Sashe 1
Rantsatstsen Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr?mode=gi_t
✨🦋 RANTSATSTSEN RABO ✨🦋
BY RABI'ATU KABIR ACHADU (FULANI)
YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION YOTA
SADAUKARWA GARE KI HALIMA HASHEEM)MIEMIEN HABIBI)❤️& AHMAD JAMIL AHMAD (HABIBI) ♥️
FULANI❣️
08082101373
✨🦋 RANTSATSTSEN RABO ✨ 🦋
PAGE1️⃣
Matashiyar budurwa ce yar kimanin shekara 17, take tafiya cikin natsuwa sanye da kayan makaranta, da alama daga makarantar boko ta taso.
Da sallama ta shiga gidan, tun a bakin kofa take jiyo irin muguwar ashariyar da wata yarinya take yi, wanda da alama fada suke yi ita da wani yaron a cikin ƴan uwanta.
Da shigarta gidan ba ta yi kasa a guiwa ba, ta kai ma bakin yarinyar duka, duka yarinyar bazata wuce shekara 8 zuwa tara ba, a razane ta dago, ta bude baki da niyyar ƙara yin wani zagin, amma ganin wadda take tsaye a gaban ta yasa ta yi sauri ta kame bakinta da hannu biyu tana zare ido.
Kunnenta matashiyar budurwar ta ja ta murɗe da ƙarfi tana fadin,
“Zainab, me nace miki akan zagi? shi Mukhtar din da kike zagin sa’an ki ne?"
Tuni idanuwan ta har sun cika da hawaye na azaba da tsoro cikin rawar murya tace,
“Addah dan Allah ki yi haƙuri, shine ya fara ɗaukan min abu kuma na yi masa magana ya dake ni”
Dara daran idanuwanta ta dago ta kalli inda yaron yake, dan kimanin shekara 10, wanda tun shigowarta ya sha jinin jikinsa, kallo ɗaya tayi mishi wanda tun kafin ma ta ce wani abu yayi saurin fadin,
“Addah wallahi ba gaskiya ba ne, ita ce na aje abu ta ɗauka kuma ba ma nawa ba ne, na sani abokina ne, shi ne ta lalata, na mata magana ta taka min rashin kunya.”
“Shi ne sai ka daketa ko?”
“A’a” yace yana zare ido.
“To sai ka mata mi?”
“Addah ki yi hakuri dan Allah,” ya fadi yana ƙasa da kansa.
Kwafa ta yi ta saki kunnen yarinyar tana fadin
“Kun yi sallar azahar?”
Tana binsu da ido alamar amsa take jira. Cikin sauri suka je suka dauko buta a bakin rijiya.
Ta ce, “Allah ya shirye ku ku kam”
Idonta ne ya fada kan Baba Zainu da take zaune tana faman aika mata da harara, tana aikin awara ta saidawa da suke yi.
Ɗan kauda kanta ta yi kadan tace,
“Baba sannu da gida.”
Dogon tsaki ta ja tana faɗin,
“Muguwa, sai bayan da kika gama cin zalin yara sannan kika ganni kenan? To wallahi ni dai ki fita daga ido na dan akan yarana zan iya yin komai, ke fitsarar da kika yi ma da dukan ki akayi ai da baki kawo yanzu ba.”
Ta faɗa tana kara banka mata uwar harara.
Ɗauke kanta ta yi kawai ta nufi kofar ɗakin su ba tare da ta ce mata komi ba, saboda ba ta da lokacin fitinar matar nan wadda ita komai za'a mata laifi ne, dan ma dai ba yar jarababbiyar tsohuwa bace ta ganta da faɗan ma sai yafi haka tana jin kila bata gidan ko tana can tana baccin asara.
Bata kai ƙarshen tunaninta ba ta jiyo muryar Hajja ta ɗaga labule tana fadin,
“Zainu wai hayaniyar menene nake faman ji? Lafiya ba za a bar mutum ya yi bacci ba?”
Cike da takaici zainu tace,
“Baba ni da wannan shegiyar yarinyar ce, daga shigowarta gida ta kama zaluntar yara. Ita dai idan tana gida yara ba su taɓa samun sakewa”
“Tsananin rashin kunya da rashin ganin girman nagaba da ita ai ba zai bari a takurata ba”
Hajja ta faɗi tana yaye labule ta fito tana ci gaba da faɗan,
“Kafurar yarinya ƴar nema ta dawo kenan! Kai mu dai wannan yarinya an haifar mana jafa’i, gaskiya Jafaru bai mani adalci ba da ya je ya auro mana wannan baƙar kadara, gashi nan da ta tashi mutuwa bata mutu ba sai da ta bar mana mugun iri”
A fusace budurwar ta waigo tana faɗin,
“Da ban shigo da niyyar tanka maku ba kaff din ku, amma Hajja saboda maganar da kika yi yasa dole sai na yi magana ki sani mahaifiyata ba baƙar kadara ba ce kuma da ikon Allah sai dai ki ga baƙar kadara a wani wuri ba nan ba”
Ta fadi tana juyawa tayi shigewarta ɗaki.
La masalli ala ina wuta!Hajja ta jefata, ta kama bambamin bala’i akan *Maryamah* tana zagin ta, tana faɗin bari Jafaru ya zo ya ɗau mummunan mataki akanta, Baba Zainu kuma na faman tunzurata.
Maryamah kam shigewarta ɗaki ta yi tana fadin,
“Kanku ake ji za ku yi ku gama, ni kam ai kun gama mani cin kashi in kyale a gidan nan wallahi”
Ranta duk a jagule ta cire uniform ɗinta ta daura zani da ɗan ƙaramin hijabi, ta dauki kayan wanka ta fito tsakar gida. Ruwa ta ja a rijiya ta nufi kewayen gida ta yi wanka kasancewar garin da zafi, daga nan ta dauro alwallah.
