← Book details Rabon Kwado Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 24

Sashe 4

Rabon Kwado Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read

NA NANA BMB.
🤍❤️🤍❤️
page 5-6
Sam mimi bata kawo komae azuciyantaba tana shiga tawuce bedroom dinsa kae tsaye tana shiga wani ni imtatceb kamshi yadoki hsncinta harseda ta lumshe idanunta, dube dube tasoma sedae bataga wayanba sema photon meenal dataci karo dashi amanne ajikin bango kamar zaka kirata ta amsa tayi dariya bakaramin kyawu tayiba a hotun tabbas ta tsaya gaban hoton aka kalleta anan za aga banbancinsu tana duniyar tunani taji huci a gefen face dinta ta dago a tsorace suka hada idanu yasakar mata murmushi kuwa, cikin tsaraka da idanu tasoma cewa yaya wlh bangantaba seda yakarewa hoton meenal kallo sannan yakalleta yace kema kinyi mamaki koh shiyasa kika tsaya kallonta, wani irin yawo tahadiye don tama rasa bakin magana, muhammad kallonta yake cike da mamaki shin wacece wannan haka datazo tarainawa kowa hankali haka kodae fuska tasakane irinta meenal dinshi, mimi kanta yana kasa sejin hannun muhammad tayi a face dinta kamar ze yage mata fuska tasaki kukan azaba zataja baya yakuma riketa sam bega wani alamuba cikin masifa yace tell me who are you?kuka mimi kawae take taki tankashi kara matsowa yayiyace ina saurarenki cikin kuka tace bansan mezance maka ba kuma kadena min haka banaso, rintse idanunsa muhammad yay saboda takaeci da bakin ciki cak kuwa tajee yadagata bedireta ako inaba se akan bed zuwa lokacin idanun mimi zazzagowane kawae basuyiba don firgici kallonta muhammad yake kuzata saduda haka tagaya masa gaskiya amma ina sema kokarin sauka datakeyi yakuwayi mata wata fisga takifa a bed din yay mata rumfa yasoma kokarin cire mata hijab din tarikeshi gam kuwa cikin shashhseka take cewa pls yaya narokeka kayimin rae kayi hakuri ka kyaleni banaso, cikin tsananin bacin rae idunshi yay jajir yace why dazan bari aiba haramun zan aikataba so kibarni na amshi hakkina tunda kin amshe kudin sadakinki yakarashe magana gamida fisge hijab din nata takarfi tasaki kara kuwa don jitae kamar ze tuge mata wuya koda yakae hannu kan rigarta tarikeshi jikinta yana karkarwa tace pls ka kyaleni haramunne abinda kake shirin aikatawa...Muhammad se a time din yadago yakalleta da rinannun idanunsa yace meyasa ze zama haramun mimi takasa cewa komae se kuka besanda sanda yadaga hannu ya sharara mata mariba yace cikin tsawa MEYASA ZE ZAMA HARAMUN? hannu biyu mimi ta dafe gefen fuskar tata cikin tsananin kuka tace saboda bani bace meenal, koda yaji haka yasaki rigan nata yasauka daga kan bed din yana furzarda iska mezafi daga bakinshi koda yajuyo yaga harta maida hijab dinta tasauko itama tanata kuka meban tausayi don taji azaba kam cikin bacin rae yace kin fiya taurin kan masifa tun a garden naso kiyimin wannan bayanin amma kika bari harta kaemu ga haka sannan kika fadi gaskiya kin batamin rae, kuma tambaya tafarko itace menene sunanki?
Cikin kuka mimi tace sunana safiyya amma ana kirana da mimi, DUM muhammad yaji kirjinshi yabuga safiyya yakuma nanata sunan yaname zuba mata idanu jin yadda yakuma nanata sunan ne yasata dagowa takalleshi fargaba takara dirar masa saboda koda tadago ayanzun fuskan auntie safiyyansa kawae yahango a tata fuskan cikin wani irin yanayi ya lumshe idanunsa nadan lokaci kana yasauke ajiyan guciya yanemi gu yazauna sannan yakalleta yace zoki zauna, sam mimi batae masa musuba tazo tazauna zuciyanta haryanzu tana mata dancing,
