Sashe 9
Rantsatstsen Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yace "Kwarai kuwa har sai mun ga tashin motar ku" Ai tuni hawayen farin ciki suka zubo mata, tasa bayan hannu ta goge su tana faɗin, "Nagode babana" Kukan ya isa haka, kin san kinada ciwon ido" yana magana yana share mata sauran hawayen.
Bayan isarsu Katsina haka suka ƙara shiga wani ɗan sahu ya kaisu KTSTA inda zasu hau motar Abuja, duk da ƙaramar mota zasu hau ba KSTA din ba, amma a can anfi samun motoci masu aminci. Da sukaje din ma can cikin sa’a mutum biyu ake jira, ai fa suna zuwa aka ce su shiga.
Ita kam Maryamah ganin da gaske fa daga nan zasu rabu da babanta yasa ta fara hawaye, yana rarrashinta da ƙyar ya samu ya lallasheta ta haƙura, nasihar ma da yaso ƙara yi mata kasawa yayi saboda gaba ɗaya ta karya mishi zuciya. Haka suka riƙe juna da Aisha suna rizgar kuka sai da ƙyar aka ɓanɓare su a jikin juna.
Gaba ɗaya hankalin mutane ya dawo kansu.
Shi kanshi Malam sale zuciyar sa ta karye yana tunanin rabuwar uba da ɗiyar shi ga kuma aminan juna, sanin kanshine juriya kawai Malam jafaru yakeyi…...
FULANI
08082101373
https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr?mode=gi_t

✨🦋 RANTSATSTSEN RABO 🦋 ✨
BY RABIA'TU KABIRU ACHADU (FULANI)
YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION YOTA
SADAUKARWA GARE KI HALIMA HASHEEM (MIEMIEN HABIBI)❤️& AHMAD JAMIL AHMAD (HABIBI)♥️
FULANI
08082101373
✨🦋 RANTSATSTSEN RABO 🦋 ✨
PAGE 🔟
Haka suka rabu cikin tsananin kewar juna, amma ba yanda zasuyi sai fatan hakan ya zamar masu alkhairi gaba daya.
Cikin mota ma Maryamah tun tana kuka har bacci ya dauke ta, haka sukayita tafiya cikin aminci, bata farka ba har sai da suka shiga garin Abuja lokacin da suka isa la'asar sakaliya.
Da zuwan su suka samu driver na jiransu, kasancewar koda suka zo Suleja, Malam Jafaru sunyi waya da Hajiya shine ta turo wanda zai dauke su. Kalle-kalle Maryamah ta dingayi, duk da bata da duhun kai irin na kauyawa, amma dai ita ko cikin Katsina zata iya ƙirga sau nawa taje.
Haka suka shiga lafiyayyar motan da akazo daukan su, da ita a ranta tana jinjina kyau da tsaruwar garin, amma zuciyanta duk tana wurin babanta, gaba ɗaya tunaninta nacan tare dashi, rayuwa kenan ganin yau itace ta tafi wani gari ta bar babanta, wasu siraran hawayene suka ziraro mata.
Haka suka nufi ɗaya daga cikin manyan unguwannin garin na Abuja, unguwar Asokoro, wadda tana ɗaya daga cikin manyan unguwannin masu kuɗin Abuja wadda sai wanda yaci ya tada kai zaka gani a irin waɗannan unguwanin, Yakubu Gowon Crescent taga an rubuta sunan street ɗin da suka shiga inda yake kusa da Aso Villa.
Unguwa ce mai matuƙar tsaro, kasancewar tana kusa da villa sannan komai nasu a tsare yake, suna da takatsantsan wurin shige da fice na unguwar, gaban wani tamfatsetsen gida suka tsaya, horn sukayi aka wangale masu get motar ta silala cikin farfajiyar gidan wanda yake tamfatsetse mai ɗauke da wasu manyan motoci masu numfashi a rumfunan guda biyu da suke ta gefe da gefe na gidan.
Gida ne ba muna gida ba, ƙaton gida wanda misalta girman gidan ma ɓata lokaci ne, yana ɗauke da part 4, part 2 dukansu upstairs ne, sai kuma part biyu da suke flat, amma suma ɗaya yafi ɗaya girma.
