Sashe 12
Rantsatstsen Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Fadil da Fudail ne suka hada baki wajen faɗin, "Morning cutie"
Murmushi tayi masu tace "Kun tashi lafiya?"
“Alhamdulillah.”
"Oya ku wuce kuyi breakfast" cewar mamy ganin suna shirin ƙara yin wata maganar.
Wucewa sukayi, lokacin ita ma Zuhura ta sauko.
Tana saukowa suka hada ido da Maryamah tace mata "Ina kwana?"
Kaman me jira ta bushe da dariya tace "Nifa wallahi kunya kike bani, in kika gaidani bafa wani girmarki nayi ba, kilan ma sai dai muyi age mate"
Murmushi kawai Maryamah ta mata.
Ita kuma Zuhura, da ta tabbatar Maryamah ba magana zatayi bane, yasa ta kalleta "ya kwanan ba kunta, hope dai kinyi bacci yanda ya dace?"
Aisha ce ta faɗo mata a rai, sanda Zuhura ke mata wannan tambayan, sai kawai tayi murmushi mai faɗi "eh alhamdulillah"
Mashaa Allah ta furta tana wucewa dining area inda su mamy suke, already har sun fara cin abincin su.
Sallama tayi dan tasan ƙa’idar mamy sannan tace mata,"Mamy good morning"
"Morning baby, how was your night?"
"Alhamdulillah"
"Mashaa Allah"
Nan suma, twins suka kalleta suna gaidata, amsawa tayi ta shafa kansu.
Kujera taja ta zauna ta fara serving kanta tea kawai ta had6a da chips.
Cikin natsuwa suka karya suka gama.
Bayan sun gama, dije mai aikinsu ta fito riƙe da lunch boxes nasu. Nan kowwa ya amshi nashi, sunawa mamyn su bye bye
"Bye ayi karatun and ayi addu’a kafin a fita"
★★★
Bayan tafiyan sune mamy ta dawo main parlour, ta samu Maryamah tace "Muje sama na nuna miki inda zaki gyara"
Bayan ta tabi suka hau saman, Ita sai yau ma ta ƙara kallon yanda benem yake, ita kam ai bata taɓa ganin bene irin wannan ba, duk da ta taɓa hawa bene sanda sukaje Katsina ita da Aisha da umma biki gidan yayan umman Aisha, Amma gaskiya ba irin wannan bane, wannan kam da banbanci da wancan, dan wannan ba ka cika gane cewa bene kake hawa ba saboda faɗin staircase ɗin, ga ƙarafunan gefen ma gwanin sha'awa.
Bata ƙara rikicewa ba saida suka isa saman, taga irin tsaruwar gurin,
ba ƙarya parlourn yayi masifar kyau, dan bata cuci kanta ba, haka ta saki ido ta hau kallon aljannar duniya, an zuba dukiya, ba ƙarya a wajen, duk da ba wani tarkace ne a parlourn ba, amma su kansu kujerun da aka ƙawata parlourn dasu abun kallo ne, Itadai ko a film bata taɓa ganinsu ba, duk da ba wani kallo take ba, haka tayi ta kalle kalle abinta.
Mamy ce ta katseta ta hanyar cewa ki fara da ɗakina, ta nuna mata corridor ɗin da ke ɗauke da ƙofofi kusan hudu, dama 2, hagu biyu,
"Ɗaki na karshe daga dama ne nawa, so shi kawai zaki gyara da toilet sai kuma nan"
Toh tace ta ɗauki kayan aikin ta nufi ɗakin.
Da shiganta ɗakin wani irin sassanyan ƙamshi ya bigi hancinta, ido ta lumshe tana furta Mashaa Allah ƙasa ƙasa.
Ɗakin ta karewa kallo ya haɗu, haka ta gyara shi tsaff, duk da daman sai kayi tunanin ma ba a kwanta a ciki ba, gaskiya ita da kanta ta jinjina tsaftar mamy, haka da ta shiga toilet ɗin, dole ta zuba ƙauyancinta son ranta tunda tasan ba me kallon ta daman mazewa kawai take, ta gama ƴan taɓe-taɓenta, ta wanke shi tsaff ta fito.
