← Book details Sakacin Waye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 28

Sashe 20

Sakacin Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

baki kadai da zan dora ki a kai (counselling) don kada ya zamo miki lahani ga kwakwalwa". "Gashi kuma Dr. Bana bukatar cire MAFARKAN nan nawa a raina sabida ina jin dadin su, na fi so in cigaba da rayuwa cikin mafarkai na, sun fi min komai dadi domin suna debe min kewar jiran sa. Na tabbata ko ba dade ko bajima jiki na na bani zai zo ne, mafarkan da kake son raba ni da su suna taya ni jiran sa, ba ni kadai nake wannan wahalar ba Likita, ka yarda da ni ba koshin wahala nake ba kamar yadda kuke zato. I believe that our hearts are jointly connected internally". Dr. Amir yayi murmushi ya mike yana hada allura, ya gama fahimtar duk abinda yake son fahimta, (she believed her fantasies and infatuations) na shekaru masu yawa raba ta da su farat daya zai yi wuya, har sai in ta samu actualizing din su. Ya gama hadawa ya dawo yace "bani hannun ki Siyama zan miki allurar da zata sa ki samu isashshen barci". Ai kuwa tunda muka shiga mota nake ta barci, Allah ya so ni gobe da jibi duka babu paper. Lallai barci Rahma ne kuma ni'ima ga dan adam, kuma yin sa da ban yi ba kwana biyu ya taimaka wajen birkita ni da ta'azzara infatuation dina. ****** bba ya dubi Anti da ke ta kokarin shirya masa abinci "ina 'yar taki ne? Tun jiya ban gan ta ba""likita ya mata allura tana barci" bata da lafiya ne" ya tambaya yana yamutsa fuska. Anti tace "lafiyar ta kalau stress ne na jarrabawa kawai shine nasa aka mata allurar barci don ta huta sosai". Abba yace "but an fi son barci natural, yin allura don kawai ayi barci?""Likitan da yayi mata ya san abinda yake yi, wajen specialist (psychiatrist) na kaita, ko ba komai yanzu hankali na ya kwanta tunda na tabbatar Siyama bata da tabin hankali kuma bata da aljanin dare as well. Imagination ne data dade da sakawa a ranta yake zamar mata mafarki. "Sai tsabagen iya shege kuma ba!" Inji Abba cikin takaici. "Ni kuma nafi kowa iya shegantaka dani take zancen. Ko lefe bazan mata ba. Wai Umar ne Siyama bata so? Humm, duniya mai abin mamaki. Zuciya mugun nama mai kawace - kawacen banza. Allah ka shirya min Siyama, ka fidda rabon shaidan daga zuciyar ta". Anti ta amsa da "Amin, amma Abba don Allah likita ya roki a daga auren kada ayi a yanzu, a kara bata lokaci zai yi counselling din ta ta manta da wancan din" "Aikin banza aikin wofi, kada Allah yasa ta manta shi koma waye. Ta dauke shi su tafi gidan mijin ta tare. Bani da burin Siyama tayi zurfin ilmi a hannu na, gidan miji zan kaita a wannan watan da zamu shiga. Duk wani nauyi da Allah ya dora min nata na sauke, a yanzu aure kawai ya rage, kuma zan tabbatar a hannu nagari na damkata, ba ruwa na da shirmen ta. In ya so tayi tayi gunduwa-gunduwa da Umar din ta kawo mini, karewar rashin so kenan dai ko?" Anti kasa magana ta yi, don tsakanin uban da 'yar bata san wa ya fi wani taurin kai ba. Ba mamaki in ya kasance gadowa Siyaman tayi. Kwana uku ina bacci sai dai Anti ta tada ni ta bani fresh milk in sha in koma, dama kuma cikin al'ada nake, wani zubin sai tazo da kanta ta kaini toilet ta taimakamin na canza Pad sabida nauyin barcin da ke kaina. Ranar da barcin ya sake ni na koma na karasa jarrabawoyi na. Wanda babu laifi na dan amsa wasu yanzu domin na samu nutsuwa sosai. ***** FAREWELL FROM REGENT COLLEGE yau mun kammala Regent College Abuja, kowa ka gani cikin farin ciki marar misaltuwa yake sai hotuna ake dauka da 'yan uwa da iyaye da kawaye. Anti ce da su Nadia suka zo dauka na bayan mun yi sallama da Azima Ko'oje da sauran wadanda muke mutunci dasu, da alkawarin zan je gidan su Azima idan na huta, kai tsaye muka kama hanyar gida, amma sai Anti tace Dr. Amir yace mu biya ta wajen sa ya kara gani na. Ban ce komai ba, ko babu komai shine wanda ya wanke ni daga hauka a idanun ta. "Aisha Siyama an gama jarabawa lafiya ko, ina fatan akwai improvement?" "Alhmdulillah Dr., na dan tabuka ana karshe-karshen" "To wane course kike so zaki yi yanzu a jami "Babana ba zai barni ba" "Sai aure kenan" Na hadiyi miyau da kyar. Ji kake mukut. "Kin kara yin mafarkin sa?" Girgiza masa kai na yi alamar a'ah, "I only enjoyed my sleep" Masha Allahu Aisha, kin karbi maganar Baban ki da muhimmanci yanzu ko? Imean ta auren dan uwan ki?" Shiru nayi ban ce masa komai ba. Shi da kan sa sai y ace. "Prefer not to say?" Na gyada masa kai da sauri, yace to ya yawan tunanin har yanzu yana nan?" Na ce a hankali "bana tunanin komai tunda na gama barcin nan, ni ina zargin ba allurar barci kayi min ba gaskiya, damuwar tayi nesa da zuciya ta sosai. Bana jin bacin bacin rai sam ko wata damuwa, sai an tada min maganar auren Ya Omar". Dr. Ya maida hankalin sa ga Aunty yace "Alhamdulillah, she has responded fully to the treatment made. Shawara ta karshe itace ku hakura da yi mata auren nan, if not, abinda ake gudu shi zai faru da Siyama wato, zata tabu". Aunty Wasila tayi zugum da ita, tace "Dr. Matsalar ba daga gare ni bane, ba kuma daga Umar bane, wallahi yafi kowa damuwa da farin cikin 'yar uwar sa, Baban su ne matsalar, ba zai taba yarda da wannan shawarar ba, iknowhim kamar tafin hannu na. In yace YES to da gaske yana nufin YES din, babu gudu babu ja da baya, baya waiwayen abinda zai je ya zo". ******* una isowa gida Abba na dawowa, duk muka yi gare shi muna masa oyoyo, ya dube ni sai ya ga na rame ga idanu na sun zurma yace "jinya kika yi ne halan? Girgiza kai nayi ban ce komai ba. Anti ce ta ce na gaya maka ai, tayi jinyar baccin kwana uku", "to Allah ya kara lafiya, ya batun jarrabawa kuma sai yaushe za a gama?""An gama yau". Ta fada da fargabar abinda zai biyo baya. Daidai sanda muka shiga cikin gidan duk muka zazzauna a leather seats na falon kasa. Abba ya bude brief case dinsa ya fiddo (flight tickets) guda biyu ya mikowa Anti. "Ga nan, amshi, flighttickets din ku ne na tafiya Lagos gidan Adamu gobe, zaku hadu ke da matar Adamu ku yi sayayyar duk abinda ya dace na gidan Omar da Siyama, ku kuma hada mata lefe irin wanda duk take so. Da na ce bazan yi mata lefen ba amma Ummati ta ki. Rana ita yau da an sakko masallaci daurin auren su insha Allahu a Mambilah". Ya kawodaya daga cikin credit cards din sa na bankin GT ya bata "abinda ke cikin nan nan ina ganin zai ishe ku sayayyar komai, ayi komai na hankali da kula bana son almubazzaranci". Hannu bibbiyu Anti tasa ta karba tana fadin. "A madadin Siyama Allah ya saka da alkhairi. Ni kuwa sai nayi kasa da kaina. Da daddare na bi Anti dakin ta na sameta tana canzawa Nadia Diaper, fuskata ba walwala nace "Anti nikam ba sai na biki Lagos dinnan ba, kuje kawai dik abinda kuka zabo zai min dai dai". Hawaye suka balle mini. Anti tace "sabida bakya farin ciki ko sabida baki godewa kokarin Baban ki ba ko??" "Anti....!" "Siyama ki shirya kayan ki zamu tashi Lagos gobe da safe insha Allahu, zamuyi kwanaki uku na san zasu ishe mu mu gama abinda ya kai mu. Kwana daya lefe, kwana daya furniture da kayan kitchen da labulaye. Nasara ta san ko'ina a Lagos da inda za'a samu komai mai kyau, zata raka mu". Juyawa nayi kawai na fita ba tareda na kara tankawa ba, don na san duk abinda zan fada din tirjiya ce kuma ta nuna min bazata karbi kowanne uzuri na ba. Na tashi da zazzafan zazzabi a safiyar washegari, zazzabi mai zafi sosai harda jijjiga, da kartar hakora, wanda yasa dole Anti ta barni a gida ta tafi sayayyar kayan aure a Lagos don bata isa keta umarnin Abba ba, ni kuma na shiga jinyar kaina da kaina don Abba ma ba ya gari daga ni sai Maryam Jamila. Ita take taimakamin da miko min duk abinda nake so ina daga kwance, ta bani paracetamol na sha naji dan dama-dam wajen azahar na dafa mana noodles muka ci nida ita. ******** asara da Wasila ba inda basu shiga sun fita ba a kasuwannin garin Lagos suka hada lefe mai tsari, sannan kayan sakawa a gidan amarya. Kwanan Anti uku suka dawo. Ashe har da Ya Omar suka dawo gidan. Bai nemeni ba sai ana daurin aure saura kwana biyar muka hadu a kitchen yana shan ruwa daga firji, ni nasan na rame sosai amma dana dubi Ya Omar sai naga ya fi ni ramewa, ga kasumba ya bari a fuskarsa wadda a baya bashi da ita. Ya kara zama cikakken namji. A zuwan sa Lagos ma Young Abba ya yi masa tayin aiki da ofishin su, yace shi a'a a ofishin su Abba zai yi aiki sabida Abba ya kusa retire. Kaina a kasa na shiga kitchen din nayi kamar ban gan shi ba, har zai fita sai ya dakata yace. "Boddo ko gaisuwa babu?" Muryar sa kamar ta wanda ke fama da mura, na kasa kallon cikin idon sa don alkawarin da yayi min bai cika shi ba, ya ce zai lallashi Abba kada a yimin auren dole amma yayi hakan? Shirin angwancewa yake yi. Da ya ga ba zan gaishe shin ba kamar yadda na saba sai yace "kada ki damu fa Boddo ni ba bakon zafi bane, it's a promise bayan auren mu ba zan zo inda kike ba, I mean... I mean ba zamu hada shimfida ba don na fahimci damuwar ki kenan. Zan yi hakuri zan jure har sai ranar da kika karbe ni as a husband don radin kan
Chapter 20 · 0% Book details