Sashe 17
Rantsatstsen Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ajiyeta tayi a gefe, tama Aisha flashing sai kam ga kiranta ya biyo baya.
Tana ɗaga wayan ta, ta fara "ayita kiran mutum, amma bazai dauka ba"
Cikin dariya Maryamah tace "Aifa ke baki ba mara ɗa kunya"
Dakatawa Aisha tayi da masifar "Ban gane ba"
Cikin dariyar tace "Daman nace zansha masifa tunda naga tarin miss calls naki, sai gashi kina kira da abinda kika fara kenan"
"Yanzu shedan da kika mini ma kenan?"
"Ba wani shaida, halinki na faɗa ai"
"Nagode sai anjima ma an fasa hiran"
Cikin sauri ta katse ta "haba tawan" tana jiyo murmushin Aishan.
"Ai indai yaudara ce, an barmiki kayan ki, duk wani mai sweet mouth bayanki zai biyo"
Dariya sukayi gaba ɗaya, bayan sun tsagaita ne Aisha tace "ya garin shugaban ƙasan ne? "
"Hmm gamu nan a cikin shi, har yau na kasa sabawa da garin sahiba"
"Haka nan zaki cigaba da daurewa zaki saba, ya mutanen gidan suke?"
"Hajiyan da nake tare da ita bata da matsala, damuwata masu aikinta guda biyu sukam bansan mena tare musu b, basu da aiki sai habaici da ƙananun maganganu"
"Baki cimin uwar su ba?"
"To uwar rashin haƙuri, meye amfanin faɗan nikam? Me lokacin su ma banda lokacin shi balle su ɗin da kansu"
"Miskila kafi mahaukacin kare ban haushi" A'isha tayi maganar da murmushi a muryarta.
Murmushi tayi kadan, tace zakiji dashi ke kam.
Maryamah tace "yawwa sahiba wai kinsan mene?"
"A'a meyafaru?"
"Hmm na baki labari wani yayansu sune kinji yanda suke kuranta shi, amma in kinga wadda zai aura sai takaici ya kusan kasheki, dan gaba ɗaya sai kin raina ma ajin shi da komai ma da akace yanadashi"
Cike da mamaki A'isha tace"Ikon Allah kinganshi ne da har kika gane macen bata dace da shiba?"
"Ko ban ganshi ba yanda suke faɗin shi da tsarin shi, Allah nidai dana ganta na raina mishi, kuma Allah gani ɗaya na mata naji bana sonta samm a raina" Ta faɗa tana ɓata fuska.
Dariya Aisha tayi "Yau naga ikon Allah toh waini shatutu, ina ruwanki dashi da matan da zai aura?"
Jin Aisha na mata dariya ya sa a ƙugule tace "Au mahaukaciya ma kika maidani kenan? sai an jima" ta faɗi tana kashe wayan, dan ji tayi yanzun har Aishan ma da shi yayan nasu da bata sani ba da wadda zai aura ɗin duka haushi suke bata.
La'asar taji an kira ta tashi tayi alwalah ta kabbara sallah, ta kusan idar wa Iya itama ta shigo ta ɗauro alwalah, bayan ta idar ta tsaya tana kallon Iya a ranta, tace tsohuwar na nada son addini"
Bayan baban ta idar ne Maryamah ta gaidata, ita kuma ta amsa tana tambayar"har kun gama aikin?"
"Eh wallahi mun gama aikin yayi mana sauri, kuma parts ɗin ma duka biyun basu da datti sossai"
"Ai da yake na Alhaji be daɗe bayanan ba, shima na Alhaji ƙarami baza a samu datti ba, gaskiya saboda hajiya na bakin ƙoƙarin ta gurin ganin an shiga an gyara duk bayan kwanaki, bari nakoma kitchen ayyukan da yawa, gashi gobe inajin ƙilan gidan ya cika bayan su Alhaji sun dawo, kinsan ahalinsu basu da yawa sosai amma sunada ƙoƙarin zumunci gaskiya dan yan uwa ne masu matuƙar ƙaunar juna"
"Allah sarki toh Iya idan akwai abinda zan kama maki dashi na biyo ki mana?"