Bayan ta shirya ta fita tsakar gida ta nufi ɗan ƙaramin kitchen ɗinsu zata ɗauki abincinta, amma ga mamakinta babu, kamar ma dai ba a aje mata ba.
Ta fito ta kalli Baba Zainu tace,
“Baba abincina fa?”
“Ban dafa dake ba uwata” ta fadi.
Maryamah ta ce,
“Yanzu abin da nake so na sani shi ne kin dafa abinci ne baki aje min ba ko kuwa baki dafa ba gaba ɗaya?”
“Bakijin Hausa ne halan? Bakiji nace ban dafa dake ba?” ta ce tana kumfar baki.
Shiru Maryamah ta yi na yan sakonni sannan tace,
“Amma ba Baba ne ya kawo abunda aka dafa ɗin ba?”
Kafin a ba ta amsa Hajja ta hayayyako tana fadin,
“In shine ya kawo fa sai akayi yaya?”
Maryamah ta saki dan murmushi tace,
“Aikam indai Babana ya kawo abinci aka dafa a gidan nan tofa banga wanda ya isa ya hanani cinshi ba.”
“To ai sai ki bigeni ki kwata fitsararriya,” in ji Baba Zainu.
“Ba za a kai ga haka ba,” cewar Maryamah, “amma fa abinci sai na ci”
Ta fadi tana komawa kitchen ta fara buɗe kwanuka.
Tana fitowa da shi Baba Zainu ta yi karaf zata anshe tana fadin,
“Wallahi ba za ki ci abincin nan ba, In kin ci ita hassu in ta dawo taci me?"
Tayi haƙuri ko ta je gidan uban ta taci” ta bata amsa tana wuce wa.
Hankalinta kwance Maryamah ta shige ɗaki ta ci abincinta.
Haka ta bar Baba Zainu da Hajja suna mata tofin alatsine da muggan alkaba’i.
Bayan ta gama ta shirya cikin kayan islamiyya ta fito ta yi alwallah tana kiran Mubarak da Zainab su shirya, kowanne ya sanya kayan islamiyya su wuce.
Baba Zainu ta ce ba inda yaranta za su je, amma Maryamah ta ce dole su je makaranta, domin ita yayarsu ce kuma tana da cikakken ikon kula da su, dole ta taya mahaifinta tarbiyyarsu.
Tana faɗin haka tana ƙunshe dariya, ta san ta gama kunnata. Baba Zainu ta kunduma ashar tana kiranta mara tarbiyya, tana rantsewa dole sai ta ga bayan Maryamah a garin nan.
Ita kam Maryamah tace,
“Ai ga Allah na dogara kuma ba wani ɗan adam da ya isa ya yi mani abin da Allah bai yi min ba”
Ta tasa yaran suka fita ta bar su suna tsine mata...
Topha....
FULANI

BY RABIA'TU KABIRU ACHADU (FULANI)
YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION YOTA
SADAUKARWA GARE KI HALIMA HASHEEM (MIEMIEN HABIBI)❤️& AHMAD JAMIL AHMAD (HABIBI)♥️
FULANI ❣️
08082101373
✨🦋 RANTSATSTSEN RABO ✨ 🦋
PAGE 2️⃣
Haka ta tasa kannenta biyu suka nufi islamiyya. Suna tafiya ta gamu da ƙawarta Aisha, wadda suke unguwa ɗaya tare da ita, ita ma da ƙannenta biyu amma duk mata ne. Suna tafe suna dan tattaunawa akan rayuwa.
Aisha ce ta kalleta tace, “Na ga kamar ranki a ɓace kawa, halan ke da mutanen gidanku ne?” ta faɗa tana murmushi. Numfashi kawai Maryamah ta sauke tace, “Ke da kika san komai, mutanen nan halinsu dai yana nan wallahi, sai dai Allah ya kyauta,” ta faɗa tana ɗan yatsina fuska alamar lamarin na bata takaici.
Aisha tace, “To ya za'ayi sai hakuri, kin riga kin saba da halinsu kam. Shekara 15 ai ba kwana biyar ba ne, tunda Allah ma ya sa kin dena masu wannan miskilancin naki, Kinaji kina gani suna cutarki ai da sauki”
Maryamah tace, “Ba za ki gane ba, dole ta sanya na buɗe bakina akan mutanen nan, wallahi gaba ɗaya su ba su da tunani, ba su san yakana ba sam”
“Allah dai ya kyauta,” cewar Aisha, suna shiga aji kasancewar har sun shigo cikin makarantar.
★★★
A can gida kuwa bayan fitar maryamah, haka ta barsu suna ta sababi, suna zage-zage akanta, wadda tana can tana karatunta ta barsu da ciwon baki.
A haka Baba Zainu ta yi awararta ta gama, tana ta saƙe-saƙe a cikin ranta na abin da ya kamata ta yi wanda rayuwar Maryamah za ta wulakanta ta koma ƙaskantacciya abar ƙyama. Haka dai ta dinga saka mugun nufinta akan Maryamah.
Hajja na gefe ita ma
tana nata tunanin sun mugun tsanar Maryamah, sun tsani su bude ido su ganta cikin gidan nan tana walwala, ba ma kamar yanzu da yarinyar ta zame musu ƙarfen ƙafa, duk ba suƙi su buɗe ido su ga ta ƙasƙanta ba, ƙasƙanta mafi muni a duniya, amma abin ya ci tura, ba kalan tuggun da ba su hada mata ba har a wurin mahaifinta, amma gaba daya yarinyar kamar mai aiki da rauhanai, sai ka ga ta tsallake, Duk da haka tana fatan wannan karon ta fada tarkon da za ta yi mata.