← Book details Rantsatstsen Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 19

Sashe 10

Rantsatstsen Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wajen ne ya ɗauki shiru, zuwa can Malam Sale ya katse shirun masu dacewa "Hajiya alfarmar dai da muke nema dani da mahaifin yarinyar shine, dan girman Allah a samu wata makarantar gwamnati ko kuma irinta mai ƙaramin karfi, sai a sanyata, Idan yaso shi albashin nata sai a ringa biya mata kuɗin makarantar dasu"

Murmushi tayi "Maganar karatunta ba wani abu bane, inshaa Allah za'a nemi makaranta a sata kamar yanda nayi alƙawari, sannan bama sai an taɓa kuɗinta ba, abin bazai gagara ba inshaa Allah"

Cikin tsananin farin ciki, Malam Sale ya hau yi mata godiya, itama Maryamah tace, "Allah ya saka da alkhairi, ya kara girma Hajiya"

murmushi tayi tace, "Bakomi ai yiwa kai ne shi ɗa na kowa ne"

Suna cikin magana ne, aka buɗe ƙofar aka shigo da sallama, matashiyar budurwa ce, zatayi sa'a ɗaya da Maryamah ta shigo, sai yara biyu maza biye da ita duk da uniform a jikinsu.

"Wash mami nagaji" tayi maganar tana kwantar da kanta a kafaɗan mamin da ta zauna kusa da ita.

Ture mata kai mamyn tayi "Abinda kika iya kenan"

Dariya twins suka fara yi mata, ita kuma ta ɓata fuska.

Katse su tayi da "halan baki ga baƙo ba?"

"Afuwan mamy wallahi ban kula ba, ina yini?” ta gaishe shi tana gyara zaman ta, Idonta bai faɗa ko ina ba sai kan Maryamah data ɗago tana kallonsu.
Cikin sauri budurwan tace "Wow, what's a beautiful creature" tayi maganar tana haɗe yatsanta manuni da babba waje ɗaya.

Maganar da tayi ce ta janyo hankalin twins daga gaida Malam Sale da suke, suka kalli inda take kallo, suma suka hada baki wajen cewa, "Wow mami tanada kyau, muna sonta"

Basu jira cewar mamyn nasu ba suka nufi inda take.

Itama kallonsu tayi tana ɗan riƙe hannunsu kaɗan, duk da bata saki jikinta ba, haka tayi ma budurwar murmushi tana faɗin "Inayini"

Zaro ido budurwar tayi tace "Kaini kike gaidawa" dariya ce ta ƙwace mata cike da mamakin an gaisuwar.

"Allah ya shirya ki Zuhyra, kuje ku cire unifoam" cewar mamyn tana kallon yaran nata.

Tashi tayi tana faɗin, "But mami who is she?" Tayi maganar tana nuna Maryamah.

Girgiza kai mamin tayi tace "Our new maid"

Yar ƙara Zuhura tayi tana ɗan tsalle "Wow mami kin biyani nikam" sama tayi da gudu, twins na binta a baya, girgiza kai mami tayi Allah ya shirya......

FULANI
08082101373

https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr?mode=gi_t

https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr?mode=gi_t

✨🦋 RANTSATSTSEN RABO ✨ 🦋

BY RABI'ATU KABIR ACHADU (FULANI)

YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION YOTA

SADAUKARWA GARE KI HALIMA HASHEEM (MIEMIEN HABIBI)❤️ & AHMAD JAMIL AHMAD (HABIBI)♥️

FULANI ❣️
08082101373

✨🦋RANTSATSTSEN RABO 🦋 ✨

PAGE 1️⃣1️⃣

Ƴar dariya malam sale yayi ya amsa da "amin itadai ba ruwanta"

"Haka take bansan ranar da zatayi hankali ba"

Da haka suka dawo maganar da sukeyi sosai malam sale yayi mata godiya haɗi da addu’o’i, sannan ya kalli Maryamah yace, "Yar babanta kinji duk abinda hajiya tace?"

Jinjina masa kanta tayi.

"Ina fata zaki cigaba da nuna halayenki nagari ga mutanen nan kamar yanda nasan ki dasu?"

"Insha Allahu baba"
"Allah yayi ma rayuwarki albarka, ya ɗaga darajarki, Allah ya cika miki burikanki na alkhairi"

Da amin ta amsa kanta a ƙasa.