"A'a ƴar nan ai kinsha aiki ki huta kawai"
"Ina so inga yanda ake abubuwan yan gayu, ina so na koya nima"
"To shikenan tashi muje a hankali zaki iya ai tunda kina so"
Kitchen suka nufa, lokacin su Sahura, sunata faman suyan kaji, dan sun gama snacks ɗin sai kajin da dambun nama, Hajiya tace ayi ma Alhaji da son dinta, daman sune sarakan cin shi, dan duk gidan sunfi amfani da shi, da suka shiga bata biye ma halin su sahura ba tayi musu sannun da aiki.
tsaki sukaja dan har ga Allah sun tsani su buɗe ido su ganta a cikin gidan, dan gani suke nan gaba kaɗan sai ta fisu fada a gidan, dan sun tsani yanda yaran gidan suka sake da ita, sai kace ita ta rigasu zuwa, bayan sun rigata
Kallon su Iya cike da ɓacin rai "Wai ku lafiyan ku kuwa? Yarinyar nan tunda tazo gidan nan take binku, amma kullum da kalan wulaƙancin da kuke mata, Waɗanda take zaman su ma basu takurata ba, sai ku da kuke cin arziqi tare da ita, ya kamata ku gyara, idan kuma ba haka ba zan samu hajiya na sanar da ita, in yaso ita sai tasan matakin da ya kamata ta ɗauka tunda mu duka zamanta mukeyi"
Haka Iya tayi masu tass sai bayan ta gama musu faɗan ta tambaye su meyayi saura a aikin.
"Dambun naman su Alhaji ne da babban yaya, daga nan sai abincin dare, shi kuma hajiya tace ba sai anyi ba, a barshi tunda yau aiki yayi yawa"
Kallon Maryamah, Iya tayi tace "Kin iya danbum nama?"
"Eh na iya"
"Bismillah inaga kiyi shi ga naman nan, akwai na rago da zakiyi ma Alhaji ƙarami dashi, sai kuma akwai na kaza wanda Alhaji za'ayi wa shi"
Amsawa tayi da toh ta nemi turmi ta tambaya dakawa za'ayi.
Ayi na dakan yafi daɗi iya tabata amsa.
Zama tayi ta ware tsokar duk ta cireta daga jikin ƙashin kasancewan an dafa shi ya dahu luguf, dakan ma bata sha wahala ba, dan daman ya dagargaje, Kayan miya ta jajjaga tarugu da tattasai, sai ta yanka albasa wadatacciya, ta daka kayan ƙamshi su citta da su kanun fari, haka ta ware sauran spices ɗin suma da duk abinda zata buƙata.
Iya ta kalla tace "iya wane kalan suya za'ayi, na cikin mai ko wanda ake sanya mai kaɗan?”
"Wanne kike ganin zaifi a ciki?"
"Duk sunada kyau, amma na cikin mai yana ɗan jimawa ana amfani dashi, be lalace ba, matsalansa idan akayi in ba a tsane man jiki sosai ba saurin tayar da ulcer yakeyi"
"Inaga ayi suyan cikin man dan bama mu taɓa gwada shi ba, in yaso sai a tsane man sosai.”
Aikin ta fara cike da kuzari da ƙwarewa, kafin kace me gaba ɗaya kitchen ɗin ya baɗe da ƙamshi saboda spices da dambun naman yaji.
Sosai Iya ta dinga yabawa cike da tsokana tace "Kike cewa kina so ki koyi abincin ƴan gayu, bayan gashi nan ƙamshin abinda kikeyi yama disashe namu ƙamshi"
Murmushi tayi "Iya ai ina kan koya ne ban wani iyaba sosai"
Suna cikin magana ne, Zuhura ta shigo tana magana "iya yau me muka samu haka ne, duk ya baɗe mana hanci da ƙamshi? Turusss tayi ganin Maryamah gaban gas tanata aikin dambun nama, Kada dai cutie ce ke mana wannan horon, ba Iya ba"
Dariya Iya tayi aikam dai Maryamah ce.
