← Book details Sakacin Waye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 28

Sashe 25

Sakacin Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta yi rayuwar ta yadda take son ta?" Young Abba sai jera "subhanallah" yake yi ba kakkautawa, yace "Boddo why? Kin san hukuncin suicide kuwa a wajen Ubangiji? Me yayi zafi a kan dan uwan ki?" Cikin kuka nace "Young Abba ba haka bane inada wanda nake so ne, sun kasa fahimta ta""ko kina da wanda kike so you shouldn't attempt this, sabida da kin mutu me zaki ce wa Ubangiji? Nima bana bayan a yi miki auren da bakya so, kuma bazan bari ba, amma maza-maza kiyi istigfari ga wannnan dingimmemen laifin da kika aikata". Nasara ta rungumo ni a jikin ta ganin yadda Young Abba ya bude min wuta sosai, ita sai take Magana cikin lallashi tana cewa "ina miki kallon mai hankali Boddon Omar, na san soyayya, i can relate with you amma ni kam kin ganni ko sigari bazan sha don na illata kaina akan namiji ba, ba zan kuma taba zabar sa akan rayuwa ta mai daraja ba balle iyayen da bani da kamar su. Maza kiyi istigfari". A fili na soma jero "ASTAGHFIRULLAH" suna taya ni. Kalmar da tunda na sha fiya fiya ban ambata ba. Young Abba ya miko min hannun sa na kama a hankali ya mikar da ni ya ja ni gefen sa ya zaunar dani a kwibin sa, yace, "Boddo do you want to stay with us? We don't have a child yet, and you know ina son ki tun kina karama ko?. An yi min relocation na wurin aiki na daga US Diplomatic Mission na garin Lagos zuwa babban reshen mu na birnin Washington D.C. Boddo zaki bi mu? Kin ga sai ki shiga makaranta ki zauna da Antin ki Nasara ki manta da wata soyayya kin ji Boddo? You are still a baby, baki kai ga cimma komai a rayuwa ba, tunda baki cika shekaru ashirin ba har yanzu, wannan rayuwar da kika jefa kan ki ta kuncin soyayya ba taki bace, ba kuma inda zata kai ki, kuma ko wanene ya sace min zuciyar diya ranar da Allah ya nuna min shi zan saka kafar wando daya da shi tunda ya hanata karatu sai soyayya". Kunya sosai naji na rufe fuska da tafuka na yace "Ummati dama sallama muka zo miki nida Nasara, to ga karin 'ya mun samu. Ku kwantar da hankalin ku Omar ba yaro bane ba zai kai kansa mahallaka ba. Ina tabbatar muku da cewa zai kula da kan sa a duk inda ya tafi. Kuma hukuncin da yayi ya burge ni, ya zabi farin cikin 'yar uwar sa akan nasa, wannan ya nuna shi mai kaunar ta ne kuma insha Allahu a hankali Boddo zata so Omar zata aure shi don radin kanta. Yanzu ki amince mana Ummati mu tafi tare da ita?". Ummati ta kyabe baki ta ce "ni ina ruwana abinda ba'a kaina take zaune ba, ku dai je can Abujar ku fara gaya musu in mahaifinta ya barta ni meye nawa a ciki? Na riga na sallama Boddo" "kiyi hakuri Ummati ki daina fadin haka a kanta". Inji Young Abba. Ummati tace "zan yafe mata kadai ranar dana ga Faruku a gabana ya dawo gida yayi aure tunda ba ita ce autar mata ba". Haka kawai naji hankali na ya nutsu da bin Young Abba da maidakin sa Nasara zuwa US. Ina fatan hakan ya zamo min hanyar samun kwanciyar hankali na har abada. Yasa ya zamo silar da zan manta da "Dream Man" dina nima in hutawa rai na. Ya sa kafin in dawo gida Ya Omar ya riga ni dawowa. Ya kuma sa tafiyata ta zama hanyar manta komai da ya faru dani a baya. (Bansan cewa wata kaddarar kana gudun ta tana bin ka bane. Ban san cewa mun riga mun saka kafar wando guda ni da kaddara ta ba. Kuma ita din tamkar Zanen Dutse take dan adam bai isa ya kankare ta ko ya tsallake ta ba). Tun a daren na hada komai nawa tsaf, da taimakon Aunty Nasara. Ummati sai cewa take "Allah raka taki gona". Ko don rashin mutuncin da ummati ke mini naji ina son tafiyar, idan da hali kada in sake dawo mata gida. Amma kuma bazan iya barin Najeriya ba tareda na je na nemi gafarar Abban mu ba koda kuwa zai koro ni ne da sanda. Aunty Nasara na zuge trolley dina taga ina sharar hawaye, tace "Dotty, ki kwantar da hankalin ki kin ji, na miki alkawarin zama makwafin Wasila insha Allahu. Sannan zan tsaya tsayin daka wajen ganin rayuwar ki ta tafi daidai kamar ta kowacce mace 'yar musulmai jikar musulmai, da yardar Allah kuma zaki samu auren duk wanda kike so Young Abba ba zai taba bari a tauye ki ba". Nace "ba damuwata ba kenan Aunty Nasara, ina tunanin yadda zan cigaba da rayuwa alhalin Abba na ya koreni, yana cikin fushi dani, son samu mu fara biyawa ku tayani in bashi hakuri, ko bai bar ni na zauna ba ya yafe mini, ya