← Book details Rantsatstsen Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 19

Sashe 2

Rantsatstsen Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka ta cigaba da yan aikace-aikacenta ba tare da ta yi sallar azahar ba, bare la’asar, wadda ita kanta lokacinta ya ja. Da maganar da ake yi ma biyar har tayi, kuma da alama ba ta da niyyar yin sallar, ita kanta Hajjan da ba komi take ba, sai da aka kira la’asar aka idar a masallatai sannan ta tashi ta yi alwallah ta shiga salla, a haka hassu ta dawo gidan ba ko sallama, tana shigowa da mugun gudu ta watsar da kayan da ke hannunta ta fada bayi ba ko buta, ta fara sakin zawo mai wata mummunar ƙara har tsakar gida ana jiyo ƙarar, sai bayan da ta samu sukuni ne ta tuna bata zo da buta ba, nan fa ta hau ƙwala kiran “Babarmu, babarmu, kawo mani ruwa a buta”

Takaici ma hana Baba Zainu motsawa yayi, sai zuwa can da ta ji kiran ya isheta ta miƙe ta zuba mata ruwa ta miƙa mata.

Bayan ta fito ma ko tunanin wanke hannu ba ta yi ba, ta fada kitchen tana kiran “Babarmu ina abinci na?” Ai fa Baba Zainu ta kara hawa tana fadin, “Yo waccan tijararriyar yar ta ɗauke ta cinye, shegiyar yarinya mai kama da ‘ya’yan mayu” Bata rai Hassu tayi tace, “Ban gane ta cinye ba ah, haba Babarmu wallahi ba zai yiwu ba”

Baba Zainu tace, “To sai dai ki yi hakuri, tunda ga awarar nan na gama ko ki yanka ki soya ki fara ci kafin ki fita suyar, ko kuma ki jika garin kwaki ki sha tunda akwai”

Rasa abin fadi Hassu tayi ranta a bace tace ita wallahi ba za ta ci duka ba, sai dai Baba ta bata kuɗi ta siyo wani abu ta ci. Hakan Baba ta kunce bakin zani ta dauko wata dukunkunanniyar dari biyar ta bata tace, “Ungo ki dawo mani da canji” Hassu tace, “Nan fa ɗaya Baba, a wannan zamanin abin 500 nawa yake, ba ma isata zai yi ba”

Bayan fitar Hassu, Tasallah aminiyar Baba Zainu ta kwada sallama a gidan. Baba ta amsa mata tana fadin, “Yauwa Tasallah, kamar kin san maganar ki nake a raina wallahi, daman ko ba ki zo ba to nima zuwa dare za ki ganni a gidanki, dan wallahi na gaji da halin waccan shigiyar ɗiyar mai kama da ‘ɗiyan aljanu, mafita nake nema.” Ai Hajja na jin haka ta yi wuff ta fito ɗaki tace, “Allah dai ya yi miki albarka Zainu, ni kaina tunanin yadda za mu yi mu kauda ɗiyar nan nake. Tunda ita dai yanzu ba za ka cusguna mata ba shegiya, na rasa ya akayi bakinta ya buɗe ta dena tsoro da shakkar kowa, Ga Jafaru ba ya ganin laifinta, ba ya aiki sai fadin marainiya ce, Kai ai Maryamah ta haifar mana jaraba wallahi, ita kanta bata san ba da son raina na hada zuri’a da ita ba, amma da ta tashi mutuwa maimakon ta mutu da cikin jikinta sai da ta haifo shi.”

A dai-dai nan Malam ya zo zai shiga cikin gidan, mura da ya tashi da ita ne ya matsa masa ya sanya shi barin wurin sana’arsa ya dawo gida da wuri. Dakatawa yayi daga zauren, bai idasa shiga cikin gidan ba yana sauraren su. Su kuma suna ciki ba su san da zuwansa ba, mugun nufi ya toshe musu kwanyar kai, sun kasa gane cewa ko maganar da za su yi ba ta kamata su yi ta a tsakar gida ba, su dai kawai mafita suke nema.

