← Book details Rabon Kwado Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 24

Sashe 13

Rabon Kwado Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Meenal ta kawata murmushin fuskanta tace.
" Aydama da ita suke soyayya bani bace"
"What!"
Sameer yafada yaname mikewa tsaye don zuwa yanzun abin yasoma fin karfin kansa sosai ya zubawa mimi idanu haka su mom ita inty tama kasa cewa kala,harara yashiga wurgawa mujaheed yace.
"Wlh ka kiyayi haduwan mu bakin mara mutumci kabar mutane a duhu kaki gaya mana abin da yake faruwa saboda yanzu kasoma canza halayenka"
" Kaifa dadi nah dakai gajen hakuri kabari mana kahuta komai dayake faruwa yau zaka sani ay kwan tarda hankalin ka" mujaheed yace dashi gami da mikewa yaje ze anshi affan a hannun mimi yana cewa." bani baby boy dina mu gaisa tunda bansamu na halacci suna bah baby haryayi wayau" saurin rike masa hannu sameer yay yace

" kaga kuwa bazaka daukeshi bah saboda bakaje tayashi murnar zuwa duniya bah don haka fushi yake dakai harda ni ubansa ehe!"

Muhammad yana murmushi ya taso ya ture mujaheed gefe yace. "kunfi kusa nidai tunda banyi laifin komai bah abani shi mugaisa"
Mimi tana murmushi ta mika masa shi ya ansa,sosai mujaheed yake dariya ganin yadda sameer ya cukurkude fuska yarike haba yana cewa.

"Haba sameer yanzu sokake ayi mana dariya dama kasan muhammad kadan yake jira,haka zamuyi dakai?"
" Eh haka zamuyi bamu ma fara bah" cewar sameer kenan.

Gyara tsai warsa mujaheed yayi yace."To indai hakane shima muhammad yama laifi don yariga ni yin aure ma" baki sake yake kallon muhammad shima tunkan yace wani abu yatari numfashin sa

"Kasan dai halin mujaheed hadamu yakesonyi danayi dabaka ganiba"

Guntun tsaki kawai sameer yay yace."kwaji da gulmarku wlh anjima dai koma meye magani nizaku mayar dan iska, to bazan lamin taba gara nayi wankana na huta zuwa anjima nasha kallo" suduka suke dariya mujaheed yabishi a baya,
fitowansa daga wanka kenan muhammad yashigo da affan yana hannunsa yana masa wasa, shikuwa mujaheed zaunarda sameer yay yazayyane masa duka abubuwan dasuka faru,gamida auren muhammad da meenal,yasanar masa dama rainonta sukeyi ba a cikin family dinsu takeba asalin family dinta sune na adamawa, da batan meenal Allah yakawo musu mimi a matsayinta, sosai jikin sameer yay sanyi dajin wan nan labarin yace.
" Haba no wonder lokacin nurses sukace mana olcer yakamata saboda rashin abinci gaba daya wan nan raunukan nata dole muna tai musu kallon mahaukata, to kai mujaheed Allah ne fah yadubeka yakawo maka mimi cikin rayuwarka saboda yasan meenal ba rabon ka bace ay ita zuwanta rahama ne a gareka,sekayita mika godiyar ka ga Allah dayin Alfahari da ita"

Caraf muhammad yace, yafayi hakan! ay wan nan bashida kirki dakake ganinsa tunda yasan kowa cece ita yake shuka mata rashin mutumci iri iri! ingaya maka,kuma dan iskan randa aka daura auren nan seda yanuna wa 'yar mutane tashin ta ido a garden,mutumin nan bashi yashigo dakiba sewajan 12 dukya bi ya.... Dukan da mujaheed yakai masane yasashi yin shiru yana hararar sa,
Cikin dariya mujaheed yace "wan nan abu ya tsone maka ido muhammad ina ruwan kane tunda aka rigada aka daura auren nan badole nayi hakuri nadau kaddaraba"

Da hannu biyu sameer yarike baki yana kallon muna finci irinna mujahhed, seda yakare zancensa yace."Gaskiya mujaheed kama raina mata hankali Allah sarki wlh harta bani tausayi"

"Kai dai bari! sameer yarin yar ga hakuri shiru shiru da ita Allah ya hadata da rigimam men miji"

Sameer yaceda muhammad. "Barshi zamuyi maganin shi ay mune dai dai dashi"

Dariya harda tin tsirawa mujaheed yakeyi yace." Aikin gama yagama sameer tunda aka riga aka daura aure se yadda nayi da amaryata ehe!"