"Insha Allah zakiyi farin ciki, kedai ki tsare kanki da mutuncin kanki, banda kwaɗayin abun wani"
"Inshaa Allah"

Da haka ya miƙe "zan ɗan shiga cikin gari, In Allah ya kaimu gobe kafin na tafi, zan biyo ta nan muyi sallama"

Cikin marairaice murya tace "Baba ba'a nan zaka kwana ba?"

Murmushi yayi "ƴar shagwaɓan babanta, in miki ta bakin baban naki, ba nan zan kwana ba, akwai abinda zanyi a cikin garin, tunda gobe nake son juyawa saboda ba kasuwanci ya kawoni ba balle na kwana biyu a garin, na miki alƙawarin insha Allah, duk lokacin da na shigo garin zan ringa leƙowa mu gaisa"

"Shikenan baba Allah ya kaimu gobe" tayi maganar hawaye na zubo mata.

Hajiya tace "Kuka bayama ɗiyata wahala dai, da alama kodai da gaske yar shagwaɓan ce?"

Ƙasa tayi da kanta tana murmushi cikin jin kunya.

Bayan tafiyar malam sale, hajiya ta kira mai aikinta babbar cikinsu mai suna lami, "Iya lami,kije da ita ɗakinku a bata abinda ya kamata, Ina ganin ta zauna ɗakinki, shi wancan ɗakin sai a barwa su dije da Sahura"

Cike da ladabi, amsa da toh hajiya, muje tayi maganar tana yin gaba.

Kallonta hajiya tayi tace, "Maryamah, zaki iya zuwa ki huta, kunsha hanya, sai zuwa gobe zaki fara aikinki"

Da to ta amsa tayi mata godiya tabi bayan iya.

Sosai kalmar godiyan tayi wa hajiya daɗi a ranta ga dukkan alamu yarinyar ta samu tarbiyya mai kyau kuma da alama ba sai an sha wahala akanta ba, dan dagani bata da duhun kai tunda ba daga ƙauye ƙayau take ba.

★★★

Bayan tafiyar su, Zuhura ta sauko cikin kaya mara nauyi, riga da wando na wani yadi mai matuƙar tsada, kanta ba ɗankali amma tana rike da hulanta a hannu sabida tasan, ko giyan wake tasha, bazata sauka wurin mami ta zauna ba ɗankwali ba, yanzun tasha ranƙwashi, gashi in ta fara mita har a kwanta bacci tanayi "Bakwa gujewa kanku shaiɗanu kudai, ku dinga ɗaukan ɗabi’un yahudawa"

Haka ta sakko ta nufi dining area ta ɗebo abinci ɗan kaɗan a plate kamar wanda za a bawa yarinya, ta haɗo da ruwa da juice a cup, kusa da mami ta zauna, ganin bata ganta bane yasa ta tambayi "Mamy tana ina?''

"Wace?" Ta mayar mata da tambayar ta.

"Ayya mamy house helper ɗin da kikace an kawo mana"

Ganin yanda tayi mata magana kaman me shirin kuka ne yasa tace "Tana ciki wajen iya Lami"

"Mamy wajen masu aiki kuma?" Ɓata fuska tayi alamun hakan baiyi mata ba.

Ido mamy ta zura mata tana ganin ikon Allah "itama ba aiki tazo yi ba halan?"

"Shi tazoyi but she's different from them" tayi maganar tana ƙara ɓata fuska.

"Au Allah?" Ta ƙara tambayar ta cike da gatse.

"Allah mamy kema ai kinga ita she's special mai aiki" tayi maganar with full of excitement.

Mamee tace "Aa, nidai kam ban gani ba"
"Nidai mamy please a bata ɗaki ko cikin parlour ɗin nan, not at wajen masu aiki" tayi maganar hankalinta kwance, tana kai abinci bakinta.

"Bari dai ta kwana biyu muga yanayinta, ni kaina yarinyar ta kwanta min a rai tun kallon farko"
Cike da jin daɗi Zuhura tace "Yauwa mamy i love you" kiss ta hura mata, ta maida hankalinta kan abinci.
Girgiza kai kawai mamy tayi.

Suna zaune twins ma suka fito, duk sun canja kaya, abu na farko da suka fara shine tambayan mamy Ina aunty cutie.

Cike da mamaki mamy tace "Tofah wacece haka kuma?" Tayi maganar tana kama haɓa.

"The new maid" cewar fadil.

