← Book details Rantsatstsen Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 19

Sashe 14

Rantsatstsen Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Banza tayi da ita, dan ita kam laziness ɗin Zuhura na bata mamaki, Ji Maryamah tun safe take aiki har kitchen, tana sane, sai da taje ta kama wa su Iya aiki bayan ta gama nata.

Kallon Mamy Zuhura tayi tana tura baki tace "Mamy nace na gaji"

Banzan kallo Mamy ta watsa mata tace "To sannu uwata"

Jin hakan sai Zuhura ta kama kanta, Ita fa Mamy abu kaɗan ta faɗa maka, baƙar magana.

Juyawa tayi ta kalli Maryamah, ita kuma tace Sannu da dawowa.

Yau kam bata tsaya neman dalili ba ta amsata.

Dining area ta wuce tana faɗin "Yau kuma mai muka samu a nan" buɗe warmers ɗin tayi taga duk ba abinda yayi mata, ita Mamy sai tayi ta sanyawa ana masu abinci mai nauyi, rufewa tayi kawai, ta haɗa cornflakes ta cika madara, ta dawo parlour ta zauna, ta d6auki duka kafafunta ta hau dasu kan kujera.

Kallon abinda ta haɗo Mamy tayi tace, “Duk kukan yunwan abinda zakici kenan?"

"Eh Mamee, ni bana cin abinda akayi"
Mamy ta ɗage kafaɗa tace "nah you sabi" kawai ta cigaba da abinda take.

Ita kam Maryamah tana can twins sunata zuba mata surutu, Suna nan zaune su Adeel da Aqeel suka shigo da gudunsu, suna zuwa suma dai kan Maryamah sukayi.

Mamee tace "kekam kinga ta kanki Maryamah, yaran nan bazasu barki ba"
Murmushi tayi tace "Ai bakomai Mamy ai yara ne"

"Aikam dai dan dukkusan sa’anni ne, tunda su twins da Adeel 40 days ne tsakanin su yanzun suna 8, sai Aqeel ne karami dake da 6 yanzun"

"Mashaa Allah, Allah yayi wa rayuwarsu albarka"
Mamy ta amsa da Amin.........

FULANI
08082101373
https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr?mode=gi_t

https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr?mode=gi_t

🦋✨ RANTSATSTSEN RABO 🦋 ✨

BY RABI'ATU KABIR ACHADU (FULANI)

YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION YOTA

SADAUKARWA GARE KI HALIMA HASHEEM (MIEMIEN HABIBI)❤️& AHMAD JAMIL AHMAD (HABIBI)♥️

FULANI ❣️
08082101373

PAGE 1️⃣6️⃣

Ana kiran magrib mamy tace su tashi suje suyi alwallah su wuce masjid, idan aka dawo kuma yau baza'ayi hira ba saboda gobe zasuyi aiki sossai da maryamah, za'a gyara part ɗin daddy dana su Sadeek tunda jibi asabar ake sanya ran zasu dawo daga umrah.

Sunajin ance daddy zai dawo, suka fara tsallen murna da gudu suka haura sama dan yin shirin masallaci.

Bayan tafiyan su mamy ta kalli maryamah tace "kamar yanda kikaji gobe insha Allahu Alhaji zai dawo da shi da sauran yaran mazan gidan nan, dan haka kiyi bacci da wuri, aiki garemu sosai daga gobe"

"inshaa Allah"

Zuhura ce tace "Mamy tabar gyaran part ɗin Abba dana yaya sai na dawo na tayata mu gyara"

"Hakan na yayi babu wani abu"

Watsewa sukayi, kowa ya kama gaban shi suka nufi yin sallah.

Bayan ta shige iya tayi wa sannu da hutawa.

Amsawa tayi tare da tambayar ta, ta dawo.
Kanta ta gyaɗa mata.

Bayan sunyi magrib da isha'i, tana zaune kan prayer mat, Iya tace yau bazakije ki taya mutanenki hira bane.

"Yau hajiya tace musu ai baza'a yi hira ba saboda gobe zamuyi aiki sosai, tace megidan da yaran gidan maza zasu dawo"

"Ƙwarai kuwa anyi haka, gobe kam akwai aiki, kinsan yaran su 5 ne manya maza, Ita hajiya nan tanada biyu, ita kuma uwargidan tanada uku"

"Allah sarki" kawai tace dan bata san mai kuma zata ce ba.

