← Book details Sakacin Waye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 28

Sashe 15

Sakacin Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

In da halacci da amana ba za ki ki dan uwan ki Umar ba!" Ko "in da alkawari Abban ki bai cancanci wannan rashin biyayyar ba? Dayan biyu, haka Anti take nufi ko me?. To ni na ce ina kin Ya Umar? Ai ina jin bayan wadda ta kawo ni duniya sai Abba sai shi a wadanda nake kauna, sai Ummati sannan kowa ma ya biyo baya. Ba zasu taba yarda da hujjoji na ba. Ko sun gane din ba zasu basu muhimmancin da ni na basu ba. Ba kowa ya san banbancin kauna ta 'yan uwantaka da kauna ta soyayyar aure ba. A sani na Namiji zai iya auren wadda baya so, ya zauna da ita for the satisfaction of his sexual desire kadai, mace kuwa ba zata iya auren wanda bata da sha'awa ta aure ko kankani a tare da shi ba, and that's exactly my point. Aure da Omar bazan iya ba gaskiya, ko duk duniya zata taru a kaina because i've no desire for him. A gareniSoyayya daban, kaunar yan uwantaka daban. Omar can never be my choice of a husband, ban taba yaudarar Abba ba duk sanda yayi zancen nan ai gaskiya nake fada cewa Yaya na ne, bazan auri biologicalbrother na ba don babu banbanci kona haihuwa a tsakani na da Omar. Ban taba dai gaya masu ina da wanda zuciya ta ta afu gare shi ba sai jiya dana yi subutar baki. Sabida bani da tabbacin mutum ne ko aljan. Allah kadai ya san nufin Sa na sako shi cikin mafarkai na har na saba da shi har haka, na ke jin duk duniya bani da miji sai shi, wanda na tabbata ko bajima ko ba dade mafarkan nan zasu zama gaskiya... Mutumin nan baki, dogo siriri, mai tarin gargasa a fuska da giran ido, mai murya irin ta Asians mai sassarfar magana don junan mu aka halicce mu.... kuma yana gab da bayyana kan sa gare ni komai daren dadewa. ****** VOA - HAUSA hirin su na safiyar yau Lahadi, wanda ya kasance (live-program) ne daga mita 0900 UTC (VOA-Muryar Amurka, Hausa). Shi Abba ya kunna a falon kasa ya kure sautin, yayi filo da hannayen sa bisa doguwar kujera yana sauraron labaran duniya daga bakin tauraruwar sa Grace Alheri Abdu. Tun bakwai na safe yake sauraren VOA har zuwa karfe tara lokacin da aka gama, kuma lokacin karya kumallon su yayi shi da iyalin sa. Grace Alheri Abdu na gama nata shirin, akayi taken VOA mai dadi, har Abba zai kashe rediyon sa shirin "HANTSI LEKA GID AN KOWA" ya rufawa sallamar Grace baya, wato ya maye gurbin nata shirin. "Hantsi Leka Gidan Kowa" Sabon shiri ne daga gidan rediyon VOA wanda ya ta'allaqa kacokam ga zaqulo fitattun mutane na Afrika da suka shahara a fannin su wajen baiwa kasashen Afrika gudunmuwa a kafatanin fannonin rayuwar su ta bangarori daban-daban da suka hada da kiwon lafiya, tattalin arziki, ilmi, rubuce-rubuce (literature), tarihi, wasanni, siyasa ko zamantakewa. "A yau shirin mu na "hantsi leka gidan kowa" yana tafe ne tare da tsohon marubucin Najeriya Farfesa (Noble Laureate) Wole Soyinka, wato Shakespearn Najeriya, wanda muka fassara wa masu saurare zuwa harshen Hausa (live) daga gidan rediyon VOA-Amurka Hausa a safiyar yau Lahadi, Ashirin ga watan Aprilu, tare da ni HAMZAH....ALMUSTAPHA....MAWONMASE........!!! (Ya fadi sunan nasa dalla-dalla yana sama yana kasa da sautin sa kamar cikin rhyme). Tare da cewa; Ayi saurare lafiya......". Iyaka abinda ni Aisha-Siyama na ji kenan a safiyar yau, safiya mai dumbin tarihi, safiyar da ta juya ta kuma wulwula rayuwata bakidaya. Muryar ta fito ne kai tsaye daga radiyon Abba ina kokarin fitowa daga daki na don halartar tebirin karin kumallo. A karshe ya yi wa masu sauraren sa bankwana da cewa daga wannan lokacin, daga wannan hirar da zai yi da Soyinka, za a jima ba a ji shi ba don zai tafi karo kwas na wasu watanni kafin ya dawo. Nan take jiki na ya karbi wani irin quickreaction na extremeshock, kafin zuciya ta tayi tsalle ta fado kasa daga cikin kirji na ta karbi wani irin coolness duka a lokaci guda. Tamkar na narke a inda nake tsaye. Numfashi na yayi sama yana dambarwa a tsakanin kirji da hanci da kuma baki na. Tamkar mai fama da ciwon asthma sakamakon yadda shaqar numfashi ya koma cikin hunhu na ya gagare ni. Domin muryar da na gama ji ce a daren jiya a mafarki na nake jin ta yanzu a rediyon Abba, muryar mutumin da ya haifar min da zazzabi da wankan janaba na babu gaira babu dalili a safiyar yau. Ko ko ince; muryar da na girma na kuma rayu sama da shekaru bakwai ina jin ta cikin kunnuwa na, a cikin yanayin barci (mafarki) da yanayi na ido biyu (imagination) a wasu lokutan. Ta yaddda ta riga ta samu kyakkyawan matsuguni a kwanya