← Book details Rabon Kwado Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 24

Sashe 5

Rabon Kwado Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read

NA NANA BMB.
🤍❤️🤍❤️
page 10-11
Sebayan 'yan mintuna dasuka shude tukunnah ummi tasauko fuskarta daukeda fara ah tunkan tazauna meenal ta cinmata tana cewa ummi meya faru ne don allah kigayamin,ummi tayi murmushi takalli bassam tace kaje kasanarwa da family you munada manyan baki a gidannan,shima haka yatashi cikeda mamaki yafice, meenal takara rike mata hannu tace suwaye zasuzo ummi?kigayamin,itadae kallonta kawae take tana zuba murmushi tace bakine zasuzo mana kuje ma kubada oder irin girkin daza a fara yanzun kibar komae se idan sunzo zaki ga komae, itadae meenal addu ah kawae take allah yasa tunaninta yazamo gaskiya,tashi tayi don cika umarnin na ummi,
Tafiya tayi tafiya su muhammad bakaramin gudu suka shararaba kafin su iso cikin garin yola,mimi itace take musu jagoran tafiya ayanzu har suka iso GIDAN FULANI,anan tunanin kowa yasoma zama abin mamaki da aljabi mimi dakanta tafito tayiwa securities magana sannan aka bude musu gate suka wuce, zuwa gate na biyu anan aka bincikesu tas sannan sannan suka wuce bakin kowa asake da mamaki suketabin gidan da kallo, har parking space takaesu suka aje motan nasu sedae kowa yakasa fitowa acikin motar se mimi kadae data fito cike da farin ciki dajin dadi ko ina takebi da ido kobakomae tayi missing gidansu matuka gaya, muhammad ne yafara fitowa yazo gurin mimi zeyi mata magana ashe mujaheed yafito shima cikin jin haushi yace waekae meyake faruwane wannan wani irin gidane ko ince gari donyafi karfin gida wannan mezamuyi anan? muhammad yay murmushi batareda ya tanka masaba haka mimi adae dae time din bassam yafito daga bangarensu nasu mimi yanata balbalin bala ei da alamu shida hasana ne, cikin tsatstsan farin ciki mimi takwala masa kira,YA BASSAM! koda bassam yaji wannan kiran seya tsaya cak kamar baze waigowaba sekuma yajuyo ahankali yadora idanunsa akansu yakasa tantance wadda yake gani saboda 'yar tazararsu hakanne yasashi tunkaraso itama mimi tanufeshi harda gudunta, tana karasawa tarike masa hannu da yakuwa rintse idanunsa yaname cewa Oh! allah my meems gizo kuma kika farayimin yanzu,cikin dariya mimi tace bagizo nake makaba nice mimice take maka magana kabude idanunka ka ganni dakyau,cikin firgici bassam kuwa yaware idanunsa akanta don bashakka wannan muryar ta kalbinshi ce ba tantama dafe zuciyansa yayi kawae yaja baya yaname kallonta cikeda da rashin fahimta ko zurfafa tunaninsa yakasa, tsoro sosae yashigesa tace ya bassam shin kundrna tarbar bakone yanzu agidannan cikin in ina bassam yace bari nakirasu jiki nabari yajuya yana waigen mimi don atunaninshi wannan anya ba aljana bace mekama da mimi saboda yanzu yagadae yabarsu agida yafito,
Ganin hakanne yasasu daddy fitowa daga cikin mota dasu auntie al ummar data soma fitowa daga cikin gidanne yakara daure musu kae tako ina mutanene suke bullowa,
Mimi asanda tayi arba da ummi ya ilahil alamin! cikin wani irin gudu mimi tanufeta taje ta daneta btasan tafara kukan farin ciki bama, I MISS U I MISS U I MISS U I MISS U!ummi ashe darabon nakara sakaki a idanuna ummi nayi kewanki sosae ummi,cikin wani irin farin ciki mara misaltuwa ummi tayiwa mimi kyakkyawar runguma tana zubar da hawayen jin dadi tana zuba addu ah ga ubangini daya dawo mata da diyarta lpy,kowa TV yamaidasu agurin nan, adae dae lokacin hasana tafito da meenal bassam yariko hannun twins,zuwa lokacin mamakin bassam yagama karewa kallon meenal kawae yake,asanda mimi tadago kuwa suka hada ido da meenal jiki nabari tasaki ummi taikanta tarukumkumeta tana ya allah meenal ashe darabon zamu gana, wannan abun kamar a mafarki ya allah kaene kadae kasan nufinka dakayi haka, meenal kallonta take tanata yashe baki yaki rufuwa addu arta ta amsu shikenan tarabu da gallababben auren nan na mimi zata koma gida duka azuciyanta take wannan tunanin,cikin farin ciki tace Oh allah abin godiya shin