← Book details Sakacin Waye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 28

Sashe 7

Sakacin Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

ni ba teburin mai shayi zan hau na zauna ba, raka ka kawai zan yi muna tafe muna hirar mu kan abinda ya dame ni, na gaya maka Ya Omar ina da damuwa".
Da wannan Ya Omar ya yarda muka tafi tare, don ya sanni wajen kafiya ko ya kara turzawa ba hakura zan yi ba. Ummati ko kula mu bata yi ba.
Sararin samaniya yayi haske da hasken farin wata, babu wadatar haske a layin, muna tafe gefen hanya ni da Ya Omar a cikin layin mu, na ke gaya masa damuwa ta a kan auren Abba ba kishi bane na ke yi, na san in kowa bai fahimce ni ba shi Omar zai fahimce ni, mun yi nisa na ce da shi cikin sanyin murya,
Ya Omar ka san yadda nake son Abba na, na kuma ji an ce matan birni irin wadannan da Abba ya dauko zai aura azabtar da 'ya'yan miji suke yi, su raba shi da mahaifiyar shi da 'yan uwan shi, su cinye halayen sa na kirki ya koma wani sabon mutum mai sababbin halaye marassa kyau.
Yau da a ce a nan Mambila Abba ya samu mata zai yi aure ba zan damu ba, kuma hankali na ba zai tashi ba".
Na karasa maganata cikin damuwa tsantsa. Ganin haka Omar ya dube ni ciki mamaki ya ce "what is your business with this? Kina nan Mambila hannun Ummati suna can Abujan su me zai hada ki da su? Wannan rashin adalci ne ki ce duka matan birni haka suke, kina ina ta kauyen ta nemi kashe Baba Gidado? Boddo ki bari ta zo ki ga irin kamun ludayin ta kafin ki yanke mata hukunci.
Zato zunubi ne koda ya kasance gaskiya Boddo na. Na hore ki da rashin daurawa kan ki matsalar wasu, abu ne da ba zai amfane ki ba".
Daidai lokacin da muka iso wajen Garba mai shayi, ya biya aka soya mana Kwan, ina can gefe harde da hannaye a kirji aka zuba mishi a leda muka kamo hanyar gida Ya Omar ya ce.
"Boddo abin kunya ne ace kina mace amma ko kwai baki iya soyawa ba, bana son wannan goyon jaki da kaya a kan da Ummati ke miki, don ke mace ce, uwa kuma matar aure, kika yi aure a gidan mijin da ke son abinci, na rantse wahala zaki sha a hnnun sa don ba zai jure ba".
Na tura baki na yi gaba na bar shi ina kunkunin cewa "Ya Omar wa ya gaya maka zan yi aure? Ai sai Mutumin Mafarki na ya zo. Kuma har yanzu bai zo ba tukunna.
Ai wato ni miji na duk duniya babu irin sa a halayya da dabi'a he
s simply special (na musamman ne) halin sa ba irin na sauran maza bane, ni na gaya maka bazai taba damuwa ba wai don ban iya girki ba, ni yake so ba girki na ba, ni kadai na san shi
A mafarki na kawai nake ganin sa
.!!!
Shi ba fari ba shi ba baki ba, gashinan dai Bakin dan Najeriya mai tsayi da cikar zati, dogo haka siriri, mai cikar gargasa da wadatar saje a zagayen fuskar shi, kullum sai na yi mafarkin sa Ya Omar ya na murmushin sa mai ratsa ni, yana gaya min cewa yana nan tafe, nan bada jimawa ba, na duba na hanga anan garin bakidaya babu shi babu mai kamar sa....".
Ledar kwai da biredin hannun Ya Omar ta subuce ta fadi kasa, a lokacin he was like (ko Boddo ta yi gamo ne?) Ya sunkuya nima na sunkuya at the same time don daukar ledar da ta fadi, sai kawai hannnu na ya sauka a kan nasa.
