← Book details Rantsatstsen Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 19

Sashe 3

Rantsatstsen Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan ta idar da sallah ta zauna, tayi azkhar ɗin ta na mairaice, wanda daman a dai-dai wannan lokacin take yin shi, In ta samu sarari, tayi bitar karatun ta, in kuma bata samu ba sai tayi uzirin da ya taso mata, to yau ma dai, bayan data kammala azkhar ɗin, tashi tayi ta fita kitchen, taje ta duba miyan da ke ta faman tafasa, gidan sai ƙamshin daddawa yakeyi.

Bayan fitar ta ne tace ma Zainab tayi sallah, ta amsa mata da eh. Tace Muktar fa ta ƙara tambayar yarinyar, amsa ta bata da bai dawo daga masallaci ba.
Da haka ta kaɗa miyan, ta sauke ta gyara wurin, Bayan ta gama komai, ta ɗauki na Hajja ta mika mata ɗaki wadda ta sameta tana jan carbi irin jan da zaka rasa, wai mema ake karantawa, Nan ma sosai tayi mamaki yau da Hajja bata hantareta ba har ta aje mata ta fito, ta leka ɗakin Baba tace, “Ta gama itama wai yau har da mata sannu da faɗin tadai zuba nata koh?” Ai fa, na mamaki da tsoron Allah suka taru, suka mata rubdugu, a ranta take Anya yau gidan nan lafiyan mutanen cikinshi kuwa? Aje tunanin komi tayi a gefe, taje ta zuba ma yaran tace, “Su wanke hannu, su kuma tabbatar sunyi Bismillah kafin su faraci.” Sannan ta ɗauki nata tayi ɗaki.

★★★

Bayan an idar da sallar Isha ne, su Malam suka nufo ƙofar gidan malam sale suka zauna a shimfiɗar shi.

Malam Sale ya karasa cikin gida yace, “A ba yaro ya miko mishi abinci da ruwa yana tare da malam Jafaru ne" daga haka ya fita ya koma wurin shi.

Yace, “To Malam, mu bari mu ci abinci ko?” Cikin sauri Malam Jafaru yace, “Malam Sale, abun da ke tafe dani wallahi, ko nace maka zanci abinci yau to ina mai tabbatar maka da cewa, ko abakina ba zai wuce ba” Malam Sale yace,

“Subhanallah Malam Jafaru, wannan wane gagarumin tashin hankali ne kuwa?”

Malam Jafaru yace, “Malam Sale ina cikin wani mummunan tashin hankali da masifa, bansam dame zan kira abun ba a taƙaice, Wato malam yau na tashi da mura, haka nan na daure na tafi wurin nema da yammanan sai na ji jikin na neman gagarata, sai na tatatra na taho gida, ashe rabon in ji tuggun da ake shirin haɗa ma marainiyar Allah ne amanar da aka mutu aka bar mun”

Nan ya kwashe duk abunda yaji su Hajja da baba suna shirin aikata wa Maryamah.
A take shima yaji hankalin shi yayi masifar tashi.

Faɗi yake Malam, “Wane zamani muke cikin dan Allah? Miyasa son zuciya yayi yawa a cikin al’ummah? Kai, innalillahi wa inna ilaihi raji’un., Allah kayi mana maganin musiba ta fili data ɓoye, Yanzu ita Hajja wai har yau bata cire qiyayyar baiwar Allah nan a ranta ba, wadda tundaga zamanta har mutuwarta ba zata ce ga abunda tayi mata ba”

"Allah shi kyauta eh lallai kana cikin tashin hankali mai tsananin gaske, Kamayi kokari, wallahi Allah ya kawo mana mafita ta alkhairi”

Malam yace, “Ameen.” Shiru sukayi su duka, kowwa na nazari. Zuwa can Malam Sale yace,

“To yanzu wane mataki kake ganin zaka ɗauka?”