yarda cewa tafiyar Ya Omar haka Allah ya tsara don babu kaddarar aure a tsakanin mu". Nasara tace "zan yi ma Adam magana mu fara tsayawa a Abuja". Muka kama hanya a washegari muka bar Gembu. Tafiya dasu Young Abba tafiya ce mai dadi kwarai, kana tare dasu kana daukar ilmin zamantakewar aure nagari, akwai kyakkyawar fahimta tsakanin sa da maidakinsa, ana tafe suna ta raha suna tsokanar juna cikin soyayya, wannan abu ya kara dasa min son aure na soyayya ya kuma sa nayi ta raya abubuwa da dama a raina inda ace nice tare da "Mr Radio" kamar yadda Ya Umar ya kira shi. A haka muka isa Kano muka kwana washegari muka karasa FCT. ****** ABUJA aga Abba har Anty Wasila suna gida yau, kasancewar karshen mako ne, Maryam Jamila ce ta fara ganin fitowata daga mota ta kuwa kwaso da gudu tana ihun murna ta rungume ni. A haka muka karasa cikin main parlour kamar zata cinye ni don murna. Abba da Anty suka amsa sallamar Young Abba nidai sai rabewa nake a jikin bango. Anti ta taso ta bude min hannuwa ina hawaye na shige cikin jikin ta. Ina kallon Abba na satar kallon mu da harara amma ya maida hankalin sa kan dan uwan sa Adamu da ya kwana biyu bai gani ba yana "lale da mutan Legas". Nasara ta gaishe shi nima na zamo daga jikin Anti Wasila na durkusa a gabansa ina hawaye na ce. "Abba na ina wuni!" Sai kuka. 8 Kuka nake mai motsa zuciyar duk mai sauraro balle zuciyar Uba mahaifi. Ina kallon yadda fuskar Abba ke takunewa cikin yanayi na rashin jin dadi ga kunyar kanin sa da maidakin sa don baya so maganar ta hada mu a gaban su, bai san cewa Ummati ta riga ta gaya musu komai ba. Young Abba yace "Dr. Siyama tayi kuskure kuma ta karbi kuskuren ta ba zata sake ba, ka yafe mata". Abba yace "Adamu ka fita a maganar Siyama, bata da kirki bata da lissafi, tunda har Omar ya bar ni a dalilin ta itama bazata zauna min a gida ba, ta tafi Mambilan tayi ta zama idan zaman kauye dadi ne. Gatan dana nuna mata shi ya bata kwarin guiwar bijiremin da bijirewa umarni na, to na janye gatan ta je tayi rayuwar ta yadda take so". Young Abba yace "ni zan dauki Siyama ta zauna a hannu na ta cigaba da karatu, idan ta samu miji zan mata aure, auren dole bashi da ma'ana Yaya, na san kana son Omar kana kuma yi musu hange mai kyau ne amma dukkannin su suna da 'yancin su rayu ba ta hanyar auren juna ba, suna da damar su zabi abokin rayuwa wanda zuciyar su tafi kwantawa da shi". Abba ya ce "saidai ta bi ka din kuwa, ban haifi dan da saidai ni in bi shi ba, ba dai shi ya bi ni ba. Kullum na ganta a gaba na bacin rai zata dasa min na kore min Omar". Na gurfana gaban Abba na kama kafar sa nace "Abba na yi alkawarin nemo maka Omar, ko bajima ko ba dade, nayi alkawarin dawo dashi gida, ni dai fata na ka yafe min Abba, ka daina fushin nan da ni don Allah ". Na kama shi na kankame kamar bazan sake shi ba sai ya furta ya yafe min din. Abba ya ce afuwata daya ce gare ki Siyama in ga Umar ya dawo gida, na janye kalamai na kamar yadda yake so". Abba ya soma matsar kwallah wanda hakan ya kara gigita ni na rushe da kuka mai tsanani. Nace "alkawari ne zan dawo maka da Dan ka, amma ban yi alkawarin zan aure shi ba". Cikin mamakin taurin kaina Anti Wasila ta daka min tsawa tace "Boddo ke da kike neman afuwa kuma kike tada bara bana, Abba yana jin ciwo in kika ce bazaki auri Umar bane gara ki bar ra'ayin ki a ran ki tunda ya ce ya janye kudurin sa". Kowa ya hau yimin fada har Young Abba, yace tunda na karbi maganar kuma nace ban amince da auren dole ga kowannen ku ba, kada ki kara maimaita wannan maganar. Afuwar sa muke nema ba tada tsohon zance ba". Abba yace "in dai bazata zauna min a gida ba taje ko ina zata je bani da matsala da wannan" ".....wanda ke nufin Abba baka yafe min ba? Na tuba Abba na bi Allah na bi ka. Ka furta yafiya a gare ni don in ga albarka a rayuwa ta". Abba yace "zan yafe miki only ranar dana ga Da na Omar a cikin gidannan, na aura msa matar data fi ki" aka kada aka raya Abba ya ki canza maganar sa. Amma ya amince in bi su Young Abba duk ma inda zasu je ba matsalar sa bace. A hakan cikin rashin kwarin jiki kowa ya kwana a gidan. Don hukuncin Abba bai yi mana dadi ba, bai yi wa kowa dadi ba, bana so ina tafiya a duniya babu afuwar sa a jiki na, don haka na dauki aniyar nemo Ya Omar ko ta halin kaka. Washegari jirgin Azman muka bi zuwa jihar Ikko. Cikin sati biyu Young Abba ya gama yi min duk
Chapter 25 · 0% Book details