Murya a raunane yace mimi ina meenal take?kanta a sunkuye tace tana gidanmu baki bude muhammad yasoma kallonta cikin rashin fahimta yace banganeba, se a time din tagyara zamanta jiki a sanyaye tace insha allahu meenal tana gidanmu itama tana rayuwa amatsayina kamar yadda nakeyi anan allah ne kadae yasan nufinshi daya kaddara hakan takasance al amarinmu akwae ban mamaki seyau nakara tabbatar da hakan nakara ganin hotonta, muhammad yace mekikenufi kenan kikace insha allah baki tabbacin tana gidan naku kenan why dazaki yaudari iyayenmu haka tunda nafara dora idanuna akanki nasan bakye bace meenal dita wannan abun yadauremin kae meyasa hakan zata kasance taya kamanninki yazamo irin nata? mimi duka abinda yafaru da ita tasanar masa da irin mafarkin datakeyi da meenal da soyayyarsu da mujaheed, mamaki yahashi magana illah kallon ta dayakeyi, girgiza kae yay yace koda akasanar daddy bashi yahaifi meenalba sam baki shiga tashin hankali akan hakan bah wannan dalilinne yasa shima daddy fara tantama akanki, sesae daga rana irinta yau komae yazo karshe gayamin awanin garin kike inda meenal take rayuwa yanzu, mimi tace gombe! gombe ina? yola, tabashi amsa, yajin jina kae yace shin kece wadda mujaheed yafara furtawa so ku kuma sunfara soyayyane da meenal kafinke?mimi ta girgiza masa kae tace nice yafara furtawa so kuma na amshi soyayyar sane saboda nagani meenal tanada masoyinta shiyasa na amince masa tunda ina matukar kaunarsa nima, cikin daga hankali muhammad yace kina nufin meenal tanada masoyi yanzu haka?
Mimi takalleshi a takaece tace eh nagane hakanne saboda irin kalaman bakinsa da sunan datayi masa saving, cikin mamaki muhammad yace to wanene wannan nikuwa dabansaniba, broda din nadiyane aminiyarta shine suke soyayya, muhammad ya rintsu idanunshi yace kada nakuma jin kinfurta wannaa maganarma dole zuwa adamawa yataso mana,
Mimi cikin tashin hankali tayi bayi tana girgiza masa kae tace pls kada kumaidani gida yanzu batareda na auri ya mujaheed bah katemaki rayuwata,muhammad yace why?setayi shiru tana tunanin aurenta da bassam bashakka yanzu wannan auren yakusa, seda tahadiye yawo tace saboda mu bama auren bare sedae a family, da mamaki muhammad yace saboda me wani irin tsari gareku haka ko ince danku komadae meye kada kidamu ni nace namiki alkawari insha allah zaki auri mujaheed cikin tashin gamsuwa tace nidae katemakeni kada kamaidani gida batare da na aureshi zuwa yanzu seda yagama nazartatta tukun yace haryanzu da akwae abinda kike boyemin so kada kidamu sansan komae idan munje gidan naku kitashi kije kiyi bacci kikuma sawa ranki cikin kwanakinnan zaki koma gida, mimi tasaki kuka tadago zata kuma yimasa magana yadaga mata hannu, cikin daure fuska yace bazan kuma jin tabakinki bafa so jeki kwanta idanma karya kikayi duka zansan komae mimi cikin cikin bacin rae tafita daga dakin tana kuka,lumshe idanunsa yayi yana ganin wannan abun kamar a dramatic allah sarki auntie safiyya ga wani muhimmin abu yana shirin faruwa dake amma bakya nan allah yajikanki da rahama koda yabude idanunsa tafda kwallah yace kema mahaifiyata allah ya kyautata makwancinki yau gashi danki yayi aure barabon kiga jikokinki...
Koda mimi tashiga bedroom dinsu sam batabi takan kurarda tadebo nana bah tana gefe tanata charting fadawa kan bed tayi cikin kuka mimi tafara magana da fillanci gamida hausa harda turanci tana cewa meyasa zakayimin haka sam bakasan halin mahaifina bane dole nakoma seyamin aurennan nikuma banason ya bassam dinnan ya mujaheed nakeso kumashi zan aura ni kuka take me tsuma guciya, zuwa lokacin nana tagama firgicewa jin mimi na yarenda bata san ta iyashiba bakaramin tsorata tayiba tamike tayi wane da mugun gudu saboda ba makawa tasawa zuciyanta meenal aljanune suka shigeta😂😂 ....

TAKU A KULLUM NANA BMB.

08147110349
[8/31, 3:39 PM] Nana BMB: 🤍💞🤍💞
RABON KWADO....
BOOK 3
💕💕💕💕💕
Chapter 4 · 0% Book details