Sannu mamy tayi mata, tana shi mata albarka da ta shigo taga yanda ta gyara mata ɗakin kamar yanda takeso, ba buƙatar saita ƙara gyarawa ko tasa Zuhura tayi mata.
Parlour ta fita nan ma ta gyara shi, ta sanya turaren wuta, sannan taje ƙofar ɗakin mamy tayi knocking.
Izinin shiga ta bata dan haka ta shiga da sallama.
Zaune ta sameta a bakin gado, daga bakin ƙofa ta tsaya ta ɗan duƙa tace "Hajiya an gama sai kuma ina?"
"Shikenan kije ki huta"
Godiya ta mata tare da ja mata ƙofa ɗakin.
★★★
Bayan ta sauka ta tsaftace duk abinda tasan tayi amfani dashi, ta maidasu ma’ajinsu.
Saita koma kitchen wajen su iya, wannan karan ma dai still haka su dije suke binta da ido.
Sannun ku da aiki kawai tace masu, ba tare da ta tsaya sauraren amsansu ba, tayi gaba wajen da iya take.
Nan suka samu abinyi, daman ashe tun jiya suke gulmar ta, an kawo mai aiki kyakkyawa kuma ga dukkan alamu ta samu karɓuwa a qurin masu gidan, duk da sunsan daman mutanen basu da wulaƙanci, amma gani suke kamar sunfi nuna zumuɗin ta yaran gidan, kuma daga ganinta zatayi girman kai.
Sahura ce ta taɓe baki tace "ni wallahi gaba ɗaya ma batayi min ba, kallo ɗaya nayi mata naji na tsaneta"
Dije tace "Hmmn ke kike faɗima wani naji"
Haka sukayita yi da ita, wanda ita batama san sunayi ba.
Kusa da Iya Lami taje tana faɗin "Iya, nagama sai kuma me"
Iya tace, "Kije kawai kiyi wanka, sai kici abinci ki huta kafin anjima in za ayi ma Hajiya wani aikin, ki wuce da abincinki kuma" ta faɗa tana nuna mata inda ta aje mata abincin.
"Nagode sosai iya"
Murmushi Iya tayi a fili a ranta kuma tana yaba tarbiyyan yarinyar da natsuwanta, duk da dai daga ganinta zatayi miskilanci.....
FULANI
08082101373
https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr?mode=gi_t

✨🦋 RANTSATSTSEN RABO ✨🦋
BY RABI'ATU KABIR ACHADU (FULANI)
YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION YOTA
SADAUKARWA GARE KI HALIMA HASHEEM (MIEMIEN HABIBI)❤️& AHMAD JAMIL AHMAD (HABIBI)♥️
FULANI ❣️
08082101373
PAGE 1️⃣4️⃣
Ɗaki ta wuce tana shiga babanta ta fara kira Suka gaisa, tambayar ta yayi sabon waje, jin zatayi mishi kuka, yace ta bari zai kirata anjima, Duk da haka saida ta share ɗan guntun hawaye sannan ta tashi ta shiga wanka.
Bayan tayi wankan ta zauna ta shirya sannan tayi zaman yin karin kumallo, bata wani ci sosai ba duk da abubuwan sun yi daɗi kuma wasu ma yau ta fara cin su, haka ta tashi ta maida sauran kitchen.
"Badai har kin ci ba?" Cewar iya ganin ta dawo da kusan rabin abincin.
"Eh Iya naƙoshi alhamdulillah"
"Toh ai bakici da yawa ba, ko ba ki sonsu ne a baki wani abun?"
"A'a nagode ya isheni"
Aishikenam daga haka ta ci gaba da aikin ta.
Kallon iya tayi tace "Maizan taya ku dashi?"
"Ai da kinje kin huta kin sha aiki"
"A'a, ai zaman ba daɗi ne" tayi maganar cikin sanyinta.
"Haka ne, kuma to ga kayan lambu can ki wanke, sai ki gyara su"
Amsa tayi tana nufan inda kayan suke, ta ɗauka ta nufi famfon da ta gani cikin kitchen (sink), kunnawa tayi ta wanke su tsaff, sannan ta nemi waje ta zauna ta fara aikinta cike da tsabta, duk abinda take iya na hankalce da ita kuma ta yaba ma tsaftarta.
