← Book details Sakacin Waye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 28

Sashe 1

Sakacin Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Root Entry
WordDocument
0Table
Data
Normal
Default Paragraph Font
Normal Table
No List
0Footer Char_856b5d4c-05f5-447e-8e16-25884833b8d3
footer
Hyperlink
0Header Char_dd3fe2a6-9631-40ae-b4bc-125678cd588f
header
SAKACIN WAYE?
Sumayyah Abdulkadir
[email protected]

HYPERLINK "mailto:[email protected]"
[email protected]
`GORON SABUWAR SHEKARA` (2023).
TARE DA NI;
SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI.
1 GA WATAN JUNAIRU, 2023.
2023
HAKKIN MALLAKAR LITTAFIN DA DUK ABINDA YA KUNSA NA MARUBUCIYAR SHI NE SUMAYYAH ABDULKADIR (TAKORI). A GUJI KARANTAWA A YOUTUBE KO SARRAFA SHI TA KOWACCE HANYA BA TARE DA RUBUTACCEN IZNI NA BA.

GEMBU
(GARIN MU DA BABU KAMAR SA A SANYI A FADIN KASAR NAJERIYA)!!!
arin Gembu, kamar yadda na samu cikakken labari daga bakin Ummati, da sauran bincike na na ilmi a kan tarihin yankin namu, kasancewa ta wata irin mutum mai son sanin Tarihi da bin ussin salsalar ilmin abu, yankin Gembu wani babban birni ne ko kuwa in ce alkarya da ke a yankin Duwatsun
MAMBILLA
a jihar Taraba a Najeriya, shine babbar Hedkwatar karamar hukumar Sardauna wato (Sardauna Local Government) da aka fi sani da
Tsohuwar Mambilla
a jihar Taraba.
Sunan Sardauna Local Government ya samo asali tun daga zuwan Alhaji (Sir) Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto yankin mu na Gembu a shekara ta (1956).
Mutanen Mambila ko Mambilla suna zaune ne a Tudun Mambila (Mambilla Plateau). Garin yana kusa da Boda wato iyakar da ta raba kasar Najeriya da kasar Cameroon. A wasu lokutan masana tsaunin Mambila kan kira tudun na Mambila da
Heaven on Earth
wato (Aljannah a duniya), wannan ya samo asali da kasancewar garin Gembu gari mafi kyawun yanayi na sanyi mai ban mamaki a arewa maso gabashin Najeriya.
Masana ilmin labarin kasa (Geographers) sun tabbatar da cewa a kasar Najeriya bakidaya babu gari mai irin kyawun yanayi na sanyin Gembu. Sannan gari ne mai cike da albarkatun kasa wanda da gwamnati zata maida hankali wajen bunkasa shi da ta samu arzikin kudin shiga mai yawan gaske a kan sa, sakamakon yadda garin ya ja hankalin masu yawon bude ido na ciki da na waje. A Gembu akwai wasu manyan Dams guda biyu wato
Barup Dam
da
Tunga Dam
masu tsohon tarihi tun tana ancient town of (Bommi), garin Mambila na zaune a matsakaitan duwatsu tsayin kusan mita 1,348 (4,423 ft) sama da matakin Teku, yana daga cikin manyan biranen Najeriya.
Gembu na da habakar kiwon shanu, tumaki, awakai da Buffalo. Tuntsayen gida kuwa Allah ya yi albarkar su a Gembu, wanda ya sanyawa garin albarkar nama da abinci mai lafiya, duk da cewa sun fi kiwon dabbobin su fiye da cin su.
Abincin da ya fi yawa a Gembu shine kayan marmari (fruits) wanda ke taimakawa kwarai wajen kasancewar mutanen garin cikin koshin lafiya, yawan shan
Piya
ya maida fatar mutanen Mambila wata irin danyar fata mai taushi da sulbi kamar larabawa.
Gembu gari ne da Allah ya halicci kyawawan mata, in na ce kyau, to ina nufin tsurar kyau na halitta fiye da na sauran duka kabilun fulanin Najeriya. Akasarin
yan Gembu (musulman cikin mu) zaka gan mu dogaye haka sirara masu cikar zati da kamala, sirantakar dake kara mana kyau, matan Gembu masu asalin dogon hanci da doguwar fuska ne, masu sassanyan kyau da babu fulanin da suka mallaki irin sa a fadin kasar Najeriya.
Wadannan din dana ambata ba dukkan su ne
yan kabilar Manbila ba, mutanen Gembu sun fito ne daga rukunin kabilu daban - daban wadanda suka hada da; Mambilla, Kaka, Kambu da Panso.
Yaren garin Gembu shine fulatanci ziryan din sa, Hausa bata da tasiri sosai. Yaran da aka haifa a Gembu ko
zo in ka she ka
da hausa basu sani ba sai wadanda suke fita ko suke ta
ammali da bakin haure.
Matan Gembu wasu irin kyawawan mata ne na bugawa a jarida kamar sun hada iri da larabawa, sabida tsananin sanyin garin basa ta
ammali da fanka ko A/C. Mutanen da aka haifa a Gembu basu taba ganin fanka ko A/C a zahiri ba sai a talbijin ko a littafi.
Sabida karfin harshen fulatancin su hatta a Choci da fulatanci a ke sermon kasancewar kiristocin su kusan sun fi musulmai yawa.
A wancan lokacin dana ke magana a kai mazan Gembu na fita cikin jihar Taraba don yin karatun boko amma matan Gembu basa karatun boko sai daidaiku, wadanda a wannan karnin da ake ciki ne ma suka dan fara karatun boko, shi yassa ake fadin cewa matan Gembu
yan kabilar Mambila basu da wayewar kai kamar na sauran fulanin Jalingo. Amma kuma suna bada karfin su a kan neman ilmin muhammadiyya wanda yasa bazaka taba kiran su jahilai ba.
Sana
ar matan Gembu sakar kayan sanyi da zannuwan gado na rufuwa masu kauri, wadanda suke sakawa don amfanin kan su sabida yanayin garin su. Sai ko kiwo da noma.
Sunan yaren garin ne
Mambila
sunan garin kuma shine
Gembu
. Kamar yadda na fada a sama Gembu shine birnin Mambilla wanda ke karkashin karamar hukumar Sardauna.
Gabadayan garin da sauran kauyukan da ke makwabtaka da shi a kan Duwatsu suke tsugunne, wato (Mambilla Plateau).
Chapter 1 · 0% Book details