Ba zan taba mantawa da wannan glimpse din ba da ya faru cikin hasken farin wata. Hasken farin watan ya haska min cikin kwayan idanun Umar, sai na ga sun koma reddish-brown ba ainahin kalar su ta zahiri ba, kunshe da wani bakon al
amari da ya fi kama da kishi da ban taba gani cikin idanun sa ba, sakar min ledar yayi na dauka muka cigaba da tafiya bai tanka komai a kan shirmen da na fada ba.
Ni kuma da gaske nake har ga Allah kullum sai na yi mafarki mijin Boddo, exactly yadda na suffantawa Ya Omar shi. Tun bana rike kamannin sa har na zo na rike, a da can bana iya rike kamannin sa banda cewa baki ne dogo mai cikar gargasa a fuska kuma ba dan Mambillah ba.
Kwatakwata Ummati bata saka ni girki, ko tace in zo in gani in tana yi wai bata so in sha wahala, jikin nawa bashi da auki, don haka ni dinnan ko dafa indomie ban iya ba a shekaru na goma sha biyar a duniya, aji uku na karamar sakandire.
Ga kiwa, ga son jiki kamar
yar mussa, inda duk wadannn abubuwan guda biyu suka hadu a waje guda ga mace to fa za
a samu boyayyar kazanta a tare da ita, bana son aiki ko kankani don tun farko ba
a sabar min da shi ba.
Gashin kaina bai yi kama da na
yammata tsararraki na ba wadanda kullun cikin gyaran shi da yin ado da shi suke yana reto akan fararen fuskokin su, ni nawa kullum cunkushe ya ke cikin bakin dankwali babu wanki babu taza babu retouching, ga kwarkwata wadda na tabbata rashin kula irin nawa ne ta sabbaba zaman ta a kai na.
Ni da Ya Omar wata irin mu
amala ce mai kyau kuma mai tsafta a tsakanin mu, ta fi karfin ta Yaya da kanwa don in da akwai alaqar da take sama da ta Yaya da kanwa a karfi da muhimmanci to ni da Ya Omar ce. Bamu da sama da junan mu a komai. Kuma bama hada lamarin da ya shafi dayan mu da komai a muhimmanci.
Ya sanni kamar yadda ya san tafin hannun sa. Na san shi kamar yadda na san farcen hannu na. Omar mutum ne mai martaba iyaye da sanin darajar su, mai wani irin kawaici da alkunya, ma
abocin maida kai a kan duk abinda ya sa gaba tun a lokacin kuruciyar sa. Mai fifita ra
ayin wani sama da nasa. A fannnin karatu kuwa na rantse na sake rantsewa; ban taba katari da hazikin mutum a karatun boko dana addini irin Omar Faruq Gidado Gembu ba. Dalili na na fadin haka shine; Ya rubuce Al
qurani da hannun sa ya kai sau bakwai ya kuma haddace shi. Abba kan ce ko Alhuda-huda ba zai so hada gasar karatu da Omar ba.
Wadannan qualities din ne Abba ke hange har yake ikirari shan alwashin hada mu aure, a tunanin Abba babu namijin da ya dace da auren Siyamar sa sai Dan sa Omar, Omar din da ya raina da kan sa, yake kuma fatan aure tsakanin mu ya dawwamar da zumuncin sa da marigayin dan uwan sa a bayan ran sa, ya kara yawan zuri
ar Ummati a igiya guda su zamo tamkar tsintsiya guda. Har ila yau, yake kuma fatan Ubangiji ya cika masa wannan burin nasa da ran sa da lafiyar sa.
Abba kan ce
a shaidar dan yau, amma ni na shaidi Da na Omar, shikadai zai rike min Boddo da irin rikon da nake so ta samu a gidan aure
Amma kuma ni Siyaman, ina girma ne tare da mafarkai na da burika na (fantasies) wadanda daga ni sai Allah muka san su. Wato tunda ni fara ce farin da babu surki to miji baki (black) zan aura wannan na cikin mafarki na, har na kan hango
yan da zamu haifa masu duhun kala da kyakkyawar suffa, idan ni suka dauko ko baban su wato mijin mafarki na zasu zama ne tamkar ruwa biyu.
