← Book details Rabon Kwado Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 24

Sashe 7

Rabon Kwado Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sewajan 9 da wani abu su muhammad suka shiga inda aka sauki su mummy yanata zalkin ganin amaryarsa,sam barka kuwa yahangeta jikin mummy anata rarrashi, soyake kawae ya rarrashi abarsa amma babu hali tana gun mummy,seda suka zauna tukunna mummy tace muhammad gara dakuka shigo yanzun munkasa shawo kan meenal, kazo kaji da ita don Allah, muhammad yay murmushi yataso yazauna gefenta yana cewa haba sweetie meyasa zakiyita wahalar dasu mummy ki fawwalawa allah komae kinji duk yadda kikaga bawa haka allah yatsara masa, toke seki godewa allah kinji bakuka zakiyiba kada kuma ki kuskura kisawa zuciyanki maraeniyace ke ko kadan karki fara,

Zuwa lokacin kukan meenal ya tsananta yanzu dagaskendae wanda taji ana ambata shine mahaifinta meyasa aka boye mata kam,koda muhammad yadagota rintse idanunta tayi gam tana shahshsekar kuka, itadae mummy tasamu tamike tashiga toilet don mararta acike take, hakanne yabawa muhammad damar janye meenal daga room din, mimi tayi tsamo da ita don inda take mujaheed be kallaba hasana baki sake kuwa take kallon ikon rabbi, takasa dena kallon meenal yanzu dama bada yayarsu suke rayuwaba wannan wani irin abin mamakine haka?

TAKU A KULLUM NANA BMB.

08147110349
[8/31, 3:39 PM] Nana BMB: 🤍💞🤍💞
RABON KWADO....

BOOK 3

💕💕💕💕💕

NA NANA BMB.
🤍❤️🤍❤️

page 15 - 16
Muhammad da meenal suna zaune kan steps, ba fita sukayi ba,kunshin hannun ta yaketa shafawa don bakara min tafiya da imanin sa yayi bah, ita kuwa inbanda shashe kan kuka babu abin da takeyi,gajiya yayi da kukan nata ya kwanto da ita kan shoulder dinsa, yana mata kalami masu dadi yana rarrashin ta, se a lokacin ta dago tazuba masa dara daran idanunta cikin kuka tace.

"Ya muhammad why! why! meyasa haka zata kasance dani? koda wasa ban taba tsamma nin hakaba a rayuwata wlh yanzun nadena ganin laifin auntie abinda takeyi min ashe ba ita ta haifeni ba ina zansa rayuwata Ya muhammad"
Cikin tsananin tausayi yasoma share mata hawaye yana gogewa wani nabi masa hannu takasa dena kuka,
Cikin damuwa yace pls meenal enough of d tears ok,yana maganar yana me dago habarta ya zuba mata idanu yana hadiyan wani yawo dake tsaya masa a wuya, lips dinta kawai ya zubawa idanu jiyake dama yamasa shan lollipop amma badama, saboda meenal batasan komaiba akan aurensu, ga ni imtaccen kamshin dake tashi ajikin ta yana rikitashi dayawa, gajiya tayi da rike mata haba dayayi ta jaye hannunsa ta kwan tar da kanta akan damtsen hannunsa,beyi kasa a gwiwaba yacigaba da rarrashin ta har yasamu tayi shiru sedai ambaliyan hawaye datake ta faman yi, suna cikin wannan halinne suka soma jiyo ruwan bala in mujaheed daga samansu,ay basusan sanda suka mikeba suka nufi saman don kanajin wannan kasan ba lafiyaba,

"Meyasa kikayi min wasa da zuciya?
Shin meyasa kika rainamin hankali har haka? Tunda nake bawanda yataba min irin wannan rainin hankalin seke"
Magana yake cikin hargagi da tsananin bacin rai, meyasa bakiyi min bayani ba tunda muka tsinceki? dayanzu ban tsaneki hakaba, ko ganinki bana sonyi,
muhammad yafini gaskiya da kallo daya yayi miki yagane bake bace meenal,meyasa ni nakasa ganeki?

