Sashe 5
Rantsatstsen Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kanta dake ƙasa ta ɗago tace "Baba to shikenan sai na haƙura da karatu, da shine burina?" Hawaye na ƙara cika idonta.
Murmushi yayi ya kalleta duk da bai kai zuci ba yace, "Yanzu zuciyar babanki haka za ki je gidan mutane kina masu shagwaɓa? Kin girma fa" Ya ƙarasa da murmushi mai faɗi. Ita ma murmushi ta yi tace, "Har abada ni yarinya ce a gaban farin cikina, ba zan taɓa girma ba idan ina tare da kai"
"A’a yanzu ma kin girma sannan maganar karatu, Insha Allah za ki yi har sai kin ce ya ishe ki"
Cikin sauri ta kalle shi "Da gaske babana"
Kanshi ya jinjina mata fuskarsa na yalwace da murmushi "Insha Allah"
"Allah ya cika mana burikanmu na alkhairi, ya yi mana zaɓin alkhairi baban maryamah"
“Ameen zinariyata, rayuwarki za ta cika da tarin albarka da ikon Allah, ki tashi kije ki kwanta dare yayi, kuma kada ki bari wani ya fuskanci cewa kina shirin balaguro, Insha Allah yadda suka so bamu mamaki, sai dai mumu basu da yardar Allah"
"Allah ya yarda babana, sai da safe"
Dariya ya yi yana girgiza kai, domin a duniya bai taɓa ganin abin da ya kasance abincin ruhinsa a jinsin ɗan Adam ba sama da wannan yarinyar.
★★★★
Ɗaki ta shiga zuciyarta fal da tunani, wai me baba yaji da ya rikice haka harya haƙura da ita yaga gara ta tafi wani wuri ta barshi, wurin da ita kanta ta san inda lafiya lafiya ne, to konan dacan ba zai bari ta je ba, tabbas biri yayi kama da mutum, sassaucin da ta gani a wajen mutanen gidan ba a banza ba, kwanciya tayi akan shimfidarta tana faɗin Allah Ya fisu, Addu’ar bacci ta yi ta kwanta da hannun dama, amma bacci ya gagari idonta, duk yanda taso bacci ya ɗauke ta abin ya gagara, juyi take tana tunanin can ɗin kuma wace irin rayuwa za ta je tayi Allah masani.
Ba ta san sanda bacci ya ɗauke ta ba, kiran sallar asuba na farko ya tashe ta, ta tashi ta ɗauro alwala, ta zo ta yi nafila tana zaune tana lazimi har aka yi kira na biyu, ta tashi ta yi raka’atan fajr, daga nan ta yi sallar asuba, ta yi azkhar, ba ta ma tsaya karatun Alƙur’ani ba, Ta fita ta hau share tsakar gida, tana cikin sharan ne baba ya shigo gidan da casbaha a hannu. Dukawa ta yi ta gaisheshi, duk da ba wani sakewa a tare da ita, ya amsa yana ƙara bata haƙuri a hankali don kada mutanen gidan su ji. Tace, "Baba ka daina dan Allah" tana dan turo baki. Ya yi murmushi yace,
"Na bari zinariya" Ita ma murmushi ta yi ta ci gaba da sharan, shi kuma ya kama hanyar ɗakin Hajja domin ya san har yanzu ba ta tashi ba, aikuwa yana zuwa ya sameta tana jan minshari, kanshi ya girgiza ya ƙarasa gareta yana ɗan taɓa ta tare da kiran sunan ta, "Hajja"
Da ƙyar ta buɗe idonta tace, "Lafiya za a zo a hanani bacci?" kauda kai yayi yana jin rashin daɗin ɗabi’ar mahaifiyar tashi yace, "Hajja gari fa ya yi haske"
“"o sai akayi me? mezan wa wani?" "Hajja sallah mana" cike da ƙosawa tace "To naji tashi ka bani wuri ai zanyi"
Haka ya mike jikinshi ba ƙwari ya nufi ƙofa, bayan ya fito ya tsaya yana tambayar Maryamah ko za ta je makaranta yau. Tace ba ta tunanin zuwa. Yace, "A’a ya kamata ki je daga nan kiyi musu sallama"
Kanta ta gyaɗa mishi. Yace ta shirya ta zo ta amsa kuɗin abin hawa.