To mimi ma dai duka abinda yafaru tagayawa su mom harda batun auren meenal da muhammad,ita kuma a time din ta tafi kiran auntie domin su gaisa dasu mom din, sunyi mamakin wa nan lamarin sosai da sosai,

Koda meenal tashiga bedroom din na aunty tasameta fitowanta kenan daga wanka tashaida mata abinda yakawota,
Kallonta auntien kawai takeyi tana tsane jikinta da towel sosai take mamakin sauyawar meenal a gareta sam bata ta ita yanzu sabgarta kawai takeyi,
Cikin isasshiyar muryarta tace.

"Meenal saboda yanzu kinji bani bace mahaifiyarki nida banza yanzu duk daya a gurin ki koh! babu abinda yadame ki dani,yanzu ummi itace babarki bani bah"

Tuni hawaye yasoma bin fuskar meenal kanta a sunkuye seda takare maganar ta tace.

" Auntie harna mutu bazan dena ganin ki matsayin uwa bah saboda koba komai baki taba goran tamin akan iyaye bah a haka kike zaune dani sam nadena ganin laifinki a yanzu yadda kike nunawa yaya kauna, nafi tunanin Daddy yay miki tilas ne akan rikona kuma kinyi kokari zanyi alfahari dake kuma akoda yaushe abu daya na rasa a rayuwata shine soyayyar mahaifiya! sam bansan wan nan ba seda Allah yakaini adamawa,soyayyar da ummi kemin ce ta hanani dawowa gidan nan sekuma Allah yazo yay ikonsa gaskiya ta bayyana, nadena ganin laifinki yanzu auntie ina matukar tausayin rayuwata a yanzu dukda zafin be hade min bah lokaci daya, Alokacin da nasan wacece ni Allah yasa ina cikin dangina koyaunzu Alhmdlh, da hakanma auntie kada kiyi tunanin zan rikeki a zuci ko kadan"

Tana kaiwa karshen zancenta tafice tabata guri taname zubar hawaye,kalamanta sun shigi Dr sosai to amma zuciyanta sam taki karaya dama a sama take tun jiya take sababin masifa Daddy ya tsallake komai yatafi dubai yace abu na gaggawa ze kaishi seyau ze dawo komai yasakar mata a hannunta ita ke kujuba kujuba....

TAKU A KULLUM NANA BMB

08147110349
[8/31, 3:39 PM] Nana BMB: ❣ RABON KWADO....!!

BOOK 3

NA NANA BMB

GARKUWA WRITTER'S ASSOCIATION
{ Marubuta masu garkuwa da alkalami domin fadakar da al'ummah }

page 35 - 36

Da gudu tawuce su tahaura sama har cikin bedroom dinsu, cikin tashin hankali take bincike kayanta har ta dauko takaddar auren nasu, jikinta har karkarwa yakeyi tabude tasoma karan tawa tana gamawa ta silale akasa tana dafe kanta sam tarasa wani irin yanayi take ciki,
Nana da mimi suna ta faman cire kayan adon da akayi musu duka suka tsaya suna kallon ta,
" Tayaya! how! yaza ayi ya muhammad yazama mijina? sam bazan iya haka bah, wayyo Allah nah! wanda nadauka yaya na shine za ah cemin mijina, taya zan iya rayuwar aure dashi?" dafe zuciyanta tayi saboda yadda take bugawa,
mimi dariya harda fadawa kan bed,

Karfin halin mikewa tayi ta isa gurin da nana take tsaye cikin firgici ta cakume tah hannu na ta bari tace." Yaya! kada kicemin dagaske ne don Allah kurafamin asiri, nashiga ukuna! taya ya muhammad ze zama mijina? wlh bazan iyaba sam bakuyimin adalci bah"

Nana ganin yadda meenal ta firgice dayawane yasata danne tata dariyar tace.