Tasallah tace, “To Zainu ke ce nace in raka ki wurin wani malami a ɗai-ɗaita rayuwar yarinyar nan, amma shegen son kudinki ya hanaki.” Zainu tace, “Kinga Tasallah, ni fa ki aje maganar malamin nan a gefe mu yi wata.” Tasallah tace, “To ga shawara,” har suka hada baki wurin cewa “Mun ji ki, menene shawarar?” Ta ce, “Ina yaron nan ƘYALLE NA DUNA?” Suka ce “Eh.” Ta ce, “To kun dai sanshi, shi har matan aure ma haike masu yake, me zai hana mu sameshi mu bashi aikin haike ma yarinyar, mu fadi masa ya tabbatar ya mata kaca-kaca yadda ba za ta moru ba, ko ta rayu ta kasance bata da sauran amfani.”
Aikam suka yi shewa harda Hajja, ta koma kamar wata sa’ar su suna kashewa, ta manta cewa surukarta ce suke tare suna kullama jikar ta mugun nufi tsabar ƙiyayyar uwar yarinyar da tsanar da ta yi mata.

Jiri Malam Jafaru yaji yana shirin kadashi ƙasa, yayi saurin dafa bango yana kiran “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” a cikin ransa. Nan take ya ji kansa ya buga hade da ciwon kai mai tsananin gaske, wani gagarumin tashin hankali ya taso masa wanda da za a gwada jininsa a wannan lokaci, to tabbas sai an bashi gado.

A can cikin gida kam Baba Zainu ce ke fadin, “Kai amma kawata baki taba bani shawara danaji ta dari bisa dari ba irin wannan wallahi, na ji dadin shawararki fiye da yadda kike tunani. Yanzu ya kike ganin za a yi kuma yaushe abin ya kamata ya kasance, yau ko gobe?” Da sauri Tasallah ta tareta da fadin, “Ke dadina dake garaje, wane kuma irin yau ko gobe? Komi fa sai mun tsara shi dan kada mu je kwaɓarmu ta yi ruwa. Daga nan zuwa sati guda dai za mu yi komi ya kamma.

Yanzu gobe sai ki zo muje dabar su ƘYALLE NA DUNA ɗin, duk da dai shi ɗin mutum ne mai hatsari, amma ai biyan buƙata ta fi komi, shi da ke shiga gidaje ma balle ace ya samu wannan a ɓagas,” ta faɗa tana dariya.

Gaba ɗaya dariya suka yi suka hau shewa, Baba na fadin, “Zan so in ga wannan ranar, zan so ganin wannan yarinyar ta wulaƙanta, kinga daga ranar da ta ga ta koma fanko duk wani rashin kunya, jinkai da bakar gadara ai ta ƙare,” ta faɗa ceke da zumudi tana hasaso cikar burin nasu......

FULANI
08082101373

https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr?mode=gi_t

https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr?mode=gi_t

✨🦋 RANTSATSTSEN RABO ✨ 🦋

BY RABIA'TU KABIRU ACHADU (FULANI)

YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION YOTA

SADAUKARWA GARE KI HALIMA HASHEEM(MIEMIEN HABIBI)❤️& AHMAD JAMIL AHMAD(HABIBI)♥️

FULANI ❣️
08082101373

✨🦋 RANTSATSTSEN RABO ✨ 🦋

PAGE3️⃣

Cikin mawuyacin hali malam jafaru ya dafa bango, ya bar gidan saboda baya son su san da zuwansa, balle su yi tunanin ko ya ji su ne su canja ƙudurin su akan yar marainiyar shi kuma amanar shi, Haka ya fita jiri na ɗibar shi amma ya dake cike da ƙarfin hali ya nufi gidan aminin shi malam Sale.

★★★

A can makaranta kuwa, karfe shida aka taso su sai da ta biya ajinsu muktar a nan ta samu zainab a bakin ƙofa tana jiran shi, dan haka ta kaɗo kansu suka kama hanyan gida, ita da su Aisha, da suka zo dai-dai inda zasu rabu, Aisha ta kalleta tace, “Dan Allah ki kwantar da hankalinki ki kuma saki ranki, kinsan a duniya ba abunda yafi baƙanta ran makiyi sama da yaga murmushi a fuskan wanda yake ƙi.”

