← Book details Rantsatstsen Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 19

Sashe 4

Rantsatstsen Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“To shikenan Hajiya Zamu taho ko zuwa jibi ne, domin yarinyan marainiya ce, mahaifiyarta ta rasu, toh tana ɗan fuskanta wasu ƙalubale ne, yasa baban duk son da yake mata ya haƙura, yace gara ta bar garin duk da kuwa yarinyan nakan zuwa makaranta, dan gaff suke ma da zana jarabawar fita daga karamar sakandire”

Hajiya tace “Ashsha abu beyi daɗi ba Allah ya kyauta, inshaa Allah karatunta bazai gagara ba In kun shirya ɗin sai ku taho jibi yanzun, zan tura maka kudi, sai kuyi amfani da shi, Itama sai abata in tana bukatan wani abu ko shi mahaifin nata”

“To Hajiya, amma su dukan su ba dan wani abu suke son aikin ba, sai dan neman mafita inaga kuɗin abun hawan ma ya isa”

“Aa, duk da haka dai a basun ai haƙƙin su ne.”

“Toh mun gode Allah ya ƙara girma”

Amsa mishi tayi da “Ameen nima nagode, sai da safe”

Bayan sun gama wayar ne, ya kalli malam Jafaru yace "Kadaiji yanda mukayi da ita" kasancewan a speaker ya sanya shi.

“Eh, naji komai, nagode sosai da ƙoƙarinka, Allah ya saka da mafificin alkhairi, Allah ya jikan iyayemu, ya raya mana zuri'a, ya kuma cigaba da basu kariya akan komai"
"Amin amin yanzun sai ka zauna, muci abinci, tunda alhamdulillah mafita ta samu, koh?" Ya faɗa yana murmushinsu na manya.

Shima malam Jafaru murmushi yayi yace "Ka bari kawai malam sale, bazan iya misalta maka tashin hankalin dana shiga ba wallahi"
"Akwai tashin hankali kam babba ma, Allah dai ya kyauta, su kuma Allah ya ganar dasu” "Ameen dai"

A nan sukaci abincin suna dan taɓa hiran abun da ya shafi rayuwa da yanda son zuciya ke sanya mutane aikata ɓarna da yanda ƙasar ta lalace, bayan sun gama, malam ya karayi ma malam Jafaru godiya sannan ya tafi gida cike da tunani kala kala, duk da baya son rabuwa da ɗiyar shi, amma yana ganin kamar tafiyan ta sai yafi zamanta alkhairi, dan haka bashi da wani zaɓi.

Da wannan tunanin ya isa gidan, Lokacin tara ta wuce sosai dan su kansu su Baba Zainu sun shiga ɗaki, ita da Hassu da su Zainab, kasan cewa a dakinta su suke zaune, saɓanin Maryamah da take ita kaɗai a ɗan karamin ɗakin da be kai nasu baban girma ba.

Da sallama ya shiga gidan, wanda Maryamah tayi zaraf ta fito tana amsa sallaman baban nata. Sai lokacin hankalinta ya kwanta, Ta kalli baban nata cike da kauna ma tariya yawa tace "Baba, hankalina ya tashi najika shiru" Ta faɗa cike da yar shagwaɓa har da hawaye. Dan ita dai indai tana gaban babanta zakaga taɓara kala kala.

Shima cikin tsanin ƙauna ya kalle ta yana murmushin karfin hali ya bata amsa "Yar shagwaɓan babanta, bakiyi bacci ba kenan? me kika tsaya jira?"

Ƙasa tayi da kanta tana ɗan tura baki irin na shagwaɓaɓɓun yaran nan da suka samu kulawar mahaifinsu irin wadda bata keta shari'a ba.

