← Book details Rantsatstsen Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 19

Sashe 19

Rantsatstsen Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Bayan ta gama wannan, ta yanka sauran fruit ɗin, tayi fruit salad ta sanya condensed milk bata juya ba, kawai ta kaishi fridge. A haka tace, in sunzo sai a sanya powdered milk sai a juya gaba daya.

Iya ta tambaya ko akwai aya, tace eh, baza a rasa ba. Tace to ta bata. Iya batama tsaya tanbayan ta ba, tunda taga aikin da tayi, ba tare da ance ga ainayin abinda ake so tayi ba, amma tayi shi daidai koma ace fiye da yanda ake buƙata, shiyasa kawai ta yarda da koma me zatayi to shima zaiyi amfani.

Bata ayar tayi, tace ko akwai sauran abinda kike so, tace eh, in akwai dabino, ina so, tunda naga ga kwakwa nan. Iya tace akwai sosai, kam ta nuna mata cupboard ɗin da ake ajiye dabino. Shima ɗiba tayi, yanda zai isheta ta jikashi kafin ta gama gyaran, ayan tasan ya danyi taushi.

Surfa ayan tayi, sama sama ta wanke, ta rage, sai ta barta cikin ruwan. Ta koma kan dabino, shima ta wanke, ta bare ta cire kwallayen, haɗashi tayi da ayar ta ɗauki kwakwar duk ta zuba tayi blending nasu, ta tace ruwan kuma ta kawo flavour na aya amma na ruwa ta zuba, ta sanya peak milk, ta ruwa ta kawo condensed milk, ƴar daidai, ta haɗa ta juya, ɗanɗanawa tayi, taji zaƙin ya mata, duk da ba wani cika son zaƙi tayi ba sosai.

Iya ta kalla dake naga aikin itama cike da girmamawa tace "dan Allah kisha kiji zaƙin yayi kuwa, ni bana ganewa tunda ba son shi nake ba"

Sha tayi kaman yanda ta buƙata "Uhmmn uhmm charkwaɗi ɗiyar nan, yo ai kin iya hidimar kitchen, kikace kina so ki koya, ni ban ma taɓa ganin kunun aya irin haka ba wallahi yayi masifar daɗi, yau kam ai kin sallami Alhaji ƙarami"

Murmushi tayi kawai ba tare da tace komai ba, wani glass jug Iya ta bata mai girma da faɗi ta zuba a ciki, sai da ta cikashi taff shima ta kaishi fridge tana cewa in mukaji shigowar su sai a fasa kankara a zuba a cikin su duka.

"Hakan yayu ba laifi sannu da ƙoƙari kinji Allah yayi albarka"

Amin ta amsa cike da jin daɗin albarkar da iyan ke yawa saka mata.

Hanyae fita tayi Iya ta dakatar da ita "waɗan nan sauran da kika bari kuma fah, naga duk sai da kika rage saura"

"Naku ne keda su" tayi maganar ta fuska ba walwala, dan ji take ta gama sakar masu fuska kenan har abada.

"Dawo ki ɗibi naki sai kibar mana sauran"
Kai ta girgiza tun kafin ma iyan ta ƙarasa "Naƙoshi Iya kawai kuyi amfani dashi"

"Ai baza ayi haka ba taya zakayi abu kice kuma ke bazakaci ba, jiya ma ina gani dambun naman da kikayi baki kai ko ɗaya bakinki ba, Kuma da kika gama namu kawai kika bari, kikayi packaging sauran, sai da dare da na faɗa ma hajiya, shine ta bada naki, gashi can ki zo ki ɗibi waɗannan abubuwan, sai ki hada dashi, ai haƙƙin ki ne"

Bata son yawan musu shi ya sa ta dawo kawai ta ɗibi kaɗan tace ya isheta ta gode.

★★★★

Ɗaki ta shiga ta aje kayan a kan bedside drawer, ta wuce toilet alwala tayi tana fitowa ta tada sallah, dan already azahar tayi saboda 1 ma ta ɗan gota, tana raka'ar ƙarshe taji diran motoci a gidan, koda ta idar bata tashi daga inda take ba, tunda taga ta gama abinda duk ya kamata ace tayi, gashi ranta a ɓace yake na abinda yafaru tsakaninta dasu Sahura, bata taba sanya lamarinsu a kai ba saboda bata da lokacin su, amma indai suka kara sanya babanta a haukan su, zata tabbatar masu da shayi ruwa ne tayi kwafa.

Ƙarfe 2 da ƴan mintuna duk suka hallara a parlourn daddy bayan sunyi wanka sun canja kaya, waya mamy ta ɗauka ta kira iya tace su zo su kawo kayan abincin babban parlourn daddy.

Tana nan ciki Iya ta shigo da saurinta tana "Tashi maza Maryamah muje mu jera kayan abinci a sashen Alhaji, daga nan muyi masu sannu da zuwa"

Dummm!!! taji gabanta ya faɗi dan ita Allah ya sani bata shirya haɗuwa da sauran yan gidan ba uwa uba, kuma wannan yayan nasu batasan dalili ba, amma tanajin shakkar haɗuwa dashi.

Ɗago kai tayi batasan ta ɓata fuska ba tayi magana a narke "Iya yanzun nima sai naje" tura ɗan karamin lips dinta gaba tayi wanda hakan ya zamar mata daɓi'a a duk lokacin da takejin shagwaɓa, Ita tama manta da Iya take magana.

"Yau kuma shagwaɓa za ama iya ai"

tanajin haka, sai kuma taji kunya tayi ƙasa da kai tana miƙewa.

Kitchen ɗin tabi Iya sukaje, Iya ta nuna mata katon tray da ake dauke da plate da spoons tace ta dauka, suje yayinda ita kuma Iya ta ɗauki wasu tsadaddun food warmers masu kyan gaske, suma su sahura duk sun dauka, wasu warmers din suka fita dasu suka nufi part ɗin Alhaji kasancewar a can za su zauna gaba ɗaya a ci abincin.

Bata san dalili ba amma gabanta mugun faɗuwa yake, dauriya kawai take suna zuwa zasu shiga parlourn, suka samu iyayen takalma gasu nan designers na different companies, amma duk da haka akwai wani d6aya da kyan shi ya fita daban, a kuma inda aka aje, shima daban ne, dan yana daga gefe palm slippers ne irin na maza, Kaɗan ta kalle shi ta ɗauke kanta, suka kutsa kai bakin su ɗauke da sallama....

Gobe kam ayi ɗiyar baba achadu haƙuri babu update🙌

FULANI
08082101373

https://chat.whatsapp.com/JHxZP3j1IIr6O5UZj4Csq5?mode=gi_t
Chapter 19 · 0% Book details