← Book details Rantsatstsen Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 19

Sashe 16

Rantsatstsen Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wow cutie so you're that cute idan kikayi smiling but why are you always frowning your face kina rage kyau Allah be smiling always"

Murmushi mai faɗi tayi a ranta tana jinjina halin Zuhura dan Allah ji yanda ta saki jiki da ita kamar ba me aiki da wanda ake ma aiki ba, bata bata amsa ba tace "yanzun dai mamy tace kada ki tsareni da surutu dan haka muyi aikin mu" tayi maganar with a wide smile on her face.

Zaro ido Zuhura tayi "cutie kema haka zaki ce"
"a'a yi haƙuri zoki nuna min inda zan fara dashi"

Parlour ne mai matsaƙaicin girma amma yayi matuƙar ƙayatuwa da tsaruwa fentin da cushions din dake ciki har curtains ɗin duka off white ne daga ganin yanayin tsaruwar wurin zaka san mamallakin gurin mai tsananin tsaff ta ne kuma ɗan gayu, dan komi a tsare yake kamar ɗakin mace ba wani tarkace ko hayaniya daga gefe akwai wani ɗan corridor wanda kana bin gurin zaka ga 2 bedrooms, a parlour ɗin kuma akwai ƙofa guda biyu ɗaya ɗan ƙaramin kitchen ne da ke ɗauke da jerin kayan tea kala daban daban da na coffee, ga kuma coffee maker a gefe sai standing gas cooker mai 4. Akwai wani dish drainer na company roveger wanda ke ɗauke da plates da cups masu kyau sosai.........

FULANI
08082101373

https://chat.whatsapp.com/DysmUMWo6dYJlLWGBPOMEI?mode=gi_t

https://chat.whatsapp.com/DysmUMWo6dYJlLWGBPOMEI?mode=gi_t

✨🦋 RANTSATSTSEN RABO ✨🦋

BY RABIA'TU KABIRU ACHADU (FULANI)

YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION YOTA

SADAUKARWA GARE KI HALIMA HASHEEM (MIEMIEN HABIBI)❤️& AHMAD JAMIL AHMAD (HABIBI)♥️

FULANI ❣️
08082101373

🦋✨ RANTSATSTSEN RABO ✨ 🦋

PAGE 1️⃣8️⃣

Kitchen ɗin ta gyara tsaf, ta wanke cups ɗin da plates, har dish drainer ɗin sai da ta wanke sannan ta sake jerasu gwanin ban sha'awa, bayan ta share ko'ina tayi mopping sosai, komai tana yi da taka-tsantsan kada taje tayi ba daidai ba yazo yace a nemo ta, yayi punishing nata, tsaf ta gyara kitchen ɗin ya ɗauki ƙyalli, kalla tayi sosai a ranta tace, ita dai tasan duk yadda ya kai ga son liƙa ma mutane laifi, nan dai ya fita.

Bata gama tunanin ba, Zuhura ta shigo, ganin yadda ta gyara kitchen ɗin sai kyalli yake, tace "wow cutie where did you learn all this?"

Murmushi ta mata "ba ko ina"
Haka suka fito Zuhura na zuzuta yadda gyaran kitchen ɗin yayi kyau duk masifan tsaftanyaya nasan dole zaiyi shiru wannan karan.

Koda suka zo parlour itama Maryamah tace, "to ai aikin da kikayi ne ma abin ya yabawa, wallahi kin yi ƙoƙari sosai sannu da aiki"

Murmushi tayi "Allah yasa yayi ma yaya kam"
"Ah haba nasan ma zaiyi mishi"

"Hmmmm ba kisan waye yaya ba shiyasa kiyi shiru kawai"

Haka suka nufi bedroom ɗin suna buɗewa wani sassanyan ƙamshi ya bugi hancinta, dan ita kam, Zuhura she's used to it, ɗan lumshe ido tayi, amma wannan karan batace komi ba.

Kallonta Zuhura tayi "ba kice komai ba, ko nan beyi miki ba?" Murmushi tayi "yayi sosai wallahi, kamar ɗakin mace"

Wani makeken Italian bed ne wanda ya mamaye rabin ɗakin, daga gefe kuma closet ɗin shine ya cinye gaba ɗaya bango, sai kuma wani guri da taga yayi kamar corridor—wai ashe prayer corner ne, gaba ɗaya tsarin ɗakin nashi yayi mata, banda sassanyan ƙamshi da take ji har cikin ƙashi da ɓargonta.