ta; a koina na ji ta zan gane ta. Na sako kafa ta a falon kenan zan wuce diningroom don na san duk irin ciwon da nake fama da shi ban isa in ki fita cin abinci ba musamman da yake yau tare da Daddy ne a karshen mako, yana gida don haka tare muke cin three square meal, amma sai na dan dakata ina saurare, iya abinda na ji kenan a kan shirin amma na gama tantance muryar DREAM HUSBAND dina ce. Kawai kuma ba zato ba tsammani na Abba ya kashe rediyon sa domin Wasila ta zo ta tsaya a kan sa tana faman gaya masa "Breakfast is ready!". Su duka suka juya a tare jin Yiiipp! An fadi a bakin entrance na shigowa falon, Siyama ce dake shigowa ta zame ta fadi kasa, gabadaya suka yi kaina a guje suka daga ni suna faman kiran sunana amma ina! Sun nemi bakin 'eye balls' dake cikin idanun kowannne dan adam sun rasa a tare da nawa idon. Wasila na fadin Baban Siyama maza dauko mukullin mota" shi kuma yana fadin "ki nutsu, mu fara bata taimakon gaggawa tukunna, kawo min ruwa mai sanyi" kafin ya rufe bakin sa Anti ta fita da gudu neman ruwa Abba kuma ya hau karanta min addu'a yana tofawa, Maryam Jamila ta na gefe tana kuka tana cewa "Anty Siyama!" Abba na shafa min ruwan da mintuna biyu na yi ajiyar zuciya mai nauyi, kamin in lumshe idanuna bakin kwayar cikin su ya dawo. Hawaye ya gangaromin ta gefen ido, na soma sambatu ".... Abba na gaya maka dama yana raye, mutum ne ba aljani bane. Allah ne ke nufin mu da wani al'amari mai girma da ya shallake tunanin mu". Abba a kidime ya ce "Waye?" Na ce "Dream Husband dina, na rantse maka da Allah Abba yau na ji maganar shi a zahiri ba'a mafarki ba...... saura ganin sa ya rage min...." nayi - nayi in tuno sunan dana ji ya ambaci kan sa da shi kuma na kasa, tamkar anyi formatting memory dina mai alhakin tuna abubuwa, ko kuma don ban taba jin suna irin sa bane?. Abba sabida takaicin dana ba shi sai ya sakar wa anti Wasila ni yayi tafiyar sa dining ya zauna yayi jugum, sai kuma ya hada shayi amma ya kasa sha. Tsaki yayi can ya tashi ya dau mukullin mota ya bar gidan ya manta jallabiyya ce a jikin sa sai gajeren boxer daga kasan ta. Shi kansa bai san ina zai je ba". Anti Wasila ta ciccibe ni ta kai ni dakin ta, ta koma ta hado shayi mai kauri ta kawo min, a baki ta bani duk da zafin sa haka na bude baki na sha sosai don jiya ban ci abincin dare ba na kwanta. Saida Anti ta tabbatar na samu nutsuwa, barin da jiki na ke ta yi na yunwa da shock ya ragu, sai ta sanya tafukanta cikin nawa ta matsa a hankali. Tace "Yau dai sai an gaya min wanene wannan Lucky din da ke neman sheka min 'ya barzahu, ya hada ta da fushin mahaifin ta babu gaira babu dalili". Wani matsiyacin kuka ya zo min, na ce "Aunty Wasila kin san ba zan miki karya ba ko? Ba zan iya boye miki komai ba ko? To wallahi duk duniya shikadai nake so, Allah ya riga ya nuna min shi tun kafin ya bayyana min shi" cikin mamaki Anti tace "a ina ya nuna miki shi din?""A cikin mafarkai na Anti, rana dai dai ne bana kwana in tashi ban ganshi cikin barci na ba, har ta kai ta kawo zuwa yanzu na haddace kamannin sa da sautin muryar sa". Idanun Anty was like irin "Siyama ta yi gamo, aljani ya aure ta". Abinda na gani a cikin idanun Anti tsabaragen tsoro ne zallah. Ta ce "kwanta ki huta, in Abba ya dawo zan masa bayani abin ba na fushi bane Siyama kina bukatar taimako". Taimakon da ban gane wane iri take nufi ba. Da Abba ya dawo daga zagayen da yaje yayi a mota don neman nutsuwar yanke hukunci akan lamarin 'yar sa Siyama, sai da tayi kokari ya sha tea da chips kadan, sai ta karkace ta soma lallashi. "Baban Siyama fushi da Siyama ba naka bane, na fahimci gamo tayi". Abba ya dakata yana kallon matar sa Wasila da kankance ido da sakakken baki, ta ce "kwarai gamo ne, ina kyautata zaton namijin dare (jinnul aashiq) ya aure ta yana zuwa mata cikin mafarki, yau kuma ta ganshi maybe a cikin bangon falo ido da ido". Jikin Abba yayi sanyi ya ce "kin tabbata ba salon iskancin ta bane?" Anty ta yi rantsuwa akan abunda take zargi ta ce kuma idan aka samo malamai na gaske da suka iya rukiyyah zasu iya raba ni da shi, (a distant cousin of hers) ta yi fama da (similar problem) kuma da iyayen suka dage da neman magani an rabu lafiya yanzu har ta yi aure. Dole Abba ya yarda da Wasila amma wani bangare na zuciyar sa yana tababar yiwuwar hakan. A tsari da kafin da yasa aka yiwa gidan nan nashi kafin su tare wani shaidanin aljani bai isa ya shigo ba har ya samu matsugunni a jikin iyalin sa. Shima Gidado ne ya bashi wannan laqanin kafin rasuwar sa. Amma don kore shakku haka ya dauko malamai
Chapter 15 · 0% Book details