Ci gaba tayi da aikinta, bayan ta gama sharan gida ta haɗa wuta ta ɗora ruwan koko, rijiya ta nufa ta ja ruwa ta wanke kewaye, sanda ta gama ruwan kokon ya tafasa ta dama, ta maida na wankanta. 7:20 ta fito cikin shirin tafiya makaranta, a lokacin baba Zainu ta fito za ta yi alwala. Kallonta kawai ta yi ta ɗauke kai, yau yan miskilanci ne a kai, ba ta tunanin ko gaisuwa za ta samu. Ta nufi ɗakin mahaifinta da sallama ta shiga tace, "Baba na shirya"
300 ya ɗakko ya bata yace tayi abin hawa da kudin breakfast, godiya tayi mishi ta fita, bayan ta fito ta ga Zainab zaune a bakin ƙofa, alamar tashinta ke nan. Ta kalleta tace, Sai yanzu kika tashi?" Ba ta amsa ba saboda tsoron addarsu. Kawar da kai ta yi tana taɓa baki tace, "Ku hanzarta ku shirya ku wuce makaranta" Tace, "Toh"
Daga nan itama ta fice daga gidan.
A hanya suka haɗu da Aisha, kasancewar makaranta ɗaya suke. Gaisawa suka yi, daga nan Maryamah ba ta ƙara tankata ba, ganin haka yasa Aisha ta san kila tana cikin bacin rai, domin duk miskilancin Maryamah da ake faɗa ita ba ta mata, Bayan isarsu makaranta suka ci gaba da ɗaukar darasi, A lokacin break ne Aisha ta kasa haƙuri tace "Nikam Maryamah yau lafiyarki kuwa?"
Kaman me jiran jin hakan take hawaye ya tsinke mata.....
FULANI
08082101373
https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr?mode=gi_t

✨🦋 RANTSATSTSEN RABO 🦋 ✨
BY RABIA'TU KABIRU ACHADU (FULANI)
YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION YOTA
SADAUKARWA GAREKI HALIMA HASHEEM 🙌🏻 TARE DA KAI HABIBI NA AHMAD JAMIL AHMAD ♥️
FULANI ❣️
08082101373
✨🦋 RANTSATSTSEN RABO ✨ 🦋
PAGE 6️⃣
Cikin kuka tace mata "Aisha wai aikatau babana ya amince naje wani gari"
Dafe ƙirji Aisha ta yi idanuwan ta duka a waje tace "na shiga uku aikatau kuma maryamah? baban dai kuma da kansa? Anya kuwa?" Gaba ɗaya ita dai ta kasa yarda
Cikin sanyin murya ta bata amsa "wallahi Aisha baba da kansa, amma yace min dalili mai girma ne ya sa zai haƙura ya barni tafiya, saboda tafiyata ita ce alkhairi a garemu ni da shi"
Yanzu maryamah yace baya fatan ki ƙara ko kwana uku a garin nan saboda tsoron abin da zai biyo baya"
“Bansan meyaji ba, amma tabbas jikina ya bani ƙila labarin wani tuggun suke haɗa min wanda yaji har ya ɗaga hankalinsa, Allah ne ya kawo shi har ya ji, shine dalilin da yasa ya samu baba Malam Sale da maganar, ya ba shi shawarar ya tafi dani wurin matar ubangidansa"
Ita kanta Aisha hawaye take ɗaukewa da yatsunta cikin muryar kukan itama ta bata amsa "Amma kwata-kwata ba Allah a zukatan mutanen nan, Insha Allah mugun nufinsu sai dai ya koma kansu, ni kaina sahiba tun da na ji wannan magana na gagara ki tafi, in Allah ya yarda rayuwarki za ta canja a can, sai sunji daman ace basu kitsa miki mugun abuba, da ikon Allah da baƙin cikinki zasu mutu ƴan wahala" Ta faɗi hakan tana ƙara kumbura, kasancewarta ita ma mafaɗaciya ce kamar ƙawarta, duk da ita ƙawar cikin ruwan sanyi take faɗa, amma maganar zafi take sosai.