"Babana! baban Maryamah! Ina Maryamah taga bacci, bataga abincin ruhunta ba"
kasancewan sunada kyakkyawan mu'amala ita da mahaifin nata, tunda ta tashi shi take gani taji sanyi a ranta, Shine uwar ta, shine ubanta, shine yaya kuma abokin hiranta, dan in tana hira da babanta, bazaka ce itace wadda magana ke wa wahala ba. Tana tuna memories nata da babanta sanda tana yarinya, ko irin lokacin zafi ne in babanta yayi shimfida a ƙofar gida karkashin bishiyan darbejiyan da suke dashi, tofa ita kuma zaka sameta kwance a akan cikin shi, kaff abokan babanta ba wanda besan ƙaunar dake tsakanin wannan uba da yar ba, wasu ma daga cikin su Maryamah babanta suke ce mata har yanzun daga cikinsu ma akwai malam Sale aminin babanta.

Kama hannunta yayi ya shiga da ita dakin Hajjah yana bata amsar maganar ta cike da jin daɗi, "toh ai ga baban Maryamah nan ya dawo cikin ƙoshin lafiya, ya samu ƴar amanar shi itama tana lafiya"

Ya ƙarasa yana sakin kyakkyawan murmushi akan dattijuwar fuskar shi, a duniya bashi da wani abun dake saka shi farin ciki bayan ganin yar marainiyar shi cikin walwala.

Da shigansu, suka iske ta tana jan numfashi kamar rago. Kai kawai ya girgiza maganganun su na dazun suna dawo mishi a rai, yace, “Ashe tamayi bacci, to mu tafi sai da safe.” Suka fito yana mai ja mata ƙofan ɗakin. Daki ya shiga, ita kuma ta nufi kitchen zata kawo mishi abincin shi.

Yace, "Zo, bar abincin nan a koshe nake, daga gidan Baban Sale nake can naci abinci"
“To” Tana me bin bayan shi zuwa cikin ɗakin. Bayan sun zauna, ya kalle ta yana me kiran sunanta.
Ɗago kanta tayi takai dubanta kan fuskar mahaifin nata kasancewan nepa sun kawo wuta da karfe 9, sai a lokacin taga damuwa kwance saman fuskar shi, dan ita in ma ba gizo idonta yake mata ba, sai taga kamar ya faɗa.

A ɗan rikice tace, "Babana meyasa meka murance dai? To kona dafa maka ruwan zafi me kayan yaji?" Bata jira cewar shi ba ta miƙe.
Hannunta ya kamo, yana mai girgiza mata kai "Dawo ki zauna magana zamuyi......

FULANI
08082101373

https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr?mode=gi_t

https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr?mode=gi_t

✨🦋 RANTSATSTSEN RABO 🦋 ✨

BY RABIA'TU KABIR ACHADU (FULANI)

YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION YOTA

SADAUKARWA GARE KI HALIMA HASHEEM(MIEMIEN HABIBI)🤍 & AHMAD JAMIL AHMAD (HABIBI)♥️

FULANI ❣️
08082101373

🦋✨ RANTSATSTSEN RABO 🦋 ✨

PAGE 5️⃣

Haka kawai taji gabanta ya faɗi zama tayi cikin sanyin jiki.
Cikin sanyin murya tace "babana ina jinka"

Shiru yayi yana tunanin ta ina zai fara mata bayanin da za ta fahimce shi, duk da ya san bai gaza a kanta ba wajen tarbiyyar da ya yi mata, amma ya san abin ba mai sauƙi ba ne rana tsaka ya zo mata da maganar tafiya aiki.

Shirun data ji ya yi yawa ne yasa tace "Babana!" Tana ɗora hannun ta akan nashi.
A jiyar zuciya ya sauke yana dawo daga dogon tunanin daya tafi, kallon ta yayi cike da tausayi ya fara mata magana cikin sigar rarrashi da fatan kuma tayiwa maganar shi kyakykyawar fahimta.
"Ɗiyar baba kin san babanki mai sonki ne ko? Kuma kin san a duk duniyar nan duk wanda zai so ya ga farin cikinki da walwalarki bayan nine?"
Cikin zaƙuwa da son jin abin da zai ce, ta ɗaga kai tana bashi amsa a ɗaɗare "Na sani babana, meyafaru?"

