← Book details Rantsatstsen Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 19

Sashe 13

Rantsatstsen Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"A'a, ba abinda zanyi dasu ai"
"Ki riƙe saboda tsaron lalura"

Bata son musu da shi shiyasa ta amsa tayi mishi godiya.

Albarka ya kuma saka mata.

Haka suka rabu ta juyo ta koma cikin gidan, shi kuma ya kama hanya driver zai kaishi ta sha.

Koda ta shiga bata samu mamy a parlour ba, sai kawai ta nufi ɗaki ta ajiye kuɗin hannunta, ta kama hanya ta koma kitchen.

Da sallama ta shiga tayi musu sannu da aiki.

Tsaki su sahura suka ja mata kasancewan Iya ta fita backyard na part ɗin tana wani abu.

Ganin haka sai bata bi ta kansu ba, ta nemi waje ta zauna tana jiran iya ta dawo, tana nan zaune, tana jinsu suna habaici, bata tanka masu ba saboda ita dai bataga abinda tayi masu ba daga zuwanta jiya-jija.

Suna cikin haka, Iya ta shigo, sai duk sukayi shiru.

Iya tace "Maryamah har kin dawo?"

"Eh" daga haka taja bakinta ta tsuke, ba tare da ta faɗi dalilin kiran da akayi mata ba, wanda su Sahura suka zuba kunne suna jiran suji, Ita kam kamar ta sani, sai bata faɗa ba, daman can tana da zurfin ciki, bata da yawan magana, sai in tana tare da babanta ko sahibar ta.

Haka suka cigaba da aikin Iya na bata yan abubuwa masu sauƙi, saboda tasan ba abinda aka ɗauke ta tayi ba, wanda hakan ma ba ƙaramin baƙin jini ya ƙara jawo mata ba, wajen su dije suna ganin kamar Iyan na fifitata ne kan su, dan dai basu samu damar faɗawa wa Iyan ba.

Bayan an gama komai su sahura suka ɗauka suka jera a dining, wanda daman kula da table ɗin na ɗaya daga cikin aikin su, sannan suka fitar da nasu, dana sauran masu aikin part ɗin maza da kuma security dake gate, duk da su acikin albashinsu ake fitar masu da kuɗin abinci, amma mamy tace a ringayi da su ana basu.

Hakan kuma ya jawo suke matuƙar ganin girmanta fiye da matar ɗayan apartment ɗin, wanda kuma ya ƙara jawo mata mummunar tsana a gurin abokiyar zaman nata, dan tana kallon hakan a matsayin munafunci da kinibibi.

Bayan sun gama komai, d6aki suka tafi da abincin su.
Ita Maryamah ta ɗauki nata dana Iya su kuma su Sahura suka ɗauki nasu, suka nufi nasu kofan, a haka ma saida Sahura ta bangaji Maryamah, dan ita tafi jin tsana da ƙyashin Maryaman akan dije, sabida ita Sahura irin mutanen nan ne masu so su zama sune na farko, ko a guri suna so afi yabon su akan kowa, wanda zuwan Maryamah daga jiya zuwa yau taga kamar ita Maryamah ce zata samu duk wanna abubuwan da taso, ace ita ce keda su.

Sannan uwa-uba baiwar kyan da taga Allah yayi ma Maryamah, wanda yanzun babu ne ya ɓoye shi, amma tasan nan da wata biyu zuwa uku, yaro6nyar zata iya sajewa da yan gidan a ringa ganin kamar itama yar gidan ce, abinda bazata taba fata ba kenan, wata tazo daga bayan su ta fisu samun shiga, sannan gashi da alama yarinyar bata da irin duhun kan da sukazo dashi, dansu sunfi shekara kafin su fara gane kan komai.

Girgiza kai kawai Maryamah tayi a ranta tana ayyana tofah! nanma ashe akwai wani ƙalubalen, amma a zuciyar ta tana jin nasu mai sauƙi ne tunda ba zaman su take ba akan nasu Baba Zainu, tuna hakan ne yasa ta faɗin Allah sarki koya suka ƙare? Oho, koya Hajja zatayi in ta dawo taji tabar garin? Allah sarki, Zainab da Muktar ina kewan ku.