"Hakane sahiba nima danaji haka nace wa babana gara na tafi, sai dai zan yi kewarku" tana faɗar hakan hawaye na ƙara zubowa a kuncinta.
Ƴar dariya Aisha ta yi tana share hawayen fuskarta tace "Mene ne yar shagwaɓan babanta?"
Dukan wasa ta kai mata tana cewa, "Duk fa na kewanku ne" share hawayen fuskarta tayi itama.
Bayan sun dan natsu, Aisha ta kalleta "Toh yanzu yaushe za ki tafi?"
"Gobe school ce nazo mu yi sallama da sauran yan class"
"Others like Uncle Muhammad?" A'isha ta tambaye ta tana dariya.
Ɓata rai Maryamah ta yi tana shan kunu tace "Ke kika sanshi, but me I know his existence?" Ta mayar mata da tambayar ta tana taɓe baki
"Really?" Aisha ta faɗa tana dariya.
Ita ma Maryamah murmushi ta yi tace, "Yeah" Daga nan sauran yan class suka dawo, aka ci gaba da karatu har aka tashi, da aka tashi ne Aisha ta yi saurin cewa yan class ɗinsu, "Dan Allah kada ku fita, Maryamah tazo yi mana sallama ne saboda zata koma gun dangin mamanta da zama"
Da mugun sauri Maryamah ta ɗago ta kalli Aisha, ita kuma ta kashe mata ido ɗaya tana murmushi tare da ɗaga mata kai alamar eh haka za a ce. Murmushi Maryamah ta yi ta girgiza kai ƙasa-ƙasa tace, "Allah ya shirya minke sahiba ki daina ƙarya" Da haka taje gaban class ɗin tana cewa, "Eh, kamar yadda kuka ji, gobe Insha Allah zan bar garin nan, dalilin ma da yasa nazo muyi sallama kenan, don Allah a yafe wa juna"
Wasu sun ji rashin daɗin tafiyarta, yayin da waɗanda suke mata hassada a kan baiwar ƙwaƙwalwa da Allah ya bata a fannin karatu suka ce, Umma ta gaida Ashsha haka, dai suka rabu suna kewar juna, duk da ba shiga hidimarsu take ba, amma they still mean a lot to her, three years no be small thing.
A hanyarsu ta dawowa gida ma haka suka yi ta jajen tafiyarta.
Cikin sanyin murya Aisha ta kalleta tace, "Best dagaske tafiya zakiyi ki barni?"
"Hmmmn!" kawai Maryamah tace, don ba taso ta buɗe baki, dan ita kaɗai tasan irin baƙin cikin da take ji da ɓacin rai a kan wannan tafiyar, dauriya kawai take yi.
Shiru suka yi kowa da abinda yake ranshi ganin yanda idanun maryamah sukayi ja ne yasa A'isha riƙe hannunta a hankali tace "Khairan Insha Allah"
Ganin sunzo inda zasu rabu ne yasa maryamah kara riƙe hannun A'isha dayake cikin nata.
"Karki damu zanje gida, anjima zan shigo na tayaki haɗa kaya"
Cikin murmushin yaƙe maryamah ta kalleta tace, "Yau kuma kece za ki zo gidanmu?"
Itama murmushin ta ƙaƙalo "Ki bari kawai ai ranar dole sai dole, amma Allah ya sani na tsani ganin baƙar fuskar matar gidanku, ga munin fuska ga na zuciya, kai tirrrrr" ta ƙarasa tana sakin yar dariya.
Rabuwa suka yi, kowa ya kama hanyar gidansu, ran Maryamah a jagule ta shiga gida, domin dariyarta da murmushin ta na ƙarfin hali ne da son ƙarfafa kanta, Bataso rauninta ya fito har Aisha ma ta shiga damuwa sosai.