Ɗauke kallon shi yayi daga kanta "Kiyi haƙuri Maryamah, ba ni da yadda zanyi ne shiyasa, wannan ce kawai mafita a halin da muke ciki"

Cikin tashin hankali tace "Baba wane hali muke ciki? kuma menene ya faru?" Take idonta ya fara tara hawaye domin jin yanda gabanta ya tsananta faɗuwa, burinta kawai ta ji wane hali mahaifinta ke ciki.

"Ki kwantar da hankalinki, ba wani abu ba ne gagarumi, kawai ina neman wata alfarma ne a wajen ki Idan da hali" ya faɗa yana yin ƙasa da kansa.
Zuwa lokacin sosai hankalin ta ya tashi cikin ƙarfin hali tace "Baba ka fi ƙarfin komai a wajena domin kai ne duniyata, kai kaɗai gare ni, kai nake gani nake samun natsuwa a raina wallahi babana raina fansa ne a gare ka"

Murmushi ya yi yace, "Allah ya yi miki albarka, ya kula min dake a duk inda kika tsinci kanki" “Ameen baba”

"So nake ki shirya ki haɗa kayanki da duk abin da kika san zai miki amfani, da takardun makaranta gaba ɗaya ki haɗa su waje ɗaya,Idan Allah ya kaimu jibi da rai da lafiya, zaki bi babanki Sale zuwa garin Abuja, zaki koma can da zama kina kama wa matar ubangidansa aiki"

Wata iriyar mummunar faɗuwar gaba da tsoro da firgici ne suka dirar mata lokaci ɗaya, kanta ta ɗago ta ɗora dararan idanuwanta kan mahaifinta a rikice tace "Amma baba" kuka ne ya sarƙeta dole ta haɗiye maganar ta, sosai hawaye yake zuba a fuskar ta tamkar an buɗe famfo.
Hannunta ya kama ya riƙe yace "Maryamah yadda kika ji haka nake nufi, ki sani ba mu da wata mafita, wannan ce kawai mafitar mu, Idan na barki kika ƙara sati a garin nan, ban san girman abin da su Hajja za su aikata miki ba, Kuma idan na ɗauki mataki a kan Zainu, Hajja fa ba zan iya ɗaukar mataki a kanta ba, saboda uwata c mahaifiyata ce, ba ni da yadda zan yi da ita, Kuma duk ba ma wannan ba, idan har wani abu ya same ki Maryamah, zuciyata ba za ta taɓa ɗauka ba, ni na san mutuwa zan yi" Ya ƙara sa maganar hawaye shima suna wanke fuskarsa.

Ba ta san sanda kuka ya kuɓuce mata ba, hannu ta saka ta toshe bakin ta dan hana kukan nata fitowa har ta janyo hankalin mutanen gidan duk da sunyi bacci, sosai take kuka har tana shiɗewa baban na dan bubbuga mata kafaɗa, sai da ta ɗan rage kukan ne.
Yace "kiyi haƙuri bada son raina zaki tafi ba, amma abinda naji yau ya sanya ko kwana biyun da za ki yi a garin nan, wallahi a ɗarɗar zan yi, ba zan taɓa samun natsuwa da kwanciyar hankali ba sai na ga kin bar garin nan, Insha Allah mugun nufin Zainu sai dai ya koma kanta" Ya ƙara da cewa "Da'ace na san inda dangin mahaifiyarki suke, tabbas wannan karan da sai na sadaki da su, komai za su yi min zan ɗauka akan zaman ki a nan"
Cikin shaƙaƙƙiyar muryar ta data sha kuka tace "Ba komai baba duk hukuncin da zaka yanke a kaina daidai ne, ka isa kayi, ka daina roƙona kai uba ne, ba za ka taɓa cutar da ɗiyar kaba, Na amince Allah yasa haka ya zama mafi alkhairi"
"Ameen"yace yana mai sanya mata albarka.
Chapter 4 · 0% Book details