Iya ta cigaba da faɗin, "Fatana ki samu karɓuwa kamar yanda kika samu a gurin ƙananun yaran, koda yake babban nema mai wahalan sha’ani, duk da ba magana yake ba bashi da hayani, amma dai yaran gidan na matuƙar tsoron shi da kuma girmama shi sosai, gaskiya dan zance bayan Alhaji to shine mai zartar da hukunci, kuma duk abinda ya yanke shi kenan, shiyasa dole sai kinyi takatsantsan"

"Inshaa Allah Iya nagode sosai, Allah ya kara girma"

Da fargabar dawowar sauran yaran gidan maza, ta kwana tana tunanin ko ya zasu kaya, itadai Allah ya sani bata son wulaƙanci, amma dai zata ci gaba da addu'a.

★★★

Yau ma kamar jiya haka ta tashi tayi sallah da azkhar ta karanta shafi ɗaya kawai saboda tasan yau sunada aiki, gashi tana so ta fara da wuri, Iya ta gaida kawai ta ɗauki hijab ɗin da take aiki dashi ta sanya, ta ninke wanda tayi sallah dashi ta fita main parlour na gidan ta fara aikinta.

6:30 har ta gama gyaran parlourn ƙasa, ta haura sama ta fara gyarawa, Shima 7 ta gama ta sanya room freshener da turaren wuta.

Tana cikin sakin curtains ɗin, mamy ta fito, duƙawa tayi ta gaisheta, ta amsa tana faɗin, Wai har kin fara aikin kenan.

"Eh, na gama da ƙasan nace bari na fara nan kafin ki tashi"

"Mashaa Allah, sannu da ƙoƙari" tayi mata sannun cike da jin daɗi.

Amsawa tayi da yawwa kanta a ƙasa.

Ɗakin su Fadil mamy ta wuce tana so taga in sun shirya dan time na tafiya, Ita kuma Maryamah ta nufi ɗakin mamy ta gyara mata.

Koda ta gama gyaran ta fita har yaran sun gama breakfast, sun wuce school da Zuhura.

A ƙasa ta samu mamy tana zaune a parlour tsugunnawa tayi tace "Mamy na gama sai ina za kuma ayi?"

Albarka ta sanya mata "Inaga za'a fara da part ɗin su sadeek ne, kuje dasu sahura su kama miki kowa ya gyara ɗaki daya, guda huɗu ne, daga nan idan kun gama zuwa anjima in baby ta dawo sai ku gyara na Alhaji da na babban yayansu"

Harta miƙe mamy tace ta jira su sahuran suzo.

Waya ta ɗaga ta kirasu akan su sameta a main parlour, cikin ƙasa da minti 5 suka ƙaraso, amma ganin Maryamah already a wurin ya ɓata ransu dan sunso ace su kaɗai ta kira, Ce masu tayi su haɗu da Maryamah, suje su gyara part ɗin su Sadeek, da to suka amsa suna miƙewa gaba daya.

Kallon maryamah tayi "kijira na kawo miki keys ɗin part ɗin da ɗakunan su"

Sama hajiya ta haura inda tabar su sunata hararar Maryamah da ƙananun maganganu.

Ita dai bata bi ta kansu ba, haka suka wuce kowa da mugun nufi a ranshi.

Bayan tafiyar su mamy ta sakko ta bata keys ɗin, ganin bata ga su sahura bane yasa ta tambaye ta suna ina.

Sunyi gaba kawai tace mata.

"Ok idan kika fita part ɗin nan ta gefen hagu, zaki ga wani part ba ginin bene ba, zakiga ƙofa ta kasu biyu ta hagun ita ne ta part ɗin su Faruk, shi na yayansu anjima zaku gyara da Zuhura.”

Data fita a bakin ƙofar part ɗin da mamy tace mata nasu Sadeek ne taga su sahura suna tsaye sun cika fam…

tana zuwa suka hau masifa, wai ta shanya su. Ita dai cikanku bata ce masu ba, taje jikin ƙofar ta sanya key ɗaya ta fara gwadawa tana so taga wanda zai buɗe a cikin su.