" Meenal nimafa nashiga rudani gaskiya,dakyar ne in hakan dagas kene maza kije ki gaya masa abin da yake faruwa suna garden, koda bakinsa ya gaya miki?"

Saurin girgiza mata kai meenal tayi alamun a ah,

"To maza kije kisamesa mana, yaudai komai yazo karshe a wuce gurin gara kidena tan tama koh gara dai kiga mijin nan naki yau, koba hakaba?"
Kamar sauna meenal take daga mata kai,seyanzun take danjin sanyi a zuciyan ta.

Sakin nana tayi jiki a sake taje ta bude window dakin sam barka kuwa ta hango shi shida su mujaheed a garden sunata arere warsu, kafa menaci ban baka bah, tayi waje da gudu don sam takasa yarda da abinda ke faruwa gara taji daga bakinsa,

Koda fitar ta nana tasoma dariya harda rike ciki da hawaye tana cewa mimi " Yau mutuniyar drama tazo karshe zamuga a yanayin dazata dawo mana kuma 😅"

Zuwa lokacin mimi murmushi tayi saboda moment dinsu daya dawo mata itada gogan nata mujaheed.

Muhammad yana zaune yaharde kafa, cikin kayansa na shan iska marasa nauyi,hannunsa daukeda glass cup yana shan juice, anata hira shikuwa yakurawa cup din hannunsa idanu yayi shiru.

" Wai ango lafiya dai? naganka cikin wani yanayi haka" fahad yay masa wan nan tambayar cikeda mamaki saboda yaga yanzu ake hira dashi harda dariya

" Inafa lafiya! amarya batasan waye angon taba har yanzu,shikuma ango gaba daya yanacin tsaka me wuya soyake...." Maganar mujaheed ce tamakale saboda kallon da muhammad ya masa, shikuma mamaki ne yasashi yin shiru ganin yadda idanun na muhammad suka sauya a dan kan kanin lokaci.

" Ay gara shi dai sau dubu wlh yafika yanada tawakalli, kaikuwa ay sedai a shafa fatiha a tashi" sameer yay maganar yana antaya wa mujaheed din harara,

Kusa da muhammad mujaheed ya matsa, yadafashi yace." Shin sai yaushe game din nan naku ze karene? muhammad tunda meenal taki duba takaddar kasanar mata mana! kaje mata a matsayin miji ba yayan taba"

Kallon mujaheed din yayi yana murmushi yace." Wani zuwane ya wuce wan nan? Aita sani yanzu"

Kallon rashin yadda mujaheed yamasa harda harara, ganin hakanne yasashi guntuwar dariya yace." To juya ka gani"

Saurin juyawa mujaheed yay sukayi 4 eyes da meenal tana tsaye kamar an dasata a gun, shikuwa yasaka dariya yamike yana cewa " Aww kace game over! bari to nayi daga ciki ni" suduka abokan nasu sukabi bayan mujaheed suna guntse dariya saboda irin kallon da meenal takewa kowan nensu.

Bayan wasu 'yan sakanni muhammad ya aje glass cup din hannun sa yamike yazo har inda take tsaye, zuwa lokacin bugun zuciyan ta ya karu saboda yaudin wani irin kwarjini taga yayan nata yayi mata setaga kamar bashiba saboda yadda yake kallonta, lokaci daya tsoronshi ya dirar mata da fargaba,
Saurin sunkuyar dakanta tayi kasa don bazata iya kallonsa ba kam,murya tana karkarwa tasoma cewa.

" Ya muhammad wai.... Kasa karasa maganar tayi saboda tayi mata nauyi gurin furtawa, hannu yasa yadago habarta cikin wani kalan voice dabata tabaji nasaba yace.
" tell me"

Tuni ta kulle idanunta don bazata iya kallonsa bah, shikuwa yasami abinyi yakura mata idanu mussam man pink lips dinta,

Hawaye nabin gefen face dinta tace " Ya muhammad wlh bazan iyaba taya hakan ze kasance kai yaya nane!"

" An miki auren dole koh"
Chapter 13 · 0% Book details