Mamy sosai tayi matuƙar mamaki Ikon Allah wai su yaran nan, daga ganin yarinya yau kowwa ya susuce a kanta, sonta suke koda yake ita kanta haka taji a ranta game da yarinyar.

Ganin yanda suka zuba mata ido alamun amsar ta suke jira ne yasa tace "She's in her room"

Har suna haɗa baki wajen tambayar "Which of the rooms?"

''Ɗakin iya Lami"
Kai tsaye suka juya zasuyi inda ɗakunan masu aikin yake, amma mamy ta kirasu tace su dawo, lokacin magrib yayi yanzun za'a fara kira, suyi maza su shiga toilet na rooms ɗin dake parlour, idan suyi alwallah su tafi masjid, in sun dawo sai suje su ganta.

A haka badan sun so ba suka tafi, sukayo alwallah suka wuce with full of excitement, kan cewa zasu je su faɗawa brothers nasu na part ɗin mommy cewa an kawo musu wata cutie aunty mai aiki.

Tashi mamee tayi ta wuce sama tana faɗin, Kema kiyi maza kigama kije kiyi sallah, time yayi, da haka ta haye sama.

Haka zuhura ta ɗan tsakuri abincin, tashi tayi takai plate ɗin kitchen saboda tarbiyyan da mamy tayi musu kenan, sanda ta shiga haka ta samu iya nata faman hada hadan tuwo, dan yau shi mamy tace ayi da dare. Sannu ta mata da aiki ta wuce ta aje plate din ta fita.

Bayan an idar da sallar isha, haka suka shigo gidan suna yan guje gujensu dasu dasu Adil da Aqeel waɗanda suka faɗawq sunyi new cute auntyn su shine fah suka zo ganinta.

Saukowan mamy kenan taji guje gujen su ana rige rigen zuwa ɗakin iya a gano aunty cutie, Mamy tace Kudai Allah ya shirye ku, ta nemi wuri ta zauna, A haka, itama Zuhura ta sauko, ko zama batayi ba ta kama hanyan shashen masu aikin su.

Mamy ce ta dakatar da ita "dawo ki zauna"

"Mamy please"

"Zasu fito yanzun dasu Fadil"

Bata rufe baki ba taji hayaniyan su sunko tasota, kowwa so yake yayi mata labari har da Fudail da magana ma bata dameshi ba, Ita kam sai murmushi take masu ta rasa wa zata amsa, haka suka fito falon.

Ganin mamyn a zaune ne yasa ta rusuna "sannu da hutawa hajiya"

kafin ta amsa har Fadil ya tari numfashin ta "Mamy zakina ce mata cutie?"

Murmushi kawai tayi, gefe da gefen kumatunta na lotsawa. Fudail yace "You look more beautiful in kikayi smiling cutie"

Wani murmushin ta ƙara, suka nemu wuri suka zauna a kasan carpet mai laushin tsiya.

Ɗago idonta tayi ta kalli Zuhura ta mata ɗan murmushi "Sannu"

Zuhura da ta cika tayi fam kam kin amsawa tayi.

Mamee ta kalleta tace, "Baby ke kam kin shigesu wallahi"

"Amman mamy kina gani ta kula kowa banda ni"

Zaro ido Maryamah tayi tana kallon Zuhuran.

Mamee tace Allah ya kyauta miki.

Haka suka zauna sunata mata hira, Ita kam hankalinta duk baya kansu sosai duk da taji matuƙar daɗi na yanda yaran suka amsheta da ma sauran yan gidan, amma tunaninta na kan takira babanta, wayan ta sanya caji ta barota dakin so hankalinta duk yana can.

Ganin har lokacin bata sake ba, mamee tace, "Oyo, Aqeel and Adeel ku je ku kwanta, dare yayi, Ta kalli su Fadil Kuma kuje kuyi shirin bacci, gobe akwai school, kubarta ta huta....."

FULANI
08082101373

https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr?mode=gi_t

https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr?mode=gi_t

🦋✨ RANTSATSTSEN RABO ✨ 🦋

BY RABIA'TU KABIRU ACHADU (FULANI)

YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION YOTA

SADAUKARWA GARE KI HALIMA HASHEEM (MIEMIEN HABIBI)❤️& AHMAD JAMIL AHMAD (HABIBI)♥️

FULANI ❣️
08082101373
Chapter 10 · 0% Book details