← Book details Rabon Kwado Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 24

Sashe 17

Rabon Kwado Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Se yamma lis suka isa gidan su mujaheed kamar bashi bah saboda yadda yadau gyara musam man bangaren amarya ya tsaru kam ba karya su innah basu zauna bah suka sa muhammad yamaida su gidan su, dukda gajiyan da aka kwaso hakan behana su cigaba da shirya bangaren amarya bah, har seda dare yayi tukunna safiyya da mom ne suka kara yiwa amarya nasihohi masu ratsa jiki, aka soma tattara kan kowa ana komawa part din mummy ram kuwa tarike ummin tasu tana kuka dole haka suka tafi suka barta anan, itama daga karshe wayau tayi mata tace tashiga wanka, koda tashiga wankan cikin sanda tafice abinta, don bata zaunaba abin kunya ango yazo yasame ta,

Su muhammad dakin mujaheed suka sauka, ango yana gaban mirror anata kalkale kal kale yafito wanka yanata musu ibar albarka kan cewar babu wanda ze shigar masa dakin amarya shima, tsaki muhammad yay yashige ya juya yaname gyara kwanciyar sa kan bed yana cewa " aikin banza jarababbe kawai zamu ragune don bamujeba, yau dai nasan mimi tabani a gurin ka don kai lamarinka ba daga kafa, ko kunyar su ummi baji zakai bah"

Girgiza kai sameer yay yace " To Allah yakyauta maka mujaheed dama tayi maganin ka inga ta kwazzaba," murmushi kawai mujaheed yay bace musu kalaba seda yagama shirinsa tsaf tukunna yace " kwayi kwa gama nidai ai yau angona nake amarcina zanyi yanda yakamata" da pillow sameer ya jefeshi yana cewa" To mara kunya san inda dare yamaka" mujaheed yafita yanata dariya, muhammad yana jinsu be tankaba sabida tunanin abar kaunar sa dayakeyi meenal yanata zuba murmushi, abinda yawakana tsakaninsu kawai yake tunani....

TAKU A KULLUM NANA BMB

08147110349
[8/31, 3:39 PM] Nana BMB: ❣ RABON KWADO!!

BOOK 3

NA NANA BMB

GARKUWA WRITTER'S ASSOCIATION
{ Marubuta masu garkuwa da alkalami domin fadakar da al'ummah }

page 39 - 40

Zuwa lokacin da daddy ya sallami kowa, time din dare yayi sosai su muhammad haka suka nufi makwanci zuciyansu kal da farin ciki su safiyya kuwa sabuwan hira aka bude ta yaushe gamo,ummi ce tabawa hajiya labarin duka abinda yafaru da safiyya taname zubda hawaye gamida tausayin 'yar tata, nana tayi tsumu da ita don kunyar su ma takeji a yanzun bata iya furta komai sedai zubar hawaye,
Wan nan dare basuyi bacci ba kam ummi farin ciki ya isheta jitake tafi kowa sa ah yanzun wai yau gata ga 'yar uwarta! Allah kenan, sunata fira cikin farin ciki har akayi sallah asuba kowa kuma ya dakufa bacci bah.

To me karatu fada ne kuma yake shirin kaurewa tsakanin dangin auntie dana daddy, sam anata buga kofa auntie taki bude kofa juyin duniya taki koda magana, harzuwa wan nab lokaci rana ta hantse, danginta daddy suka dorawa laifi cewar ay komaeye yasameta shine sila shiya jawo komenene don be mata adal ciba ay munafur tatta yayi donme zeyi mata haka, kasancewar suna goyon bayan 'yan adamawa ne yasa abin yakara harzuka su, mussam man matar yayan auntie tafi kowa zakewa da rashin mutumci akan me anyi mata ba dai daiba kuma 'yan uwansa sunyi shiru ko ajikin su abin bedame suba seta kira iyayen ta tasanar musu,
Duka kuma bawanda ya kulasu shi daddy sammakon barin gidan ma sukayi, se su mummy da inna kuma bawanda ya sauraresu, To azhar nayi kuma aka soma jidar mutane zuwa gidan safiyya inda za ayi walima,abin mamaki ga gidan nata gana muhammad dukansu sun hadu babu karya, koda mutum daya a cikin 'yan uwan Dr bawanda yaje sunata ikirarin cewa wan nan ma ay cin mutumci ne, koda aka kira yayan na auntie ya shaida musu cewar kada wanda ya kuskura ya kira iyayensu yadaga musu hankali kome yasamu maryam itace tajawa kanta kada ma wanda yakara kiransa karshema kashe wayansa yayi gaba daya,
To gashi kuma Dr haryanzu taki bude kofah!

Gidan auntie safiyya kuwa anata shagali ana shirya amare cikin wasu lafiyayyun abaya, koda wasa meenal taki yarda su hadu da muhammad, wanda shikuma nemanta yake ruwa a jallo, seyanzun da dole gurin zama ya hadasu bayadda zatayi, ram yarike mata hannu kuwa yana tuhumarta itakuwa takasa dagowa mah saboda bayan kunyar data addabe ta mah harda tsoronsa dayake kara linkuwa a zuciyanta har yanzun tagaza yarda wai ya muhammad mijinta, mamakin shi yaki barinta akan abinda yamata ashe ya muhanmmad haka yake! 😀yanzu shine yake mata wan nan magan ganun dasuka fi karfin kanta sam jitake kamar mafarki take duka wan nan abinda yake faruwa,

'yan uwan youseep suma sunzo dama su nadiya sune amarori, shikuwa gogan mom ce tasawo shi agaba ta taso keyar sa suka taho tare, ba mom ba har shi daya kalli nana seda tabashi tausayi yadda takoma, sedai ji dakai yahanashi koda kulata mah, ana tashi bejira suba yabawa motar sa wuta yay gaba, hakanne yakara sawa zuciyan nana karaya takasa dena kuka seda safiyya ta rarrasheta sosai tukunna tasamu tadan sawa cikinta wani abu tasha magani saboda ciwon da kanta yakeyi.

