Sashe 16
Sakacin Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
nagari masu fitar da jinnu daga jikin bil adama suka saka ni a gaba aka banka min turare sannan suka fara karatu. Baka jin komai sai tari na lokaci - lokaci sabida rashin dadin turaren nasu, amma har suka gama Suratul Baqarah ras nake, sai ma kafa danake canzawa position don karatun yana min dadi, na dade ban yi tilawar surah Baqarah ba sabida sakaci irin nawa. Ni na san bani da wani aljani amma na isa in yi jayayya? A je a hakan. Watarana da kan su zasu yarda da ni cewa, na san abinda basu sani ba. A karshe malaman suka gayawa Abba gaskiya babu shaidani a tare da ni, watakila dai na saka wani saurayi a raina ne shiyasa nake yawan mafarkin sa yake kuma yi min gizo a kunnuwa na. Abba ya kawo sadaqa ya sallame su. Bai ce komai ba ya bi matattakala zuwa saman bene Anti Wasila ta rufa masa baya. Tun kafin su karasa daki ya ce "kin ga abin da nake gaya miki ko. Salon iskanci ne kawai irin nata don ta gujewa auren dan uwanta, Omar bai ki Siyama sai ita ce zata ki shi har haka? Na rantse da Allah sai na aura mata Omar sai dai ta mutu da kiyayyar hakan..." Anti bata taba ganin fushin Abba a fili irin na yau ba. Tace "to tunda ta ce yana raye a duniya ka nemi ta kawo shi, in ta kasa sai kayi abinda ya dace" yace "babu wanda zan saurara akan Siyama, ni addini ya baiwa damar zaba mata miji kuma na zabar mata, ya rage nata tayi min biyayya ko ta bada min kasa a ido babu wani shirmen ta da zan kuma saurara". A daren ranar Anti ta sameni a daki dauke da indomie da dafaffen kwai guda biyu, ina kwance ne kawai ina fiskantar ceiling tunanin duniya ya addabe ni, kunnuwa na ba abinda suke son sake ji sai muryar sa da sunan sa, takamaimai bansan daga wane gidan radiyo bane don tsakiyar zancen na tsinta babu farkon sa. "Inaga zaki iya cin wannan tunda baida nauyi" ta fada tana zama a gefe na. "Bana jin yunwa Anti""nikuma bazamu yi magana ta fahimta ba sai kin ci abinci, tashi zaune a baki ma zan baki" ta debo abincin ta nufo bakina da shi, na kauda kai, sai ta hau yimin wakar da take yi wa Shukra-Nadiya idan ta ishe ta da rigima. "Hayya bina yaa Nadiaa, kam sa'atan laki na'imah!"(Tashi haka ya ta Nadiya, awannin ki nawa kina barci?) Dariya ta bani sosai don wato nufin ta yau ni da Nadia yar watanni shidda bamu da maraba a wurin ta. Dole na karbi lomar abincin daga hannun ta, loma uku nayi nace don Allah ta kyale ni kada in yi amai. Da Anti ta fahimci na dan ware sai tace dani. "I want to see him!" Da alamar tambaya na dubeta ina juya hannu wato ina son sanin wa take son gani din? "I want to see our Dream Guy, in yi magana da shi ta gemu da gemu. Idan na gamsu dashi zanyi kokari in gamsar da Abba duk da na san ba karamin aiki bane mai sauki na daukowa kaina ba. Amma a matsayi na na 'yar uwa mace na san illar auren dole don haka zan taimaka miki, ki fada masa gobe ya zo ina son ganin sa a office dina" Sai na rasa abinda zan ce mata, anya idan na kara maimaita mata cewa nima ban san shi a zahiri ba, ban taba ganin sa ba, ban kuma san a ina yake ba zata manna min hauka ba? Tunda dai ta ce in kawo shi zata taimaka min to abinda zan yi yanzu shine in nemo shi, a duk inda yake, in kawo mata shi ta rarrasar min Abba ya karbe shi. Siyama kina da tabbacin shi yana son ki zai kuma iya auren ki? Haka ake soyayyar baka san mutum ba baka san halin sa ba baka san komai akan shi ba? Bai ce yana son ka ba sai ka je ka ce masa zo ka aure ni? Idan ma kin same shin kenan. Ko kuwa shi yace miki yadda kike mafarkin sa shima haka yake naki mafarkin? Lamarin is complicated amma ba'a san maci tuwo ba sai miya ta kare. I vowed to find him, a duka gidajen radiyon jiha dana tarayya. Kuma zan ke ta kasa kunne a duka gidajen radiyo da talbijin ma tunda na fahimci mijin mafarkin nawa Professional Radio Presenter ne. Ba zai min wuyar riska ba. Da Aunty ta ga nayi nisa a duniyar tunani sai ta mike tana fadin "sai ya zo. Ki fada masa daga karfe tara na safe zuwa sha biyu na rana zai iya gani na a HumanitarianAffairs". Daga haka ta fita, tana kara cewa "kinsan dai WAEC da NECO ne a gaban ki, ki ajiye komai ki fuskance su in kina son gina future din ki yadda ya kamata, idan zaki bari soyayya ta zama priority din ki a rayuwa kin kade har ganyen