Shiru Malam Jafaru yayi sai zuwa can ya dago yace, “Malam Sale, gaba daya kaina ya kulle, na rasa wane kalar tunani zanyi, Allah ya sani, ina son yarinyata tayi karatu mai zurfi, ban san daɗin boko ba, mahaifiyarta bata san daɗin shi ba, Amma tunda ta samu cikin nan ta kwallafa rai akan abunda ke cikinta, inshaa Allah zai yi karatu mai zurfi ko Allah zai taimake ta sanadin karatun shi ya shiga har inda zai sadata da danginta, to ashe ko fuskar abunda zata haifa ɗin Allah ma bazai bata ikon gani ba” ya ƙarasa maganar cike da karyewar zuciya yana share hawaye.

Haka ne inji Malam Sale domin ya rasa, mema zaice wa aminin nashi.

Chan dai ya nisa yace “To yanzu ya kake ganin za a yi? Ni da inada babban yaro wallahi, da na aura Maryamah shi, ko dan a samu a cire yarinyan nan daga wannan ƙangin rayuwaer da take ciki, To amma yarona babba ma ita kanta Maryamah ta girme shi”

"Hakane" Malam Jafaru ya fadi yana duƙar da kanshi ƙasa.

Shiru ne ya biyo baya, sai zuwa can Malam Sale ya ɗago ya kalli Malam Jafaru yace,

“Malam, ga wata shawara, amma ban san ko zarayi maka ba????

FULANI
08082101373
https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr?mode=gi_t

https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr?mode=gi_t

🦋✨ RANTSATSTSEN RABO 🦋✨

BY RABI'ATU KABIR ACHADU (FULANI)

YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION YOTA

SADAUKARWA GARE HALIMA HASHEEM(MIEMIEN HABIBI)❤️& AHMAD JAMIL AHMAD(HABIBI) ♥️

FULANI ❣️
08082101373

✨🦋 RANTSATSTSEN RABO 🦋 ✨

RAGE 4️⃣

Cike da zumuɗi, malam Jafaru ya ɗago yana faɗin “Ah haba malam ni da daman neman shawaran ne ya kawoni gareka, ai kawai ka faɗamin i insha Allah zan yi aiki da ita nasan bazata cutar da maryamah ba”

Shiru malam Sale yayi na ƴan sakonni, zuwa can yace, “To malam Jafaru shawarar dai tawa ba wata bace illa ina Alhaji Muhammadu da muke har kar kasuwancin dabbobi dashi, wanda nake kaima dabbobin kiwo yake ajesu a gidan gonar shi dake can Habuje?" Kallon shi yana jiran amsar tambaya dayayi masa idan ya gane wanda yake magana akai.

“Eh! na’am nagane shi dai Alhajin dake baka zakka duk shekara, koh?” shima ya mayar mishi da tambayar shi.

"Yauwa shifa"
Bai jira cewar shi ba ya ɗora mishi da bayani.

“Toh me ɗakin shi ta biyu zuwan da nayi, take ce mani dan Allah in cigita mata yarinya da zata ringa kama masu aikin gida, kasancewar wadda take masu yan aikace-aikacen aure zatayi, su kuma basu cika son tarkacen yan aiki ba, shine tace dan Allah in nemo mata wadda na yaba da hankalinta, Allah ya sani inda ace Halilu mace ne wallahi zan bata saboda nasan ɗiyata bazata taɓa wulakanta ba, kuma nasan zata samu kulawa dai-dai gwargwado. Inda ace uwargidan ce tace in nemo mata, Allah da a take zance mata babu, kuma bani da hanya, To kasancewar amaryar ce, kuma na yaba da haƙurin matar da yakanar ta, nace mata toh, gaskiya daman ɗiyar wajen ƙanwata nayi niyyar kai mata, dan har na yi magana da ita Hajaran nace mata zata bani gaje in kaita wurin aiki, kuma da ita da megidanta sun amince"

“Amma in kana ganin cewa zaka iya bada Maryamah, sai ince ma ita gajen ta zauna gaba. In an samu wata damar sai a kaita"

Shiru malam Jafaru yayi cikin tsannin baƙin ciki Allah ya sani, yana tsananin son ɗiyarsa domin itace sanyin idaniyar shi, kuma yasan malam sale bazai taɓa cutar dashi ko abinda ya haifa ba, yana ganin kamar gara ya bada ta, ta bar garin taje can inda su Hajjah da Zainu bazasu ganta ba, balle suyi tunanin cutar mishi da ita.