Zukatan kowa cike yake da farin ciki da kauna a wannan gidan, murna da rawar kafa gurin angwayen biyu ba ah magana

WASHE GARI

Yau take lahadi! za ah mika meenal dakin mijinta tunda ta tashi takejin ta sukuku jikinta yayi sanyi sosai kiris take jira a zungureta tasoma kuka tawani lafewa safiyya ajiki, shikuwa muhammad tunda suka tashi mujaheed yasa shi a gaba da tsokana kan cewar yau yake ango.
Fuskar mom dauke da murmushi tasami meenal da mimi tana shaida musu cewar ay zarah itada iyayenta suna kan hanyar zuwa donma wani uzuri ya rikeso da tuni sun nan ana shagali dasu, bakaramin farin ciki mimi tayiba saboda tasaba da zarah sosai tanata zumudi,

Su muhammad sun tafi raka abokansu na nesa airport, 4 da 'yan mintuni kuma motar su zarah tayi parking a gidan na safiyya a time din kuma motocin Abban su mimi suka parker, yazo gidan domin yin sallama dasu yau ze wuce saboda uzurin da yake dashi,
Mahaifiyar zarah dince tafara fitowa acikin motan, hamshakiyar mata ce meji da kudi da class tasoma takunta cikin takama da izzah, se su zarah itada inty dasuka take mata baya yanzun, inty itace taje taho dasu gidan saboda basusan shiba, baban na zarah ne yafito daga karshe a mazau nin driver, abin mamaki koda suka zo shiga ciki securities din Abban su mimi, hanasu shiga sukayi hakanne yasa maman ta zarah juyowa tanawa Abban kallon mamaki, wanda shima hakanne take, cikin wani irin yanayi yake kallon su da matukar mamaki hannun sa har rawa yake ya daga waya yakira daddy awaya,
Batare da bata time bah daddy yafito, sedai koda ganin abinda yay arba dashi yasashi yin turus a tsaye yana wani irin yamutsa fuska kamar yaga kashi, zuwa wan nan lokacin maman zarah tasoma kufula cikin fushi tasoma tambayar daddy lpy ne meke faruwa? sedai sam be tanka mata bah illah iyaka ma hankalinshi yana kan mijinta bama jinta yake sosai bah, jawo kofan daddy yayi ya isa gabansa yana me yi masa wani irin kallo na kaskanci da rashin mutum ci, finger dinsa guda daya yasa ya nunasa ya ambaci sunan sa

" Imam!
Menene yakawo ka gidan nan? akan wani dalili mah zaka zomin gida taya yama!" daddy yana maganr ne cikin wani irin fushi da kunan zuciya, se a lokacin Abban ya karaso inda suke tsaye yace." Yazone domin yakara haddasa mana wata masifar a rayuwar mu, domin zuwan wan nan butulun gidanka sam ba alheri bane,"
" Inafa ze zama alheri!"
Daddy yay maganar yana kallon Abban, jikin imam a mugun sanyaye yace.

" Alhj Abubakar!" koda ya furta sunan daddy kukane yakwace masa yana me cewa." Tabbas kaine nashafe tsawon shekaru ina nemanka seyanzu Allah yahadani dakai, saboda nasan babu makawa kasan inda matata safiyya take....

TAKU A KULLUM NANA BMB

08147110349
[8/31, 3:39 PM] Nana BMB: ❣ RABON KWADO....!!

BOOK 3

NA NANA BMB

GARKUWA WRITTER'S ASSOCIATION
{ Marubuta masu garkuwa da alkalami domin fadakar da al'ummah }

page 41 - 42

Tassss! kakejin daddy ya kwadawa imam mari, cikin karaji yace." Wannan yazama nafarko kuma nakarshe dazaka kira safiyya matarka kagane koh!
Wani irin kallo imam yake watsawa daddy idonshi yakada yay jajir yace." Alhj mekake nufi dahakan?" Haba daddy kawai yake shafawa yama kasa cewa imam kala saboda takaici,
" Iman kayi gaggawar tattara iyalan ka kubar gidan nan! tunkan asan abinda yake faruwa mah,inkuma bahaka bah yanzu zansa bodyguards suyi waje daku"
Abbah cikin fushi shima yakewa imam maganar, kallon wulakanci imam yay masa yabudi baki zeyi magana, sega meenal da mimi sun bude kofa sun fito cikin farin ciki suka rungume zarah sam basusan abinda yake faruwa bah seyanzun dasuka kalli fuskan ko wannen su suka san ba lafiya ba, jikin meenal a sanyaye ta karasa inda su daddy suke tsaye tace." Daddy lpy kuwa muka ganku a tsaye haka meyasa basu shiga ciki bah," sam yarasa abinda ze cewa meenal mah, juwa tayi da kallonta kan imam wanda har seda ta tsorata da irin kallon da yake mata na kurillah, sauke ajiyan zuciya daddy yay yashafi kanta yace." Meenal kushiga ciki babu abinda yake faruwa yanzu zamu shigo muma" jinjina masa kanta tayi taname shirin juyawa tayi anyi ram da hannunta, hakanne yasa ta juyowa a tsorace tana kallon imam saboda irin rikon daya mata,
Chapter 17 · 0% Book details