Ɗakin beyi wani datti ba yar kura ce ta an kwana biyu ba a shiga ba, ta faɗa ma Zuhura. Ita kuma tace "kinsan bai cika zama ba da yake yana ɗan taɓa business duk da ba wani sosai ba, dan yafi son aikin shi akan business ɗin, kinsan babban likitan jijiya ne da ake ji dashi a Nigeria, Neurosurgeon ne, and he's one of the best Neurosurgeon here in nigeria"
Allah sarki, Maryamah tace, duk da ita bata son taji ance mutum likita ne, don gani take duk likita ɗan iska ne and he's exposed to mata shiya saka ita aikin samm be mata ba.

Ɗakin suka fara gyarawa, bedsheet ɗin suka canja, suka ɗauko wani fine white bedsheet mai laushin gaske suka shimfiɗa, irin mai haɗe da duvet cover ɗin nan ne, suka sanya bedsheet ɗin, sai suka maida duvet cover ɗin suka ɗora, amma shi sai sukayi folding nashi into half of the bed, haka suka yi arranging mashi 4 pillows, a ranta tace kome yake da pillows har 4 a gado oho.

Bayan sun yi tidying room ɗin yayi kyau sosai, suka kunna burner suka sanya turaren wuta, mixing Maryamah tace suyi dan taga cupboard da yake ɗauke da varieties na turaren wuta a ɗakin, and different brands, duk ba irin na ƙasan nan bane—irin na su companyn Al-haramain ne da Naseem, gasu nan dai kala-kala, shine tace ma Zuhura su gwada mixing kala huɗu suji wane kalan kamshi zai bada, hakan sukayi, and alhamdulillah ya basu feedback mai kyau kam, dan wani daɗaɗɗan kamshi ya bada wanda mutum zai kasa gane wane kala ne.

Mirror ɗin shi suka je suka gyara, amaki ya kusan kashe Maryamah taga abu kamar an buɗe kamfanin turare, gasu nan kala-kala irin masu muggan tsada ɗin nan, Itama saima ta rasa bakin magana, taga duk yadda takai ga son ƙamshi akwai wanda ya takata a nan kenan, saima ta fara tunanin duk wannan turaren, to shi basa saka shi mura.

Haka suka gyara gurin tsaf sukayi rearranging mashi kayan dake kan badubi gwanin ban sha'awa, toilet ne kawai ya rage masu, nan fa Zuhura ta noƙe tace Maryamah ta shiga ta gyara, kada taje tayi yazo yace tayi mishi ba dai-dai ba.

Haka itama Maryamah ta shiga tana ɗar-ɗar, toshi wannan wane irin mutum ne wanda komai za'a mishi ba a burgeshi, haka ta fara wanke shi a natse, tanayi tana kaffa-kaffa. Ita dai fatanta ta gama lafiya, dan wallahi in ta mishi ɓarna gara ta bar gidan, wata zuciya tace, to in kin bar gidan kije ina? Ina kika sani a Abuja?.

Tana ciki tana wanki, ita kuma Zuhura na bedroom ɗin tana ta faman ɗaukan hoto da videos, gaban mirror nashi tana videos irin mirror view ɗin nan.

Tana cikin yi taji an banko ƙofar, an shigo "uban waye ya buɗe part ɗin nan?"

Sanin ko suwaye suke shigowa yasa bata ko ɗago kai ta kallesu ba, ba kowa bace face Nadiya, ɗiyar kanwar mom wadda ake ta so a likawa yayansu, sai yar korenta Husnah, ɗiyar mom wadda suke kusan age mate da Zuhura amma ta bama Zuhura 3 months.

Ko kallon inda suke batayi ba, ta cigaba da videos nata.

Gabanta Nadiya tazo "you idiot, ba dake nake ba, bakiji nace uban me kikeyi a ɗakin mijina ba?"
Wani sakaran kallo Zuhura ta mata "au haba ashe ɗakin mijinki ne? Sorry ai bansan an ɗaura auren naku ba, ko kuma may be dan ba'ayi mana shelar hakan bane oho"

Sakare Nadiya tayi tana binta da kallo, tana jinjina rainin wayon yarinyar, ta daɗe da gane cewa yarinyar ta raina ta, sam bata ganin girmanta, koda ba ita yayanta zai aura ba, ai ta girme mata nesa ba kusa ba.