Kallon tayi na ɗan wani lokaci kaman bazata bata amsa ba sai kuma tace, “Hakane, inshaa Allah zanyi ƙoƙarin yin hakan nagode sosai da ƙwarin guiwar da kike bani, Allah ya barmu tare tawan ya baki ɗan amadudu musha shagali.” ta faɗa sakin murmushi.
Dukan wasa Aisha ta kawo mata, ta kauce tana dan murmushin gefen baki tace, “To sahiba da alkhairi.” Aisha tace, “Allah ya sadamu dashi,” tace “Ameen.” Nan suka rabu.

A gida ta iske su Zainab sun rigata isa kasancewar gaba sukayo da ta tsaya tana magana da Sahiba kamar yadda tace. Da sallama ɗauke a bakinta ta shiga gidan, duk da tasan ba amsata zasuyi ba, amma dole ne ta fita hakkin zaman tare, tunda tasan amfanin sallaman, ga tarin mamakinta, sai taji Baba ta amsata har tana cewa, “Da ita Maryamah kin dawo kenan.” Cike da dumbin mamaki, ta kalli Baban amma kasancewanta miskila, sai kawai ba ta ce komi ba sai eh da ta amsata da shi, wanda ya kara kular da Baban, wadda duk cikin shirinta ne, ba da tana gudun bata shirin ta ba da sai ta mata tass.

Ɗaki ta wuce, ta shiga da sallama, amma ranta fal tunanin, To anya kuwa lafiya? Meyasa yau baba ta amsata, kuma har ta shigo ɗaki bata ji tana sakar mata baƙaƙen maganganu ba da muggan zargin da ta saba?” Oho dai kawai tace tana me ɗage kafaɗanta.
A haka ta cigaba da canja kayanta bayan ta gama, da taga akwai kamar minti 40 kafin a kira sallah, yasa ta fita tsakar gidan inda taga Baban na aikin tuwo tace, “Kawo na ƙarasa miki" ta faɗa kamar bata son yin maganar.

Ansar girkin tayi, ta cigaba da yin inda take gudanar da komi nata cikin tsafta, ta tuke tuwan lumui ta kwashe, sannan ta maida miyar wadda daman Babanta riga da tayi jajjage ta daka daddawa kawai hadawa tayi, sai ta nufi bakin rijiya inda ta wanke tukuyan tuwon da baki bakinta, gudun kada yayi kanzo, ta cikata da ruwa ta aje a gefe, buta ta ɗauka tayi alwallah ta shige ɗaki.

★★★★

Da ƙyar malam jafaru ya iya kai kanshi ƙofar gidan malam sale aminin shi, Lokacin da yaje ya samu malam sale na alwalah saboda magriba da ta gabato. Ganin yadda yake tafiya yana hada hanya ne, ya sanya malam Sale saurin tashi, tare da riƙeshi yana fadin, “Subhanallah Malam Jafaru, lafiya kuwa? Yi a hankali” zaunar dashi yayi a gefensa aƙwai ruwa, ya ɗauka ya bashi yace, “Ungo maza sha”

Kaɗan malam jafaru yasha yace, “Alhamdulillah”
Kallon shi malam sale yayi yace, “Kaɗan samu natsuwa sai kayi alwallah, muyi sallah in muka dawo sai mu tattauna"
"To ba laifi nagode sossai Malam” shi kuma yace, “Kai haba menene abun godiya kai kuwa”

Da haka Malam, bayan ya ɗan huta, ya jawo buta yayi alwallah, suka rankaya suka tafi masallaci.
Bayan idar da sallah, Malam Sale ya kalli Malam Jafaru yana fadin, “Muyi maganar yanzun ne ko mu bari mu sallaci Isha sai mu fita gaba ɗaya?” Nan ma Malam Sale cewa yayi, “Ba laifi, mu jira har ayi Isha din ta yanda in muka gama magana sai na wuce gida,” ya fadi cikin ɗacin zuciya.

★★★★
Chapter 2 · 0% Book details