← Book details Rantsatstsen Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 19

Sashe 15

Rantsatstsen Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Part ɗinta ta wuce tana kwala ma ɗiyar ta kira mai suna Farha. Zaune ta same ta tana famman danna waya, hankalinta kwance kamar bataji uwar tana kiranta ba, ranta ne ya ƙara ɓaci akan wanda ta shigo da shi.

tsawa ta daka mata "bakiji ina kiranki ba bane?"

Ɗago idonta tayi daga danna wayar, itama cike da izza, wadda har taso tafi ta uwar tata "Lafiya?" Ta mayar mata da tambayar ta.

Zama tayi kusa da ita "Kinsan kamannin yarinyar da akace Zeenatu ta dauko aiki?"

Girgiza kanta tayi ta cigaba da danna wayan ta, sai zuwa can ta ɗago ta kalli uwar tace "Mom miye haɗina da ita da zan san kamanninta? Infact ni ban ma taɓa ganinta ba, kin manta Nabeela ce ta ganta tazo take faɗa maki?"

Wani zazzafan huci mom ta sauke "Hmmmn wata useless yarinya na gani ta fito daga part ɗin su Haydar, kinsan inama yarinyar nan magana ta wuce ni ta barni tsaye" ta ƙara sa maganar cike da takaici.

Ido Farha ta zaro cike da mamaki "Who the hell is she?"

Mom tace "Ina zan sani dan ubanta? Aikam in itace mai aikin, gobe daddy ku na dawowa dole ta maidata inda ta daukot wallahi!!!!

Ta ƙarasa maganarta ta cike da alwashi.....

FULANI
08082101373

https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr?mode=gi_t

https://chat.whatsapp.com/DysmUMWo6dYJlLWGBPOMEI?mode=gi_t

✨🦋 RANTSATSTSEN RABO ✨ 🦋

BY RABIA'TU KABIRU ACHADU (FULANI)

YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION YOTA

SADAUKARWA GARE KI HALIMA HASHEEM (MIEMIEN HABIBI)❤️& AHMAD JAMIL AHMAD (HABIBI)♥️

FULANI ❣️
08082101373

🦋✨ RANTSATSTSEN RABO 🦋 ✨

PAGE 1️⃣7️⃣

Koda ta shiga bata faɗawa mamy ga abinda yafaru ba kawai keys ɗin ta maida ma mamy tace sun gama sannu tayi mata tana sanya mata albarka tace taje ta huta kafin Zuhura ta dawo in sunyi azahar sai suyi aikin ko zuwa azahar ne.

Ɗaki ta shiga daman a jigace take dan yau ba ƙarya ta aikatu gashi bata ma gama ba, tana shiga wanka ta farayi sanan ta zauna zaman breakfast time din 10:30 na safe flashing tama babantayan katsewa yayi ya kira ta dauka cike da shauki da kewa tace babana! Shima a can bangarenshi cike da kewar gudan jinin nashi yace diyar babanta kina lafiya, tace alhamdulillah sai tsananin kewar ka baba. Murmushi ya saki mai sauti yace to ai gani a waya, cikin yar shagwaɓan tace to ai kewar ta zahiri ce. Haka sukayi wayan cikin tsananin so da kauna irinta ɗa da mahaifi har sai da katin shi ya kare sukayi sallama.

Bayan sun gama takwanta tunda taga akwai sauran time aikam bacci ya ɗauke ta, ba ita ta farka ba sai 1 iya ta shigo kusan sau biyu amma ta sameta tana bacci kuma bata tada ta ba tunda tasan yau kam tasha aiki a haka ma ba gamawa tayi ba.