Shiru ne ya biyo baya kowa na nazari a cikin ranshi, zuwa can malam Sale yace, “Amma in kana ganin bazaka iya ba, sai a kai masu gajen ita kuma Maryamah, sai mu nemo wata mafitar Amma dai a wannan gaɓar da muke ciki, tafiyar ta ina ganin kamar zaifi zama alheri, Kuma can inda zata, ina mai tabbatar maka da cewa wani me mugun nufi zaiyi wahalar samun daman yin kutse cikin wannan gidan saboda tsaro, domin sojoji ne ke tsaron unguwar gaba ɗaya, dama gidan kasancewar baban yaron gidan babban soja ne me babban muƙami, inshaa Allahu zata kasance cikin tsaro a can"

Nannauyar ajiyar zuciya, malam Jafaru ya sauke tare da fadin "Bakomai malam Sale na amince, gara ta tafi can din, hankalina zaifi kwanciya akan kasancewar ta a nan, koda yanzun ta tsallake wannan gaɓar, bansan kuma me zasu ce zasuyi mata ba nan gaba"

★★★★

A can ɓangare gidan su Maryamah haka tayi sallan isha, bayan ta idar ta taci abinci, ta fita ta qara jan ruwa a rijiya ta shiga wanka kasancewar ta da son wanka kamar ƙwaɗo, bayan tayi wanka ta shirya cikin wata koɗaɗɗiyar rigar bacci, ta dan shafa turare, taja littafinta, ta kunna torchlight tana bitar karatunta kasancewar gaf suke da fara JSCE exams dinsu, wanda taciwa buri sosai, so take taci daga nan ta jona SS tana fatan ta samu damar yin karatu mai zurfi, tuna hakan a cikin ranta ne yasa ta lumshe dara-daran idonta wanda suke da yalwar gargasa.

Tana nan kwance tana karatu, taji shigowan Hassu lokacin tara saura na dare, a ranta take ayyana yau da ɗan arziƙi an dawo da wuri, haka ta ringa jiyo kwarafniyar su da ita da uwar a tsakar gida, suna ƙirga kudin cinikin da sukayi da kuma wanda ta samu ƙari uwar nata shi, mata albarka cike da alfaharin kuɗin da ɗiyar tata take kawo mata bayan na tallar.

Aranta tace, “Allah dai ya kyauta.”

Shiru tayi tana tunanin, yau baba ko lafiya be dawo ba, kodai muran ce? Gashi ita ko yar rakani kashin nan bata da ita, balle ta kirashi taji lafiya.

★★★

Shi kam malam Jafaru yana can suna tattaunawa da malam Sale akan yadda tafiyan zai kasance da yaushe ya kamata suyi tafiyan ma.
Malam Sale ke ce mishi gaskiya, shi da abunda ya tsara sai nan da sati biyu yake so yayi tafiyan, amma tunda haka ta taso, bari ya kira Hajiyan yaji ya za ayi.

Nan malam Jafaru yace, “Eh, kirata dan Allah, dan ni wallahi kwana biyu ma in Maryamah ta kara a garin nan inajin jinina sai yayi hawanda da wahala ya sauka.”

Malam Sale yace “Subhanallah, kadaina faɗin haka abokina, inshaa Allah ba abinda zai sameta sai alkhairi"

“Allah ya tabbatar mana dashi.” ya amsa yana kallon shi ganin har ya danna kiran wayar.

Cikin ikon Allah, malam ya samu Hajiyan a waya, Bayan sun gaisa, yake ce mata daman maganar yarinyar an sameta, amma nida nace sai nan da sati biyu zan taho"

A take hajiyan tace, "Aa malam Sale nidai in dai yarinyan na da iyayenta sun shirya, ko gobe ko jibi ku taho zan ɗauki nauyin komi in Allah ya yarda"
Chapter 3 · 0% Book details