Part ɗin da yake ta hannun hagun su me benen suka nufa bayan driver ya adana motan a mazauninta, fitowa tayi tana ƙarewa gidan kallo, gabanta taji tana faɗuwa tana, Anya kuwa gidan nan ba gidan yankan kai bane? Sai kuma wata zuciyan tace mata, kinsan dai har abada Baba Sale bazai taba cutar dake ba.
Jikinta a sanyaye ta fito, driver ya fito mata ta jakarta Baba Sale zai ɗauka, tayi saurin kai hannu "A'a Baba ka bari, zan ɗauka" Haka ta dauka, shi kuma Malam Sale ya sake kiran Hajiyan yana sanar mata da isowar su, mai aikinta ta aika akan taje tashigo dasu, wadda tazo tayi masu jagora zuwa cikin gidan suna biye da ita.
Da isar su kofar gidan, mai aikin ta danna wani abu a bakin ƙofar, saiga ƙofar ta buɗe suka shiga da sallama.
Palour ne mai matuƙar girma da ke ɗauke da kujeru saiti biyu, akwai ƙofofi barkatai a ciki wanda ita dai Maryamah bazatace gashi ko ƙofofin menene ba, daga gefe, ta hannun dama akwai dining area wanda yake ɗauke da ƙaton dining table mai cin kujeru 10, sai ta gefen hannun hagu kuma ɗauke take da staircase wanda zai sadaka da saman wanda Maryamah bazatace ga yanda yake ba, amma shi kanshi staircase din abun kallo ne, dan kai tsaye bazakace ga da abunda akayi shi ba. Gashi irin mai faɗin nan ne wanda bazai ba mutum wahala ba wurin hawan shi saman, kuma akwai baranda wadda ke d5auke da ƙarafuna masu tsananin kyau kamar dai ginin gidajen India.
Da sallama suka shiga, suka samu wata hamshakiyar mata zaune akan ɗaya daga cikin luntsuma luntsuman kujerun da sukaiwa palourn ƙawanya, tana zaune cikin ado, tana danna wayarta ƙirar Samsung latest one, ɗago wa tayi tana amsa sallaman su, fuskarta cike da murmushi "lale Marhabun da Malam Sale, kun ƙara so kenan" tayi maganar tana ɗago idanuwanta daga kan wayar, wanda basu sauka akan kowwa ba sai kam Maryamah, shock taji ta shiga ta kalleta sossai, taji wani yanayi na shiganta akan yarinya, kuma lokaci ɗaya taji yarinyan ta kwanta mata a rai.
"Bismillah Malam Sale ku zauna" ta faɗa tana ƙara kallon Maryamah.
Waje malam Sale ya samu zai zauna a ƙasa.
Da sauri tace "A'a dan Allah haba Malam dan girman Allah ka hau kujera mana"
Haka Malam Sale ya hau kujera, Maryamah ta zauna a ƙasa kusa da kafarshi.
Gaisawa suka shiga yi da Malam Saleh cike da girmama juna.
Maryamah cikin muryanta mai daɗin saurare ta gaida Hajiya duk da muryan ta dashe saboda kukan data sha, Hajiya ta amsa tana mai maida kallonta gareta tace "Malam Sale wannan anya mai aiki ka kawo min ko ɗiya gata nan, Mashaa Allah"
Hakanan taka sa ɗauke idonta akan yarinya wadda kanta yake a ƙasa tana sauraren su.
Murmushi yayi yace "Todai Hajiya gadai tanan duk wanda kika zaba"
Kayan abinci mai aikinta ta fara jera musu Hajiya tace "Bismillah kuci abinci sai muyi magana"
Malam yace "A'a zamu fara sallah dai, akwai Azahar da La'asar a kanmu, a hanya suka riskemu"
"Eh lallai kam gara kuje kuyi kam dan ita kanta Asr ɗin lokacinta yaja tunda gashi har 5 ta ɗan gota"
Haka Malam ya tashi ya fita farfajiyan gidan, ya nufi inda ɗakin drivers din gidan da sauran masu aikinsu maza suke, inda wurin su yake ta can baya, yaje yayi sallah, kasancenwan ya saba dasu.