Tana farkawa sallah tayi ta fita kitchen ta fara shiga ta same su sun kacame sunata aiki kowa da abinda yakeyi a ranta take cewa ko mutune nawa ne zasuzo wannan uban kayan fulawa da akeyi(snacks). Sannu ta masu iya ta amsa su kam tsaki suka mata bata damu dasu ba dan batasu take ba, wurin iya ta karasa tace mata sannu da aiki iya, tace yauwa Maryamah kin tashi kenan, tace eh ashe bacci ne ya ɗauke ni ban sani ba me zan kama maku dashi naga kunata aiki, Iya tace a'a kibarshi ɗauki abincinki kici in kin gama sai kije wurin hajiya dan naji hajiya ƙarama (Zuhura) na neman ki sannan mutanen ki ma sunata zaryan nemanki dan ma hajiya ta hanasu tadaki da taji kina bacci ne.

Murmushi tayi tace to bari naje in na dawo sai naci abincin, Iya tace a'a da dai kintsaya kinci saboda in kikaje be zama lallai ki dawo yanzun ba yau aiki garemu da yawa.

Tace ai banajin yunwa kinga ina cine ma bayan na gama bacci ya ɗaukeni, haka ne sai kin dawo.

Kitchen ɗin ta fita ta nufi parlour inda tana dosowa taji hayaniyan su da kamar ma ƙarin wasu mutanen, a nutse ta shiga da sallama gaba ɗaya hankalin mutanen parlourn ya dawo kanta yayinda su twins suka fara rige rigen zuwa wurinta suna faɗin oyoyo cutie itama hanayenta ta buɗe musu kaɗan duk da bata so ta zaƙe amma bai kamata ta share ƙaunar da yaran ke nuna mata ba, jikinta suka shiga cutie we miss you kansu ta shafa to ai gani kuma kunga weekend za a shiga zamuyi hira sosai.

Sunajin haka suka fara tsallen murna, ɗago kanta tayi da murmushi taga yanda baƙuwar fuskan dake zaune kusa da mamy tana breastfeeding babyn ta wadda bata wuce 11 months ba,ta saki baki tana kallonta tana murmushi.
Ƙasa tayi da kanta tace mata ina yini ta amsa cike da sakewa "Mashaa Allah daman kece cutie ɗin da su Fadil suka damemu da labarinta kenan tunda na iso abun mamakin wai har da Fudail" murmushi kawai tayi ita kuma waccan ta cigaba da "ah Mashaa Allah lallai kinci sunan cutie"

ta kalli mamy tace "mamy ina kika samo kyakkyawan ɗiya sai ki bani itama kawai in zan koma mu tafi tare gaskiya"

"Toh uwata aminatu dole zan baki ita mana tunda ina tsoronki ko kada ki min baki na lalace"

Dariya duk sukayi "au nafa manta mamy yanzun zaki fara mita amma dai Allah nikam dama ki bani ita"

Banza mamy tayi da ita dan bata ganin zata ƙara tanka mata ta maida kallon ta ga Maryamah tace "kinzo kucigaba da aikin ne?" "eh haj....." kafin ta ƙarasa Fudail yace "mamy not hajiya'

Gaba ɗaya falon murmushi sukayi mamy tace "Maryamah haƙuri kawai zakiyi ki dena kiran hajiyan nan tunda su Fadil sun bani ke matsayin ɗiya"

Itama murmushi tayi tace inshaa Allah mamee, mamee tace ko kefa, kallonta ta maida kan zuhura da tun ɗazun bata ce komai ba "hajiya fati a tashi a fara aiki koh?" Dariya duk sukayi Zuhura tace "yau kuma fati na koma mamy?" tace yo eh mana ai duk sunan ki ne.

Tashi tayi "muje to may be daga nan zuwa asr mu gama tunda ba wani datti ne dasu ba"

mamee tace "probably amma sai idan kun maida hankali baki tsaya zuba magana ba" "kai mamee" ta faɗi tana kumbura baki, aunty amnah dake zaune tace hali ai mamee ta sani. Ita kuma Zuhura ta ƙara tunzura baki tace mamee kinji aunty ba. Mamee tace ki tsaya shaida kada ki tafi kuyi abu5nda ya dace.

Tashi sukayi tace ma Maryamah "cutie muje" itadai in sukace cutie ɗin nan sai taji abun wani banbarakwai haka tabi bayan ta su Fadil sukace zasu bita mamy tace bazasu ba in sunje bazasu barta tayi abinda ya dace ba.

