yadda ta koya min shi a kicin. Haka da ta samu lokaci ta dauke ni muka je tayi min shopping kayayyaki na dinkawa kala kala atamfa, shadda, leshi da materials, ta bada a dinka min a gidan su bayan telan gidan su ya auna ni, sannan ta saya min kayan masarufi dana tsaftace jiki iri - iri, turaruka da deosprays masu dadin kamshi na Dolce&Gabbana, haka ta ke bata lokacin ta wajen nuna min yadda zan ke amfani da komai, yadda zan gyara fuskata, hatta shafa lipstick ita ta nuna min, kasancewar tana hutun aure bata zuwa aiki sai bayan wata daya.
Amma duk da haka ni kullum cikin jin haushin Aunty Wasila nake. Gani nake ta takura rayuwa ta ta canza ta iyakar canzawa, ta matsa mini.
"Me yasa ta damu da sai ta canza min tsarin rayuwa ta?"
Idan ina yi ma Ya Umar wannan korafin sai ya girgiza kai ya ce
nan gaba kadan zaki gane babu mai son ki a duniya bayan iyayen ki sai Antin ki, Wasila
. Nace
au kai baka so na?
Yace
ni ba na cikin lissafin su, soyayyar miji daban ta iyaye daban. Aunty wasila da Abba iyayen ki ne
Sai bayan ya fada yayi nadamar subutar bakin sa, yayi maza ya gyara da cewa
soyayyar Yaya daban take da ta kowa, kin ji? Ki daure ki daina korafi kan Antin ki, ki bata dukkan goyon baya da hadin kan ki. Bata nufin ki da komai sai tarin alkhairi.
Ina tabbatar miki duk kudin da ta ke kashe miki ba Abba ne yake bata ba, hasali ma bai san tana yi ba. Don Abban namu Economist ne ba zai salwantar da kudi masu yawa har haka a kan ki wai don ki zama 'yar birni ba.
Had you know how beautiful and radiant you have become now, da kin gode mata iyakar godewa. She is indeed your lifestyle influencer!
Murmushi nayi. Ban san takamaimai ma
anar kalmar da ya fada ta karshe a wancan lokacin ba, illa zuciya ta da ta fassara ta yadda ta ga dama, na san dai kawai Omar yana yabon kirkin Anti Wasila ne.
Da hutun Anti ya kare ta koma aiki sai na samu saukin ayyukan gida, ni kadai nake wuni a gidan, kuma sai naji gidan ya yi min fadi babu dadi kamar da, kewar ta ta dame ni. Kasancewar har zuwa lokacin admission dina bai fito ba daga
Regent College
inda Abba ya nema min.
Ya Umar kuwa yanata zirga zirgar registration din sa tsakanin gida da Gwagwalada inda zai fara level 1 a tsangayar da Abban mu yayi nasa karatun wato tattalin arzikin kasa (economics). Don Abba so yake a komai Umar ya gaje shi tunda dai bai da dan da ya fi Umar din, amma shi a ra
ayin sa karatun likita ya so ya yi, likitan zuciya, amma tunda Abba yace ga abinda yake so ya karanta ya karba da hannu bibbiyu. Ko dama can shi mutum ne mai muhimmanta ra
ayin wanin sa a kan nasa, a haka kowa ya shaide shi.
Kullum Anti ta fita aiki zaka same ni ne ina gyaran gidan mu ciki da bai din sa, bani kicin bani falo bani saman bene har sai naga ko
ina yayi kal-kal, tsaf-tsaf, yana daukar ido, sannan in dora mana abincin rana, zuwa yanzu kam ba laifi na iya girki daidai gwargwado na zamani amma banda na gargajiya wadanda Anti su tafi koya min.
Direban ofis din su Abba na zuwa daukar masa abinci karfe biyu daidai na rana kasancewar Abba tunda ya auri Wasila bai iya cin abinci a waje. Ya Umar in ya tafi Gwagwalada tun safe sai yamma yake dawowa, motar haya yake hawa don Abba motar shi daya ce tal Anti ma haka, ina ji rannan yana masa alkawarin idan ya fito da (first class) mota sai wadda ya zaba zai saya masa. Amma a yanzu ya fi so ya koyi rayuwar gwagwarmaya irin ta kowanne dalibin public university a Najeriya.
Ta hakan ne zai san muhimmancin wahalar neman ilmi. Ya iya tattalin abinda yake da shi. Sai a ka yi sa'a kusan duka halayen Abba irin na Umar ne, abin nufi anan Abba da Umar-Faruq ko kadan basu dauki rayuwar duniya da zafi ba, suna tafiyar da ita a saukake, a duk yadda ta riske su. Sun yarda jin dadi da daukaka basa zuwar ma mutum ta sauki a lokaci guda sai bayan ya sha gwagwarmaya a rayuwa.
A tsayin watanni uku kacal na zama wata kasaitattar
yar hutu, budurwa
yar kwalisa mai aji da hankali na kwatance, mai nutsuwa mai kuma kyawun surar da yake samun gyara da attention din uwa, sannan da gani babu tambaya ka ga
yar gatan uwar riko da Abban ta.
Rayuwa ta ta canza min baki daya positively, jiki na ma ya samu canji, ya nuna samun hutu da tsabta. Abu daya ne kawai har gobe bai canza a tare da ni ba wato (strong fulfulde accent) din Mambila bai bar baki na ya iya furta kalaman turanci dana hausa sosai ba.
Ni kaina na san ina daga cikin
ya masu sa
ar mahaifi a rayuwar su, wadanda basu taba neman wani abu daga mahaifi sun rasa ba. Wadanda maraicin uwa bai taba affecting walwalar su da jin dadin su ba, ko kuma don ban taba sanin ta bane?
Farkon zuwa na sabida yadda Anti ke faman takuramin da aiyuka bana samun lokacin kaina balle har in samu lokacin tuna mijin mafarki na ko yin mafarkin sa. Kusan kullum sai na kira Ummati a wayar Anti mun sha hira, don ni Abba ya ce ba zai mallaka min waya ba sai na gama sakandire amma ya baiwa Faruq bayan dawowar mu nan, kullum na kira Ummati sai na bata labarin duk abinda nake ciki kamar kawata aminiya, rannan Anti bata nan ta bar wayar a hannu na nake ce da Ummati.