Sashe 6
Sakacin Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Basu kare ba Ummatin Mambila, kuma har abada bazasu kare ba, wannan din ce dai kawai hankali na ya kwanta da ita. Ba ita ta ce tana so na ba ni na gan ta da kaina a gidan mahaifin ta, na yaba da hankalin ta, tarbiyyar ta da gidan da ta fito, na roki mahaifin ta cikin alfarma da ya bani ya kuma amince sabida kaunar da yake yi mun, ya ce in zo in turo magabata na
Ko ba komai bayanan da yayin abun a duba ne, don haka Ummati ta rasa abin cewa, can kuma ta ce.
Ka ba ni kwanaki uku in yi istikhara
Jiran kwanaki ukun a garin Mambilan da suka zamarwa Abba tamkar jiran shekaru uku, don hakika yana son Wasila.
Bayan kwana ukun kuwa Ummati ta ce da Abba ya je ya samu waliyyan su wato aminan mahaifin su marigayi Malam Dalhatu su je su nema masa auren. Bata ga komai a tare da yarinyar ba sai alkhairi mai tarin yawa tattare da ita. Ta tambaye shi ko
yan asalin ina ne? Ya ce
Katsinawan Dikko ne. Aiki ne kawai ya kai mahaifin ta Abuja kamar yadda ya kai kowannen mu
Ummati ta yi murmushi tana ta karantar farin cikin da yake ciki duk da yana kokarin dannewa ta ce,
kai da dan uwan ka duk Katsinan kuka gudu? Ina nan zaune kan shimfida ta zaku zo neman karin ta bibbiyu a Mambila, don matan mu basu da maraba da Hurul eenin aljannah
. Abba ya yi dariya sosai ya ce,
to babu laifi Ummati, bari sai mun karasa Aljannahr gaske, sai na kara da su
Kowa ya na ta murna Abba zai yi aure ban da ni, karewa ma, bakin ciki nake yi sosai, ni bana son matar duk da zata auri Abba gaskiya haka kawai ta raba mu da shi. Ranar da na yi kuskuren fadin wannan maganar Ya Omar sai da ya buge min baki da tafin hannun sa, Ummati kuwa ta ce
irin ki kam, kishi zakuyi, har dana balbal wanda bai dace ba. Allah ya shirya masu kishin iyayen su, matar sa ai uwar ki ce in da tunani, kada in kara jin wannan maganar a bakin ki Azumi, shima in ya ji baki so ko bai fasa ba zaki sanyaya masa gwuiwa.
Ke daban a wajen sa, matarsa ma daban, da wannan zaman da yayi shekara goma sha biyar cikin gwaurantaka ba gara masa auren ba koma wacece zai aura ai ta rufa masa asiri ta kuma taimake shi
Wannan Magana ko kadan bata sanya na ji ina farin ciki da auren Abba ba, damuwa sosai na dauka na sakawa raina a kai babu gaira babu dalili har da kin cin abinci wuni guda, har Ya Omar ya gane fushi nake yi da dukkan su, tunda babu wanda ya bi bayan ra
ayi na.
Na zo wucewa cikin gida daga islamiyya na gan shi zaune akan dakalin kofar gidan mu yana karatun jarida, wucewa nayi ba tare dana yi masa magana ba don har zuwa lokaci ina jin haushin buge min bakin da ya yi a kan matar Abba da bata kai ga zuwa bama. Omar ya bi ni da kallo ta kasan idanun sa har na wuce ciki ya ce,
Boddo am, kawomin buta a cikin gida zan yi alwallahr sallah, magriba ta yi
na zumbura baki na yi cikin gida ina cewa a raina zaka ga buta, tunda kana bayan auren Abba, kai ma idan ta zo raba mu zata yi don na fahimci ta fi ni farin jini yanzu a wurin ku, don ba abinda suke yi duk gidan yanzu sai shirye-shiryen tarbar matar Abba, an yi renovating gidan mu sosai ya koma na zamani, sabida a nan gidan mu zata fara zama na tsayin sati hudu. Na ji Ummati na fadin saura kwana uku daurin aure.
Ya Omar ya na can yana ta jiran buta, har aka kira sallah, dole ya shigo cikin gidan ya dauka da kan sa yana mamakin share shin da na yi, sanda ya shigo nima alwallah nake yi a gindin famfo ya ce.
"Boddo kin kyauta, ni kika share ko?" Kasa-kasa yadda Ummati bazata jiyo ni ba na ce "amaryar Abba ta dauko maka, tunda har zaka iya bugun baki na a kan ta" dariya yayi ya ce "to ni meye gami na da amaryar Abba? Ban san ta ba bata sanni ba, rashin kunya kika yi na hukunta ki, shin ma wai ke meye matsalar ki da auren Abba ne? Kada dai kina nufin kishin Baban ki kike yi?
Zaro ido na yi ina kallon Ya Omar, amma can a karkashin kasan idanun tabbacin hakan ke bayyana kansa baro-baro, wato tawa mahaifiyar na ke tayawa kishi wadda ke karkashin kasa har ta zama turbaya, a fili kuma nace.
Ba haka bane, zan gaya maka dalili na Ya Omar bayan sallahr isha".
Ana idar da sallahr isha kuwa Ya Omar ya shigo gidan kamar yadda ya saba, Ummati na lazumi har zuwa lokacin, ban taba ganin mutum mai yawan jan tazbaha irin Ummati ba, abincin daren sa na fara dakko masa, gudun kurna ne da miyar taushe Ummati ta yi mana, yana budewa ya yamutsa fuska ya ce "Ummati, kin san bana son wannan abun" ta harare shi ta cikin hasken kwan lantarki da ya haske fararen fuskokin mu bata ce masa komai ba don bata gama lazimin ta ba.
Ya mike tsaye yana karkade jikin sa yana fadin "da in ci wannan kulakulan naki ya sa ni bacin ciki gara na yi birki a teburin mai shayi an soya min lafcecen kwai da zazzafan shayi da ya ji madara creamler" ai jin haka yawu na ya tsinke na mike ina cewa "sai dai mu je tare baza ka ci kai kadai ba" wata harara ya sakar min ya ce "tebirin mai shayin zaki je? Kiyi zaman ki zan kullo miki" na ce,