ki". Nisawa na yi bayan fitar Anty ina cewa ni kam ai har fadowa kasa warwas na riga na yi daga kan bishiyar karewar kadewar ganye indai a kan sa ne. A yadda nake jin karfin soyayyyar sa a raina zan iya bashi rayuwata, zan iya batawa da kowa in dai har zan tsira da shi. In na ce kowa ina nufin KOWA! ******* unty ta fito daga matattakalar bene inda dakin barcin ta yake zuwa daki na rike da 'yan mukullan motar ta "Siyama na fita, zani Wuse Market kayan cefanen mu sun kare, da dai-dai kike da na nemi rakiyar ki, to duk kin bi kin susuta kan ki akan da namiji, kin susuta min Abban ki babu gaira babu sabar na kasa gane kan sa. Ga nan Nadia ki kula da ita kafin na dawo". Ta fada tana miko min yar autar mu Nadia, babu kiwa ba komai yarinyar ta taho zuwa gare ni tana bangale baki, ta bani jakar jegonta mai dauke da abincin ta na frisco cream da kayan canjawa da su pampers din ta. "Sai kin dawo Anti, in kin ga radio please ki sayo min, latestone". "Radio kuma? Yaushe kika koyi sauraron radio naga dai da bata dame ki ba?" "Ina neman abinda zai ke debe min kewa ne ya hana ni tunanin auren dolen da ake son yi min". Aunty ta gyada kai kamar kadangaruwa ta sa kai ta fita tana mamaki. Ita bata ga aibun Omar ba, yaro saurayi matashi jazur da shi kamar sai ka wanke hannu kafin ka taba, ga tsafta ga addini, a irin shakuwa ta da shi bata taba zaton haka zata faru ba in aka fara maganar auren mu. Duk da na dade ina cewa ai Yaya na ne. Zata so kwarai ta ga wannan dream man din na Siyama, ta ga shin me ya taka har haka da ya narkar da zuciyar Boddo-Siyamah a murya da mafarki kadai? Ta san dai ba fin Omar kyau yayi ba yaro kamar Balaraben kasar Kuwait. Kuruciya ce kawai take damun Siyama ta ke neman kai ta ta baro, to wanda ya ki bin maganar mahaifin sa ai kuwa ya kai kan sa ya baro. Anti da ta tashi dawowa ta sawomin Radio mai quality kirar LG wadda babu inda bata kamowa gida da waje. Na yi mata godiya mai yawa sosai. Na ji kamar ma na hadu da shi na gama. Tamkar ta cikin radiyon nan zai bullo ya cimmani, ya wanke tsatsar kaunar sa da soyayyar sa da ke zuciyata. Tun daga ranar na yi mata saitin kamo tasoshin ko ina, na dukufa sauraren tasoshin radio daban - daban na gida Najeriya, da ban kara jin muryar dana ke nema ba sai na karkata ga sauraren International Media masu magana da Harshen Hausa, nice kullum BBC ke har ma da VOA dana fi karfafa zaton a can naji shi, kuma ita ce major din Abba, da wuya ka ji yana sauraron wata tasha ba VOA ba, amma abun kamar delusion na samu a waccan ranar. Don kuwa ban kara jin waccan muryar ba ko mai kamar ta, ko sunan da ya ambaci kan sa da shi wanda na yi ta kokarin in tuna na kasa, sai a mafarki na kuma. Ni dai na tabbata na ji ta real a Radiyon Abba, saidai ban samu naji ko daga wace tasha bane, in na yi kamar in tambayeshi "Abba kwanaki wace tashar rediyo ka kunna ranar dana fadi dinnan ake maganar hantsi? Sai kuma in kwabi kaina da cewa zasu manna min hauka, zasu maida ni Psychiatry da zama, Abba likitan ilmi ne wadanda duk wani kankanin mental abnormality ba wuya zasu dangana shi da asibiti. Tunda an ce mai nema yana tare da samu, to zan ci gaba da nema da saurare har Allah yasa in kara jin sunan sa da muryar sa, ko da bazan gan shi a zahiri ba. An jarrabce ni da babbar jarrabawa mai girma a kan sa, wani iftila'i ne ya same ni wanda ban taba jin mai irin sa ba, na san ba zan fadi wannan jarrabawar a banza ba, yana can yana jira na ko ba dade ko bajima shima. To amma shin Siyama Abba (Dr. Mamman Gembu)", ya cancanci ya saka kara ki tsallaka a kan wani mutumin da baki da tabbacin a duniya yake? Ya cancanci butulcin da kike shirin yi masa na bada masa kasa a ido akan tsohon burin sa? Amsa ce mai nauyi da bana son baiwa kaina amsar ta. Shi kan sa Ya Faruq wani jigo ne a rayuwata da baya bukatar sai an tuna mini girman matsayin sa a gareni. Amma a fannin aure zuciyata bata zabi kasancewar sa abokin rayuwata ba. Sai kuma aka yi rashin sa'a ni mai sakarwa zuciya linzamin kanta ce. Idan a baya ina tababar wanzuwar sa da kasancewar sa dan Adam, to daga ranar da na ji muryar nan tasa a Radiyon Abba, ya fadi sunan sa da nasabar sa na tabbata Dream Husband dina is a Human Being... he s somewhere far away from me, but he's in existence a tashi duniyar wadda