Matsowa Husnah tayi gaban ta "to uwar rashin kunya ai ko baki girmama ta dan komai ba, kin girmamata dan kasancewar ta wadda yayanki zai aura"

Banzan kallo ta aika mata "au Allah? To ai sai ku jira a ɗaura, bawai ta dinga faman zarya a tsakanin gidan iyayenta da gidan nashi iyayen ba, kai jama’a, su balama dai anyi asarar kunnuwa" tayi maganar tana ƙunshe dariya.

Zaburowa Nadiya tayi cikin hargowwa "ke ƙaramar mara kunya ni kike zagi?"

Hayaniyar su ce ta fito da Maryamah, wadda already ta riga ta gama, ta ringa jiyo hayaniya sama-sama kamar faɗa ake yi, shine ta fito taga Zuhura ita da wa kuma?

Daidai lokacin da Nadiya ta matso kusa da Zuhura ta ɗaga hannu da niyyar kai mata mari kenan, Maryamah ta fito gaba ɗaya.

Kallon juna sukayi ita da Nadiya da idanuwan su suka faɗa cikin na juna wanda a take gabansu suka ji ya mugun faɗuwa.

Maƙalewa hannun nata yayi, ita bata kai shi ga fuskar Zuhura ba kuma bata sauke ba, sosai gabanta ke dokawa, ta aje idonta ƙyam akan Maryamah.

Wanda itama Maryaman a nata ɓangaren hakan ce ta kasance, idonta cikin na Nadiyan take mata kallon tsakiyar ido.

Juyawa gurin da Husnah ke tsaye tayi, ta kalle ta tace "who is she?" Ta faɗi tana maida kallonta ga Maryamah.

Husnah ta kalleta a wulaƙance "maid i guess" ta bata amsa in a disgusting tone.

"Maid?"ta ƙara tambaya cike da rashin fahimta.

"Eh the new maid" ta ƙara bata amsa tana banka ma Maryamahn harara, saboda itama kanta sai yau ta ƙara kallon ta ta gane ma idonta kyaun da su Adeel suketa faɗin tanada shi, ashe ta ma fi yadda suke faɗi ɗin a fili, haka kawai itama taji batayi mata ba.

Wata uwar tsawa Nadiya ta buga "and what the hell is she doing in my spouse room?" Dan gaba ɗaya yadda taga yarinyar ta firgitata don kyau da diri kam tabbas akwai su a gurin, a haka ma dan bata gama cika shekarun yammatancin ta ba, sosai taji tsanar yarinyar da wani mugun kishinta, saboda yarinyar ta haɗa komai da ake buƙata na mace ga wani sassanyan kyau mai fusgan mutane gareta.

"Point of correction your fiance dai ko?" cewar Zuhura, bata jira cewar taba ta ɗora "tunda ai ba'a riga an ɗaura ba, abinda kuma takeyi a nan shine gyara ɗakin shi wanda kike kira mijin naki, domin nasan in ke aka bari da gyaran ba iyawa za kiyi ba" ta bata amsa hankalinta kwance.....

FULANI
08082101373

https://chat.whatsapp.com/DysmUMWo6dYJlLWGBPOMEI?mode=gi_t
https://chat.whatsapp.com/JHxZP3j1IIr6O5UZj4Csq5?mode=gi_t

✨🦋 RANTSATTSEN RABO 🦋✨

BY RABIA'TU KABIRU ACHADU (FULANI)

YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION YOTA

SADAUKARWA GARE KI HALIMA HASHEEM (MIEMIEN HABIBI)❤️ & AHMAD JAMIL AHMAD (HABIBI)♥️

FULANI ❣️
08082101373

✨🦋 RANTSATTSEN RABO ✨🦋

PAGE 1️⃣9️⃣

Kauda tunanin ta tayi a ranta, ganin tuna ta ma ƙara ɓata mata rai yake bata san dalili ba, amma ita kam zata iya cewa bata taɓa jin irin wannan ƙin wata halitta a rayuwanta ba, gani take gaba ɗaya ma bata da mamora.
Chapter 16 · 0% Book details