Koda ta samu na ƙofar murzawa tayi ta buɗe ta shiga, tana zare sauran keys ɗin ta shiga dasu.

Bin bayanta sukayi suna sakin tsaki, da suka shiga nan ma ƙara gwada keys ɗin tayi har ta gane na ɗakunan ɗaki 4 ne a ciki, biyu hagu biyu dama, duk buɗe su tayi, ta kalli su Dije da suka nemi kujeru, suka zauna kamar ɗakin uwar su akuyar kulle ta samu sake.
"Bismillah, zamu iya farawa"

Sunajin haka suka yo mata caaa da masifa "Toh uwar iya ai da yake kinfimu sanin abinda ya kamata"

"Allah ya baku hakuri" ta katse su tana shiga ɗakin dake farko, tana shiga ta fara gyarawa duk da ba wani datti yayi ba, amma ya ɗanyi ƙura kaɗan, tsaff ta gyara shi cikin ƙanƙanin lokaci, ta canja bedsheets, ta wanke toilet, sai ta sanya room freshener ta kullo ɗaki.

Parlour ta dawo nan ma ta gyara, time ɗin su ba wanda ya gama gyara ɗakin da ya shiga har ta gama gyaran parlourn, basu fito ba aranta tace, Komai suke oho.

Su kam ashe suna sane suka ƙi fitowa suka barta da aikin.

Ɗayan ɗakin ta shiga kawai ta gyara dan bata ga amfanin tsayawa jiran su ba.

Suna jin shiganta dayan ɗakin sai gasu sun fito, daman sun gama kawai basa so su fito ne su gyar, koda suka fito basu tsaya jiranta ba, tafiyan su sukayi hankali kwance.

Bayan ta gama ta fito taga basa nan, rufo ɗakunan tayi ta fito, tana cikin rufe part ɗin ne wata hamshaƙiyar mata ta ƙaraso wajen cike da izza, da ganinta zatayi rashin mutunci, duk da ba a shaidan mutum daga ganin farko, bata san dalili ba amma sai taji samm matar batayi mata ba.

Ƙarasowa wajen tayi "Ke ubanwa, yace ki buɗe gurin nan" tayi maganar a tsawace.

Maimakon taji tsoronta, sai ta tsaya tana mata kallon ido cikin ido, dan haka nan taji matar batayi mata ba, kuma bata da kwarjini Sam a idonta, tace hajiya ce, tace a gyara ma yaranta zasu dawo.

Cike da isa ta ƙara daka mata tsawa "Cire idonki cikin nawa yar matsiyata, kina kallon mutane cikin ido gidanku ba su baki tarbiyyan da ya dace bane halan?"

Don ita kanta a nata ɓangaren ganin yarinyar, saida ya sanya mata mummunar faɗuwar gaba, kuma lokaci ɗaya taji ta mugun tsanar yarinyar, duk da bata san wacece ita ba, kuma bata tantance matsayinta ba a gurin waccan matar uwar yan kwashe-kwashe.

Kauda kanta tayi gefe duk da taji zafin maganar matar, amma tunda rashin girmama na gaba da ita ba halinta bane, yasa ta ƙyaleta, dan ko su baba sai da taga zasu kasheta da azaba ta fara kwatar kanta a gurinsu, cire key ɗin tayi ta ƙara kallon hajiyar cikin ido, sannan ta ɗauke kai, tayi gaba ba tare da ta amsata ba.

Hakan da tayi ya ƙara rura wutar tsanar da hajiyan taji tanayi mata duk da bata san wacece ita ba, fisgota wata zuciyan tace tayi, amma sai kuma taga ai ba girmanta bane, ta tsaya sa’insa da wannan kuchakar a compound ɗin gidan, ƙwafa tayi, zamu haɗe in har ta tabbata itace yar aikin da akace waccan matar ta kawo gidan, ta rantse da wanda ranta ke hannun shi, wannan karan sai yarinyar ta bar gidan, dan bazai yiwu ta dinga masu kwashe-kwashe ba, wataran ta kwaso wanda zai zamar musu jaraba.
Chapter 14 · 0% Book details