"Ki fadamin abinda kikayi min hakane? da idanuna suka rufe"
Yana maganar tamkar ze rufeta da duka gashi ya tsareda da jajayen idanunsa wanda suka rikide da ruwan bala ei,

Kukan mimi ne kawae yake tashi a gurin nan me taba zuciyan me sauraro sam yaki bata damar maganama yanata zazzaga mata masifa,

"Wai meyasa kika amshi soyayyata?taya zaki barni nayi nisa a soyayyane taya"
Cikin takaici yake wannan maganar, mimi kuwa cikin shashe ka tace.

" Am so sorry yaya na amma kasani soyayyata gaskiya ce san nakane ya hanani yimaka bayani nakasa controlling kaina akanka ban taba yiwa wani Da namiji son da nake yi maka ba ayanzu, kaine nafarko wanda zuciyanta tafara aminta da...."Kiyimin shiru!" mujaheed yafada cikin daga murya,Toni bana kaunarki hasali ma ko ganinki bana sonyi saura kwana uku a daura miki aure don rashin mutumci shine zaki tsaya kina gayamin maganar banza,
Cikin kuka mimi tadora hannunta kan nashi tana cewa kayi hakuri kamanta da maganar auren nan ni kai nakeso yanzu,kamanta kayimin al kawarin kome yafaru bazaka juyamin bayaba zamu kasance atare, to meyasa kuma yanzu zakayimin haka? meyasa? ka gayamin,
Cikin takaici yajanye hannunsa yace ni meenal nayiwa al kawari ba keba, so kisan me kikeyi yanzu kinji koh!

Durkushe wa mimi tayi a gabansa tana dafe zuciyan ta tana kuka me cin rai, zuwa lokacin duka 'yan dakin su mummy seda suka fito jin haya gagan na mujaheed yayi yawa, ga muhammad tsaye da meenal suna masa kallon mamaki wanda yasa duk suka kasa cemasa komae, dukkanin abinda yake faruwa bassam da abbansu suna daga bayansu suna kallon abinda yake faruwa wanda bassam dinne kadai dafarko yafara zuwa don kiran su hasana yaci karo da abinda yadaga masa hankali yakuwa kira Abbansu shima yazo yaganewa idonsa,hawaye masu zafine suke saukowa daga idanun bassam jiyake kamar yahadiye zuciya yamutu,jiki a sanyaye ya tako yazo inda take a sunkuyen ya dagota idanunsa na zubda hawaye murya a raunane yace.

" Shin nikuwa mimi mena aikata miki haka a rayuwa dabakya kaunata haka? inasonki kamar namutu akanki amma meyasa zakiyi min irin wannan sakayya? meyasa zakiso wanda baya sonki baya son ganin ki? kina ganin kinyi min adalci kenan kosau daya kin taba tunanin halinda zanshiga kuwa idan narasaki?

" Kayi hakuri ya bassam bayin kaina bane Allah ne yadasa min sonsa a zuciyata har nakejin bazan iya rayuwa bah inba shi,kate maki rayuwa ta ya bassam kace kafasa aurena tun farko kasan bana sonka iyaye na nakewa biyyaya"

Cikin wani irin yanayi bassam yasoma jada baya yana girgiza mata yana rintse idanunsa cikin bakin ciki,matsoshi takumayi tarikeshi tana kuka tana yimasa magiya, hakan ne yakara sa mujaheed kuma hassala in banda harara babu abinda yake antaya musu,

Mimi bata ankara da Abban su bah se gani tayi yajanye bassam yana me cewa kada ka tashi han kalinka bassam wannan auren baze fasuba seka aureta yaja hannunsa suka tafi suka bar mimi cikin mawuya cin hali....

TAKU A KULLUM NANA BMB.

08147110349
[8/31, 3:39 PM] Nana BMB: ❣️RABON KWADO....!!

BOOK 3

NA NANA BMB

GARKUWA WRITTER'S ASSOCIATION
{ Marubuta masu garkuwa da al kalami domin fadakar da al'ummah}

page 21 - 22

Kallon mamaki general kawai yake wa dan nasa, ita kuwa ganinsu ne yasa ta juyawa tabar gurin tana kuka! shikuwa kallon da yaga mahaifin nasa yana masa ne yasa zuciyan sa karaya don yasan akwai magana a wan nan kallon,