Cikin sauri ta ƙarasa inda Maryamah ke tsame dambun daga cikin mai, "Like seriously, cutie kece kikayi wannan aikin? Jira ma dai waike, komai kin iya tayi mata tambayar with full of suprise.
Murmushi tayi "A'a fah, yanzun nan na koya wajen Iya"
Iya tace "Kidai faɗi gaskiya"
Plate Zuhura ta ɗauka zata zuba dambun naman dan miyanta duk ya gama tsinkewa.
Maryamah ce ta katse mata hanzari "ai sai an tsaneshi idan ba haka ba maiko bazai bari kiji daɗin ci ba"
"Eh kuma fah haka ne, buh lemme test small" Ta ɗiba tana kaiwa baki.
Lumshe ido tayi tana bada sound din hmmn, tana girgiza kai irin na wanda daɗi ya kaimawa "Hmmn what a yummy and delicious dambun nama" fito da harshen ta tayi tana lashe gefen lips nata inda ya ɗan zuba.
Murmushi Iya tayi "Babyn mamy kodai a sanya miki waigi ne?"
"Allah Iya ban taɓacin dambun nama mai daɗin wannan ba, upon all the danbum nama I ever ate in mah entire life"
Rarraba ido iya ta fara can tace "kedai kika san me kikace, ni kinsan ba gane wannan Yaren nake ba, amma ni kaina tun kafin naci ganin yanda take haɗashi nasan zaiyi dadi kam"
"Aikam ya masifar yi wallahi iya kici kiji"
Ita dai Maryamah tana gefe tana jinsu, kuma ko banza taji daɗin yanda suka yabi ƙoƙarin ta, tissue ta ɗauka irin na cikin kwallin nan, ta zuba ma Zuhura akai. Bayan ta ɗora shi a kan plate tace "gashi tissue ɗin ma zai ƙara taimakawa wurin rage maiƙon jiki"
Godiya Zuhura ta mata ta fita tana ci.
Zuhura na zuwa parlour dashi aunty Amnah tace "Wow, wannan danbum yayi kyau sosai a ido, make am test am"
Zuhura na dariya tace "Saima kinci zaki tabbatar wallahi cutie ce tayi shi"
Su Fadil da suke wasa da babyn aunty Amnah, jin ance cutie tayi, sukace zasuci suma.
Nan fa Zuhura tace, bazasu cinye mata ba, suje kitchen ɗin su anso mana.
Aunty Amnah ma da taci taji How sweet it is, sai cewa tayi itama bari taje ta zubo.
Mamy dake gefe tace "kunsan fah na daddy kune da yayanku"
Haɗa baki suka yi wajen cewa mamy please"
Allah ya bada sa'a daga haka ta tsuke bakin ta.
Kitchen aunty Amnah ta wuce "Cutie wato abun yar wariyar launin fata ne koh? Shine kika ware Zuhura, kika bata, kika hanamu?"
Bakinta ta rufe da hannu "Laaa aunty Allah a'a, itama yanzun ta shigo ta gani, shine tace tana so fah ta ɗiba"
"Ai kin kyauta"
"Afuwan aunty, bari a sanya miki naki"
Sai gasu Fadil da gudu suna "Cutie zamuci please"
Sahura da dije kam sakin baki sukai suna kallon ikon Allah, wato haka yarinyar nan ta samu shiga dai a gurin yan gidan har wani suna suke kiranta da shi.
Sahura tace "Hmmn, dole mu zauna dan bazai yiwu ba wallahi"
Ko ta kansu aunty bata biba Iya kawai tayi ma sannu da aiki saboda ita dai samm yaran basu mata ba.
Plates ta nema, duk ta zuba masu, ta hada masu da fork.
Thanks suka ce mata suna fita daga kitchen ɗin.
Sahura data kasa haƙuri tace "yau muna ganin iyayi ke baiwar Allah daga zuwa sai ki zaƙe kibi ki shige ma yan gida, to wallahi masu kuɗi dai ba'ayi mausu shishshigi aikin banza kawai"