Ɗaki ta wuce ta ajiye ma Iya nata abincin, itama ta ajiye nata, ta shiga ta ɗauro alwallah tazo ta kabbara sallar azahar kasancewan lokacinta yayi, bayan ta idar, ne tadan tsakuri abincin, da ita bata saba da wannan cimar ba, Kishingiɗa tayi daga nan bacci ya ɗauke ta saboda har lokacin da gajiyar tafiya a tare da ita, ga kuma yau ta sha aiki, ba laifi.........

FULANI
08082101373

https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr?mode=gi_thttps://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr?mode=gi_t

https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr?mode=gi_t

✨🦋 RANTSATSTSEN RABO 🦋 ✨

BY RABIA'TU KABIRU ACHADU (FULANI)

YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION YOTA

SADAUKARWA GARE KI HALIMA HASHEEM (MIEMIEN HABIBI)❤️ & AHMAD JAMIL AHMAD (HABIBI)♥️

FULANI ❣️
08082101373

PAGE 1️⃣5️⃣

CHARANCHI

Tashin hankali na gidan duniya, malam jafaru ya shige shi, sanda ya koma gida, ya samu Hajjah nata surfa bala'i, ta inda shiga bata nan take fita ba, tace saboda ya rainata zai ɗauki yarinya, yace ya bar gari da ita, to gidan ubanwa ya kaita? duk inda ya kaita ya je ya dawo da ita, haka ta dinga uwar masifa, ta maƙi tsayawa ta saurare shi gaba ɗaya.

Da yaga abun bana ƙarewa bane, sai ya fita ya je gidan kawun Hajjan, wanda shi kaɗai ya rage mata, kuma tasan yafita masifa, sannan ko bata so haka take jin maganar shi, da yaje ya same shi ya faɗa mashi abinda yake tafe dashi da kuma dalilin shi na barin garin da maryamah.

Nanfa kawu lawalli ya fusata, "muje gidan na sameta, ashe Ramatu bata da hankali har yanzun ban sani ba, ache da ita za'ayi ma jikarta wannan mugun ƙullin kai, tirrr da halin Ramatu" faɗa yake haɗi da mamaki duka a lokaci ɗaya.

"Baba ni so nake kawai ka tsawatar mata akan cewar da tayi, sai na maido Maryamah ko ta tsine mani albarka" yayi maganar cike da takaicin abin da mahaifiyar tashi tayi mishi da shi da ɗiyar shi.

"Shikenan kaje zanzo gidan yanzun"

Bayan tafiyan Malam Jafaru, ne Kawu Lawwali yabi bayan shi.

Yana zuwa a ƙofar gida ya sameshi dan shi har ga Allah zullumin shiga gidan yake, bai samu ƙwarin guiwar shiga ba saida Kawu ya iso, yayi mishi jagora, suka shiga da sallama, har Hajjah ta fara masifa, amma ganin wanda ke bayanshi ya sanyata haɗiye abinda tayi niyyar cewa.

Ita kanta Zainu tasha jinin jikinta don tasan Kawu Lawwali tsaff zai zagesu, ita da Hajjan da take goya mata baya, dan Kawu cikakken bakatsine ne, ya zagesu ya kuma tsine su tass.

Tabarma Hajjah ta shimfida tana faɗin, "Kawu kaine tafe?"

Yace "Eh, nine tafe, tunda kin uzzura ma ɗanki kin sashi dole ya isko ni a gida ya min bayani, anya kuwa Ramatu ashe bazakiyi hankali ba?" Ya faɗi yana karkatar da hula, wanda tasan da taja magana tayi tsayi ƙarshe, zai zageta ne tass a gaban ɗanta da suruka, shi ba abinda ya dameshi.