Itama Maryamah, haka Hajiya ta saka mai aikinta ta tafi da ita zuwa ɗakin su, tayi sallah sai ta kai mata abincinta can taci kafin Malam Sale ya kintsa ya shigo, sannan ta umarci mai aikin da in ta kai Maryamah ta turo ɗayar mai aikin ta kaima Malam Sale nashi can inda yake sbd zaifi sakewa a can.
★★★★
A can kuwa gida Charanchi, Baba Zainu bata dawo daidai ba sai da ta ɗauki wani lokaci mai ɗan tsayi sannan ta dawo hayyacinta, aikam da mugun gudunta tayi waje wanda ko mayafi bata tsaya ɗauka ba, haka ta doshi kofar gidan, tana zuwa zaure, sukayi karo da Hajjah.
"Lafiyar ki kuwa Zainu?" Hajja ta tambaye ta a tsoro ce.
Haba ai kamar abunda take jira kenan, ta ɓarke da kukan baƙin ciki "Shi kenan Hajjah, burinmu ya ruguje"
Cikin rashin fahimta, Hajjah tace "Bangane ba, mekike nufi da burinmu ya ruguje? shige muje gidan muyi magana, kin kama hanya kin fito kamar wata mahaukaciya"
Haka suka shiga gidan, Hajjah nacewa "meyafaru yasa duk kika wani firgice kamar wadda ta warke daga hauka?"
"Hmmm Hajjah Malam ya shammace mu gaba ɗaya ya ruguza mana tsari"
"Me shi Jafarun yayi kuma?" Ta jefa mata tambaya cikin rashin fahimta.
"Hajjah ya ɗauke yar shi ya bar garin da ita, kuma duk yasan shirin mu akan ta"
zaman daɓaro Hajjah tayi "ke bansan hauka ya ɗauke ta ya kaita ina tace?"
"Hajjah ban san inda ya kaita ba, nan da ya tsaya ya ƙare min tanadi tass, sannan ya tasa ɗiyar shi a gaba, yace ta bar mani gidan inci uwar da zanci dashi" Sallallami Hajjah ta fara tana "Wai shi Jafarun?"
"Shifa Hajjah"
Hajjah tace "Eh lallai kam ya nuna mini shi ya haifi abar shi, amma ki barni dashi, zaizo ya sameni duk inda ya kaita sai ya dawo da ita, wato ya nuna ban isa dashi ba, ina gidan ko ya faɗa mini zai bar garin da yarinyar, tsabar ya nuna mini ban isa ba koh aikam zai dawo ya sameni"
★★★
Abuja
Bayan sunci abinci sun natsa, Hajiya tasa aka kira mata su, nan suka sameta zaune inda suka barta, wata sabuwar gaisuwar sukayi.
"Malam naji daɗin cika alƙawarin da kayi min wallahi, kuma gashi ka kawo mini irin yarinyar da na keso, fatana dai ace ta iya ayyukan gida yanda ya kamata"
"Inshaa Allah bazaki samu matsala da ita ba, yarinya ce mai matuƙar ƙwazo da zafin nama, ɗiyar aminina ce, mahaifiyarta ta rasu tun tana jinjira ranar da ta haifeta, ita kuma ta koma ga Mahaliccinta"
Cikin jimami Hajiya tace "Allah ya sanyaya makwancinta"
Haɗa baki sukayi wajen amsawa da Ameen, Maryamah na share hawayen da suka zubo mata.
"Kiyi hakuri Maryamah, rayuwa ta gaji haka
kinji" cewar Hajiya.
Jinjina kanta tayi.
Bayan nan, Hajiya taja numfashi tace Toh Malam Sale, aikin Maryamah a gidan nan shara ne da goge-goge, saboda banajin daɗin na waɗannan da sukeyi, gani nake kamar basu iya ba, ita wadda takeyi da ta koma garinsu ne"
Malam yace "ba wani abu, inshaa Allah bazai gagara ba, zata iya"
Hajiya tace "alhamdulillah, sai kuma maganar kuɗi za'a ringa bata dubu hamsin a wata"
"Ba laifi Hajiya Allah ya ƙara girma, ya ƙara arziki mai albarka"
"Amin ya Allah"