Haka suka fita ita da Zuhura tana ɗan yi mata hira kaɗan kaɗan ita kuma sai murmushi kawai dan batasan mi zata ce ba, ko da sukaje part ɗin daddy Zuhura ta sanya key ta bude suka shiga, part ɗin din shigen yanda ginin part din mamee yake shima haka yake, furniture's ɗin ne kawai suka babanta sai kitchen ɗin da yake dan ƙarami sannan kuma ƙasan 2 bedrooms ne kawai.

Sama Zuhura tace su fara gyarawa suka dunguma sukayi sama, nan ma dai Maryamah tasha kallo amma tana kamewa dan kada Zuhura ta fuskanta haka ta ringa mazewa, ɗakin daddy suka fara shiga Zuhura tace tare zasuyi komi ita dai Maryamah binta kawai take, gado Zuhura ta fara gyarawa ita kuma Maryamah ta shiga toilet ta wanke shi fesss.

Sanda ta gama ta fito itama Zuhura ta gama gyaran ɗakin tayi mopping ta canja bedsheet, turare ɗakin sukayi sannan suka fito suka gyara parlour sama daga nan sukayi ƙasa shima suka gyara shi tass in not less than an hour sun gama komai na part ɗin daddy, Zuhura nata zuba mata surutu dan surutun ta ma yafi aikin yawa.

★★★

Bayan sun gama part ɗin wanda taji anacewa shine babban yayan su suka nufa, suna tafiya Zuhura tace "to Allah yasa in mun gyara in ya dawo yace yayi dan shi yaya ba a mishi gwaninta ka gama wahala yazo ya ce baka iya komai ba" ta ƙarasa tana ɓata fuska.

Jin yanda Zuhura ke mita yasa Maryamah jin fargaba akan aikin nashi batasan tace ma Zuhura to in beyi mashi ba ya yakeyi cikin low tone.
"Hmmmn idan ya fara masifa ba hmmmn daga karshe sai ya gyara abinshi baya yarda ana gyara mishi part fah cewa yake wai duk bamu iyaba, babu abinda muka iya, but a haka ma wai ni yace idan nayi yana ɗanyi mishi akan nasu ya Farha da Husna na part ɗin mom, sukam yace ba abinda suka iya sai ciye ciye da lalaci wai mijin da ya aure su ya shiga uku da ƙazanta imagine fah" ta faɗi tana yar dariya.

Itama Maryaman dariyan ne tayi kadan tace "amma dai yayan baya duka koh kamar in an mishi ba dai dai ba?"

Dariya Zuhura tayi "ah haba baya duka but ya iya punishing mutane in such a way that zaka so ma ace dukanka yayi wallahi" tayi maganar tana ɓata fuska.

murmushin yaƙe Maryamah tayi a ranta tana fadin inshaa Allah bazamu hadu ba balle har ya sanya ni abu nayi ba daidai ba.

Suna isa nan ma Zuhura ta buɗe musu suka shiga Maryamah ba tasan lokacin da tace wow Mashaa Allah tana haɗe yatsunta wuri ɗaya tama manta ba ita kaɗai bane a wurin.

Saida taji Zuhura tayi magana "so you like the part" dage mata gira tayi alamun tana jiran amsa.

A take ta dawo hayyacinta cikin jin kunya tayi ƙasa da kanta.
"Allah baki isa ba tunda muka taho nake miki surutu baki nuna labarina na burgeki ba and munzo nan Allah ya kamaki kika buɗe baki kikayi magana daga zuciyan ki yanzun dan nayi magana zaki wani ƙasa da kai wai kunya"

Yar dariya tayi tace "kai wai daga zuciyana inji waye yace daga zuciya na na faɗi ban ma fa san na faɗi ba" tayi maganar a shagwaɓe ba tare data kula da hakan ba, dan ɗan sakewan nan da tayi da yanda Zuhura ke mata surutun sai tajita kamar tana tare da Sahiban ta.
Chapter 15 · 0% Book details