Ba ruwa na da abinda Abba ke hange, ba ruwa na da mafarkan Abba sai nawa mafarkan, ba ruwana da burin Abba, duk da ya dade yana fada yana maimaitawa a gaban mu ni da Omar din. Iyakaci Omar ya sunkuyar da kai amma bai taba tankawa a kan hakan ba, ni kuwa a duk lokacin da ya fada na kan zumbura baki ne in ce.
Abba! A ina ka taba ganin Yaya da kanwa sun yi aure?
Abba sai ya ce
daga kan ku za
a fara!
. Kuma daga wannan amsar da ya ke bani, ba na daukan zancen da nisa.
A haka muke girma hankali na kara shigar mu, amma mafarki na da buri na na auren bakin mutumin cikin mafarki na bai taba canzawa ba, ta kai ta kawo har ina imagining din sa a idanu na na zahiri, I can feel his eyes all over me, da lamarin yayi gaba sai na fara jin muryar sa all over my earsyana kiran sunana in a unique way. A cikin mafarkin na kan gan shi tarr, ganin ido na, in ji shi sarai jin kunne na, in kuma rike kamannin sa amma da zarar na farka sai a shafe komai daga kwakwalwa ta.
A wannan shekarar Ya Omar ya kammala karatun sakandire, da sakamakon su ya fito Abba ya ce ya cike jami
ar Abuja a JAMB form din sa don burin Abba kullum shine ya bude ido ya gan shi tare da Omar. Duk da ya san ba karamin yaki zai yi da Ummati ba kafin ta yarda Ni ko Omar wani ya bar gaban ta. Amma dole ne Omar ya shiga jami
******
n daura auren Abba da Anti Wasila a wata ranar Lahadi. Abba ya yi furnishing bangarensa na nan gidan mu ya tashi a matsayin apartment na zamani, ba can kadai ba har bangaren Ummati ya gyare tas babu maraba da nasa bangaren, ya min daki na mai kyau ya zuba min duk abin bukata. Duk garin Gembu yanzu babu gida kamar namu har wani lakabi akewa gidan wai gidan gilashi, sakamakon duk ta inda ka bi a gidan mu gilashin tagogin da na kofofin ke daukar idanun ka.
Anti Wasila ta tare a gidan da tarin dukiya wadda ta kara kawata sassan nata kwarai. Ta tabbata
yar Ogan su Abba domin kuwa ni dai ban taba ganin duniya irin ta dakin Anti Wasila ba, ko kuwa don bani da exposure? Amma da na tuna Abba ya ce diyar shugaban sa ce sai ban yi mamaki ba.
Anti Wasila na yawan gayamin cewa wai kira ta da suffata ta matan manya ne, wannan ya na kumbura kaina ya kara min burin auren mijin mafarki na, domin kuwa babban mutum ne ba yaro ba. Maganar da Abba na ke yi ba tun yau ba wai zaman Ya Umar nake ban taba daukan ta da wani muhimmanci ba.
Can nake hango miji na bakin dan Najeriya, dan sardidi da shi na burgewa, ban taba addu
ar Allah ya bani miji nagari ba, nidai kullum addu
a ta Allah ya bani mijin cikin mafarki na, ya sada fuskokin mu nan ba da jimawa ba, domin jiki na ya gama bani yana raye cikin duniya, amma ba a Mambilah ba; shi ba fari bane yafi zama a rukunin bakake, dogo siriri mai yawan gargasa a fuska, mai wani kasaitaccen aji na musamman.
Ranar da Ummati ta ji na furta wannan addu
ar bayan na idar da sallah taji nace Allah ya bayyana min mijin mafarki na haka, sai ta yi tsam, ta nutsu, tana sauraro na har na gama. Cikin nutsuwa Ummati ta ce.
Chapter 7 · 0% Book details