Haka ta gyarasu, ta yanka su gwanin ban sha’awa, suna cikin aikin ne, mamy ta kira iya a landline ɗin kitchen ɗin tace ta turo mata maryamah.
Bayan iya ta aje wayar tace, mata ta aje abinda take, taje hajiya na kiranta.
To tace, ta wanke hannunta tana nufan ƙofar fita daga kitchen ɗin, yayinda su dije da Sahura suka bita da ido suna magana ƙasa-kasa da gani dai gulmanta suke yi.
Girgiza kai iya tayi tana jiran azo gabar da zatayi masu magana, dan taga kamar zasu hade ma yarinyar kai.
★★★
Da sallaman ta ta shiga parlour, ta samu hajiya da malam Sale zaune, cikin hanzari ta ƙarasa gare shi tana faɗaɗa murmushin fuskanta, dan ganin shi take kamar wani ƙani ko yayan mahaifinta.
Shima da murmushi a fuskar shi yake tsokanar ta cike da jin daɗin ganin ta "inyee kaga maryaamah babanta"
Wani murmushin ta ƙara saki tana ƙasa da kanta, kusa da ƙafarshi ta zauna "Baba ashe kaine kazo ina yini?"
"Lafiya lau, alhamdulillah, Maryamah ya baƙunta?"
Alhamdulillah kawai tace mishi.
"Nasan ai kunyi waya da babanki ko?"
"Eh yace ma zai ƙara kirana"
"Da kyau daman zuwa nayi muyi sallama, yau zan wuce gida"
Sosai ta ɓata fuska "ayya baba tun yau" taff idonta ya ciko da hawaye.
Mamy dake gefe tace, "Kedai Allah yayi miki arhar hawaye"
Ƴar dariya malam yayi yace "ai indai Maryamah ce, zaki gaji da gani, dan farin ciki ma ita kuka take mishi"
Da haka ya mike "Toh hajiya ni zan tafi, duk halin da ake ciki sai a sanar dani ta waya, gata nan in tayi ba daidai ba a tsawatar mata dan Allah"
Cike da dattako ta bashi amsa "Bakomi wallahi ni nama yaba da natsuwanta wallahi tun jiya, Sannan maganar makaranta, ina ganin zamu bari first term sai a akaita, tunda kaga yanzun muna 3rd term ne, kuma ba a da6de da shiga ba, Idan yaso sai a saman mata JSCE certificate, sai ta jona SS1 kawai"
"Shikenan ba laifi hakan ma mun gode, Allah ya ƙara girma"
Kuɗi ta bashi tace yayi kuɗin mota, sannan in ya koma sunyi magana da mahaifin Maryamah, sai su faɗi a inda ya kamata a ringa sanya mata kuɗin aikin.
Tohm inshaa Allah zaiji da haka ya fita yana ƙara mata godiya, Ita kuma Maryamah tana biye dashi.
Saida suka fita farfajiyar gidan, sannan ya tsaya ya juyo yana kallon ta, tsaya daga nan ba sai ta kaishi da nisa ba, gidan nada faɗi, kada ta dawo ta rasa inda zata shiga.
Kallonta yayi yace, “To Maryamah, kinga inda rayuwa ta kawo ki, ina fatan kiyi amfani da damarki ta hanya mai kyau, ki zauna da kowa da zuciya ɗaya, sannan ki kauda kanki daga duk abinda be kasance naki ba, sanan banda rawar kai duk da daman ban sanki da ita ba, sanann ki tsare mutuncin ki kinji, koh kuma ki cigaba da muraja’ar karatunki, nasan in Allah ya yarda, hajiya duka zata sanya ki islamiyya da boko"
"Inshaa Allahu baba zanyi amfani da duk shawaran da ka bani, bazakaji wani labari mara daɗi ba daga gareni, zanyi abun6da ya dace" tayi maganar tana share hawaye.
"Yauwa ki kwantar da hankalinki, kinji koh, kidena ƴan koke-koken da kike kisa a ranki, dan kwanciyar hankalin mahaifinki kema zaki kwantar da hankalinki a nan har ki cimma nasararki ta rayuwa"
"Inshaa Allah baba nagode, Allah ya kiyaye hanya ya kaika gida lafiya"
Ameen ya amsa yana miƙo mata kuɗi cikin envelope.