Washe gari
Yau takama ranar yankewa su bassam hukunci don kowa ya amsa laifinsa batare da sun wahalar da shari ah ba, shi bassam dama general yakawo shedu akan sa na temakon mimi da yayi, wannan dalilin ne yasa aka sas sauta masa nasa hukuncin, zeyi shekara 2 a gidan maza batare da beli bah,balaraba da asiya kuwa shekara 5 ne suma zasuyi babu beli kowa yana Allah wadai da wan nan halin nasu,
Mimi tana jikin ummi tanata kuka tawani bangaren tanajin dadi da Allah yaraba ta da kadda rarren auren bassam da bata so,haka itama tana sharar kwallah bakowa take tausayi bah se bassam,

Hasana sosai take tausayin bassam a yaunzu, mussam man dataga yadda yaketa ambaliyan hawaye, zafi zuciyansa take masa da kuna,
Seda aka gama yanke hukunci taron mutane ya watse shari ar tasu tazo karshe,inkaga kanwar bassam seta baka tausayi yadda takoma tayi kuka kamar zata mutu ga yanzu kuma da dukansu an dauke matasu ba uwa ba kaka ba yaya tamkar zata zare se fita akayi da ita aka nufi gida tunkan agama shari ar mah,
Mimi tunda suka fito tazubawa mujaheed idanu sede sam yaki kallon inda take tun hatsa niyarsu bekara kulataba kuma abin yanayi mata, to itama nana sam batako kalli inda yousep yakeba donjiya yashaka mata dayawa,meenal tana gidan batasan wainar da ake toyawa bama haka auntie,
Kiran da Abbansu yama mimi ne yasata isa gareshi da hanzari yakama hannun ta suka koma ciki, bassam tasamu a zaune shida general cikin office din dasuka shiga haryanzu a daure yake da anchor jiki a sabule tazauna gefen Abban nasu kanta yana kasa, yace.

"Mimi haryanzu kicigaba da kallon bassam a matsayin wanda zaki aura wannan abun daya faru bazesa najanye kudiri naba"
cikin wani irin firgici mimi tamike hannuwa biyu tazube a kirji tadafe shi saboda irin bugawar dayake yi mata,se hawaye shar!
Ganin hakanne yasa bassam yataso izuwa gareta cikin wani irin yanayi yake kallonta kana yace.

"Mimi idan nahakura da aurenki nabarwa mujaheed ke zaki yafe min? kitemaka kiyafe min mimi" yana maganar shima yana hawaye,
Kallonshi tayi na dan lokaci san nan tadaga masa kai, juyawa yayi ya tsugunna gaban Abbansu cikin sanyin murya yace.

"Abbah ina neman al farma a gareka"

"Ina saurarenka bassam"

Seda yasauke ajiyan zuciya yace." nahakura da mimi Abbah tunda batasona nahakura alfar mar danake nema kuma Abbah kate maka kabawa mimi wanda takeso idan kayi min hakan kagama min komai a rayuwa,hakan shine zebawa mimi farin ciki har a bada idan takasan ce da masoyin ta, idan na aureta na tauye mata farin ciki mujaheed yana tsananin kaunar mimi shima saboda ganina ne yasashi boye nashi son,kayarda dani Abbah idan kayi haka nasan mimi zata yafemin abin da namata katemaka Abbah, kada kaji tsoron bawa kado auren 'yarka saboda kafini sanin halin dattakonsu sunada amana kada abinda yafaru damu yasa kayi tunanin duka haka suke, kai Allah yaha daka da mutane nagari,"

Tunda yafara maganar Abbah shiru kawai yayi yazuba masa idanu yana tausayin bassam yasan karfin haline kawai yakeyi don shikadai yasan abinda yakeji a zuciyansa dafashi yayi yace,
"Shikenan bassam tunda kahakura dakanka babu komai, alfarmar dakane ma kuma insha Allah zanyi maka ita," hannunsa bassam yarike yace.
"Abbah inason ganin wan nan dauren auren kafin natafi katemaka Abbah kada ka ce a ah hakanne zebani karfin gwiwan yin rayuwa cikin salama a prison"
Kallonshi Abbah yayi dakyau san nan yace.
"Indai sun amince zasubi al'adarmu bassam meze hana"
Mikewa general yayi yace .

"Aminta kamar sunyita ne sungama kada kadamu da wan nan bassam a yau din nan zamuyi maka abinda kakeso,yau insha Allah za ah daura auren mimi kuma za ah hada dayarona yousep dakuma 'yar gidan Alhj.Abubakar"
Chapter 7 · 0% Book details