Shiru tayi tana hararar baba dake gefe, karaf a idon Kawu, aikuwa ya fara sababi "Ai ni ya kamata ki harara ba shiba Ramatu, ko kuma ki tashi ki rufeni da duka"

"Kayi haƙuri Kawu"

"Duk ba wannan ba, Jafaru yazo kuma ya faɗa min duk abinda yafaru, ni na amince da hukuncin shi, dan haka ni nace a can yarinya zata zauna, kuma kada in karajin an tada zancen, In kuma ba haka ba, rayuka zasu ɓaci aci, ke kinsan halina"

"Shi kenan Kawu, anbar maganar baza a kara tada ta ba"

"Tom dai yafi miki"

Da haka yayi masu sallama, Malam Jafaru ya rakashi yana godiya, shi kuma yace dashi duk lokacin da ta kara tada maganar, yaje yaa sameshi, in yazo sai ta gwammaci ta haƙuran kamar yanda ya bukata a farko.

Da haka ya samu magana ta mutu, amma Hajjah na fushi dashi bata dai ce mishi komi ba.

★★★★

Bacci sossai Maryamah tayi, dan har kusan 4, sannan ta tashi tayi sallah.

Iya ta tambaya koda abinda za'ayi.

Amsa ta bata da a'a bakomai, dan yau ma Hajjah tace ba sai an ɗora girkin dare ba.

Toh tace daga haka ta ɗakko littafinta na makaranta tana bita, har 5 tana nan zaune, Aisha ma ta kira, sun gaisa har suka gaisa da Umma, ta ƙara mata nasiha akan ta kwantar da hankalinta, Ita tama rasa abinda zatayi, saboda ta saba inda gida ne, da yanzun tana islamiyya, dan tana dawowa boko ƙarfe 2 tayi abinda zatayi, 4 ta tafi islamiyya, sai kuma 6.

Tunanin gida ta dingayi, a haka ma sai da taji tana kewan masifan Baba Zainu da Hajjah Tana nan zaune, taji an shigo ɗakin da sallama, ɗagowa tayi tana amsawa, taga Fudail ne da Fadil, ashe har sun dawo, shine suna cire uniform sukayo gurinta.

Da murmushi a fuskarta tare su "Yammakaranta an dawo?"
"Mun dawo cutie,
Shine bakizo kince mana oyoyo ba"
"Eyya kuyi haƙuri to gobe zanzo nayi maku, ai kunga bansan time ɗin da kuke dawowa ba"

Fadil yace "5 muke tashi sanda zamuzo gida 5:30, saboda akwai ɗan nisa, kuma kinga yamma in tayi Abuja akwai hold up"

Murmushi tayi "A'a aini bansan Abuja ba, kaga bazansan akwai hold up ba"

Suma duk murmushi sukayi suna cewa "Kizo muje main parlour please" suka faɗa suna haɗe hannunsu waje ɗaya.

"A'a kuje dai ai kunzo mun gaisa"

Ƙara haɗe hannayen su sukayi "Please please" Fadil ya kamo hannunta, wai ta miƙe yana please Da haka suka rinjayeta tace shikenan, muje to.

Haka suka sanyata a tsakiya suka fito ɗakin, a bakin ƙofa suka samu su Sahura suna masu laɓe, ɗauke kai yaran sukayi, duk da basu da raini, amma Samm sudai Dije da Sahura basuyi masu ba, musamman Fudail da yake miskili shi daman ba kowa yake birge shi ba Shi ya sanya ita kanta Mamy tayi mamaki da taga har dashi cikin masu ɗokin Maryamah.

Wuce su sukayi da yake itama Maryamah gwana ce wurin shariya, suka nufi parlour.

Anan suka samu Mamy zaune tana waya, bayan ta katse tace mata, "Barka da yamma Hajjah" Tana duƙawa ƙasa.

Fadil yayi saurin cewa, "Mamy not Hajjah"
Murmushi tayi kawai.

Mamy tace "Toh kinji abinda Fadil yace?"

"Tom inshaa Allah mamy"

Zama sukayi, suka sanyata a tsakiya suna mata surutun makaranta.

Ita Mamy ma mamaki, Fudail ke bata yaron da beda yarda, amma shine ya saki jiki da Maryamah da ya sani jiya jiyan nan.

A haka Zuhura ta sauko, tana sanya riga da wando irin yan Turkish din nan, masu taushi da ɗaukar ido, kanta sanye da hula ta cusa gashinta ciki.
Bayan ta sauko ne ta nemo guri ta zauna kusa da Mamy "wash Mamy na gaji"
Chapter 13 · 0% Book details