kina ina kekuwa duk wannan lokacin?mimi tasaki murmushi tarike mata hannu suka nufi inda su muhammad suke tsaye sudukansu,wayyo ay meenal wata fincika tayiwa hanunta saura kadan tayarda mimi akasa cikin gudunta nabara tafellah, tana kwalawa yayan nata kira YA MUHAMMAD! muryanta kuwa gaba daya seda taratsa ilahirin jikin sa ya lumshe idanunsa yaushe rabon duniya da ayyare dayaji muryar sweetiansa, cikin tsananin farin ciki muhammad yasoma zubawa allah godiya seda takusa karasowa kuwa ya isa gareta cak yacafe abarsa sama yana juyata cikin nishadin dabesan yanayibama,(da alamu yamanta dasu daddy) meenal tana dariya ahankali yasauketa takarasa fadowa jikinshi yay mata kyakkyawan rumguma kuwa sosae taji yadda yake sauke ajiyan zuciya, idanun jama ah kamar ze fado kansu don sun burge kowa dake gurin,sunkuyawa yayi yasoma yimata rada akunne yana cewa sweetie haka kika koma masha allah!cikin jin kunya tace ya muhammd haka ka koma kaema gaba daya kasauyamin,yasaki 'yar karamar dariya yace bawani zaki wayance kinji nace kingirma koh kema irin ta yaya ta yaya kin girma kin fara....Toshe masa baki meenal tayi tana rintse idonta don kunya tana cewa pls kar ka fada wlh bangima bama ni,muhamma yashagala da kallonta ma baduka abinda tafada ba yaji yana mamakin ganin meenal dinshi yadda takoma,daddy ne yakaraso yace oh muhammad bazaka sakar min 'ya mugaisabane? cikin mamaki meenal tadago tana tana cewa lah daddy harda kae akazo tarike masa hannu atime din taga mujaheed yana tsaye kamar gunki,tasaki kara tai kansa tana cewa ya mujaheed harda kae dama ay ban gankabah, alokacin kuma nana takaraso don tagaji dashan mamakin haka cikin rudu tariko ta tana cewa meenal! habawa wani tsalle tayi ta dafe nana saura kadan su fadi tana cewa yaya haka kika dawo ya allah kowa ya sauyamin asannan tahango su mummy dasu inna tace oh allah farin ciki kasheni don murna daya bayan daya meenal taje tana rumgumesu saboda tsananin farin cikin datake ciki bata kula da yanayin da auntie tashigaba sakamakon mugun gamo datayi,haka muhammad suman tsaye yayi ganin wadda take tunkarosa, ummi ce fuskarta dauke da fara ah tamaraso gurin muhammad, tace ikon allah kenan kaene wanda meenal kullum take ambato a cikin baccinta,tabbas bakawa yanzu yatabbatar da wannan auntie safiyya ce cikin firgici yace auntie safiyya!dama kina raye? itama cikin kidama tarike masa hannu tace muhammmad menaji ka ambata yanzu? lips dinsa yana kar karwa idonsa tafda kwalla yace auntie safiyya dama kina raye? Ya allah jikin ummi yana bari tace wlh ba ita bace muhammad ba safiyya bace 'yar uwartace ni sosae tarikesa tasaki kuka tace na rokeka tana ina ina take safiyya 'yar uwatace,tunranda nafara ganin meenal nasan ba mimi bace nayishiru dabakinane saboda wannan tunanin danakeyi kuma gashi yazamo gaskiya tabbas bakawa itace tahaifi meenal tana ina dukda kullum ina kuka idan natuna da 'yata mimi bansan tana cikin wani haliba bansan waca irin rayuwa takeba haka na hakura sabod jikina yana bani nakusa ganin 'yar uwata safiyya!tana ina kagayamin tana maganar tana girgizashi shikuwa muhammd kamar dolo haka yasau baki yana kallonta,
A time din motocin abbansu yasawo kae cikin gidan kae tsaye yafito don yasan ba lafiyaba,ganin muhamma d bashida niyyar tanka mata yasata sakinsa tanufi gurin meenal, to me karatu lamarin Dr se addu ah gaba daya tanemi kuka tarasa tadafe zuciyanta cikin girgiza kae tace impossibls baze yiwuba cikin kidima takara maimata BAZE YIWUBA! taya hakan zata kasance sosae jikinta yake kar karwa tana fiddo maganae😂😂 su mummy dukse suka zuba mata idanu ganin tana shirin ficewa a hayyacinta,
Cikin kuka ummi tarike meenal tace meenal narokeki kigayamin ina mahaifiyarki take? cikin jin tausayi meenal tace ummi lpy kike kuka?girgiza mata kae tayi tace meenal ina mahaifiyaki take? hannunta meenal takama suka nufi inda auntie take tsaye....

TAKU A KULLUM NANA BMB.

08147110349
[8/31, 3:39 PM] Nana BMB: 🤍💞🤍💞
RABON KWADO....

BOOK 3
💕💕💕💕💕
Chapter 5 · 0% Book details