← Book details Rabon Kwado Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 24

Sashe 10

Rabon Kwado Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Yana sonki mana so me wuyar fassarawa,sonda yakeyi mikine ma yasa ya mallaka miki zuciyansa gaba daya ke kadaice a cikinta,tun kina zanin goyo kaunarki tazama jinin jikinsa so kinga wan nan shine masoyinki na gaskiya ba yousep bah,kuma iname tabbatar miki soyayyar sa zata mantar dake wani yousep fargabar dayakeyi a yanzu shine idan yazo gareki zaki kaunaceshi ko kuwa bazakiyiba"
Kallonsa meenal kawai takeyi da mamaki dauke a fuskanta.
" Sweetie kiyi min al kawari aduk sanda kika kasance tare da mijinki zaki gaya masa gaskiyar abinda ke zuciyanki kada kice zakiji kunyar sanar masa,idan kinajin sonsa ki gaya masa haka idan baka sonsa ki gaya masa"

Hannunsa takara rikewa tace." pls ya muhammad ka gayamin wanene shi daya dade yana sona haka"
murmushi yayi yace." ay bakiyimin al kawarin bah tukunnah"

" To nayi maka al kawari, haba! ya muhammad sekace baka sanni bah inbana sonsa kobe tambayaba sena gaya masa but innaji ina ra ayinsa zan nuna masa,amma kagaya min wanene shi?"

muhammad yay murmushi yace." shedar auren tana nan zanbaki da sadakinki sekiga kowaye a ciki"

" Shedar aure kuma! ya muhammad tun yaushe akayi auren ne?"
Yamike yakama hannunta suka koma ciki seda suka shiga parlour yasaki hannunta yace, "kije kiyi wanka bayan breakfast kizo inbaki"
Ya haye sama abinsa yabarta nan tsaye da sakak ken baki,
Tunkan yashiga bedroom din yake jiyo masifar mujaheed seda yashiga yaga ashe waya yakeyi,yashiga masa murmushin mugunta seda yagama wayar yajuyo yana antaya masa harara,hakanne yasa muhammad fashewa da dariyar mugunta, be ankara bah kuwa yaji mujaheed ya cimimiyo masa riga yana cewa.
" Bakin mara mutumci komai kaine kahada shi ay banjiba banganiba kowa yakwaso masifar sa seya kirani kuma kazo kana min dariyar mugunta"

Cikin dariya muhammad ya kwaci rigarsa yana cewa "meyay zafi Allah yabaka hakuri kowaye zemaka mita kabashi hakuri abinda yanzu zamu fara indai shagul gulan bikine, mutum harseya gaji dazuwa"
Yana shafar cikinsa yana cewa
"be cool angon mimi maida wukar"
duka mujaheed yakai masa yay saurin shigewa bathroom yana dariya....

TAKU A KULLUM NANA BMB

08147110349
[8/31, 3:39 PM] Nana BMB: ❣️RABON KWADO....!!

BOOK 3

NA NANA BMB

GARKUWA WRITTER'S ASSOCIATION
{ Marubuta masu garkuwa da al kalami domin fadakar da al'ummah }

page 23 - 24

Rike kai sameer yay yace.
"Wai meyake faruwane? gaskiya mujaheed bakada mutumci,ay zamu hadu,ina tsiyama ko a waya ka gayamin sedai naga anayi ay yayi kyau"

An gama taron daurin aure lpy, sedai koda 'yan jaridu sukaso jin tabakin angwayen guda biyu basu samu damaba don fuskar kowan ne babu annuri garama mujaheed yana dan yake akan yousep da idanunsa sukayi jajir don bacin rai,
Cikin gidama kowa yanata bidiri banda meenal da mimi,saboda mimi fargabace tahana ta sukuni tana tunanin yadda zasu kare da mujaheed,ita kuma meenal kunci da bakin cikine sukasa har yanzu take zubar hawaye idonta dukya kumbure wai anyi mata aure kuma ma batasan waye aka aura mataba don cin zali tanajin yadda a keta shelan an aura wa nana wanda takeso sosai take ganin an tauye mata hakki,
Nana kuwa tunda take bata taba shiga farin ciki irin nayauba ( nikuwa nace Allah yasa yadore wan nan farin cikin ) jitake kamar an mata bushara da gidan al jannah wai yau itace matar yousep ganin abin take kamar a mafarki,
Auntie tana daki a makure speakers nata kuwwa ana shelan daurin auren kamar daga sama taji wai harda nana diyarta sosai abin yadaure wa auntie kai kuma koda wasa takasa fitowa koda parlour,
Bassam yana ganin duka shagalin da akeyi kuma koba komai yanzu yacikawa mimi burinta hankalinshi ze kwanta,to koda akazo tafiya da shi Abbansu yabashi letter dinda mimi tayo masa,koda yakare karanta wa bassam mur mushi mara yankewa ne yake bayyana a fuskarsa yanajin wani kwari a tare dashi sedai Abbansu tausayin bassam yake sosai,
Letter din yamar wa da Abban yamaidata aljihu, kuma be tashi karan tawa bah seda suna hanyar komawa gida yaga abinda takunsa wasikar abin mamaki shima murmushin kawai yayi ya maida pepper din.

Muhammad yay mamakin ganin yadda meenal takoma lokaci daya tawani kojale idanu sunyi suntum, shikuwa daddy bin nana kawai yake da idanu ganin irin farin cikin dake tare da ita se yashe hakora take don takasa boye farin cikin ta, se yanzun yake gasgata ashe kam nana tana son yousep din,dama shine wanda nana take nufin tanaso kenan? shikadai dai yaketa sake sakensa azuci,
To koda tashiga gurin auntie tata ma kaimata abinci, auntie da mamaki tasoma bin nana da ido ganin yadda taketa farin ciki babu alamun damuwa a tare da ita,

Babane zaune yatasa mujaheed a gaba yanata zolayan sa ana dariya cewar baze taba mantawa da zuwansa adamawa bah,
Haka nadiya se tsokanar nana takeyi itakam batasan farin cikin datake cikiba, sunyi rarrashin duniya meenal takiyin shiru seda suka kira su mummy tukunna tayi mata magana ta tsagaita da kukan sedai kukan zuci,
Ta kafafen sadarwa muhammad gaba daya yabi yawatsa dauren auren nasu mujaheed duka abokansu suka gani aka soma kiran mujaheed kuwa karshe ma kashe wayan nasa yayi don besan meze cemusu bah,kowa da korafin da zeyi masa bayan basu san sama taka abin yafaruba😅.

Karfe 9 na dare komai yalafa kowa yanemi ma tsuguni, sedai haryanzu mimi batada sukuni wanka tashiga tafesa tazo tashirya tanata zuba kamshi tasaka simple kayan bacci, tayafa dan gyale tafito i zuwa inda meenal take kwance tarike mata hannu tace.

" Sister pls taso muje garden muyi magana"

Sam batayi mata musuba tamike suka fito sukaci karo da muhammad don shima gurin meenal din tashi yanufu, da fara arshi yarike mata hannu yace.

" Sweetie gurinki dama zanzo yanzu yau bansamu time mun zauna bah,"
Kmar jira take kuwa meenal hawaye yacigaba da sintiri a fuskarta,mimi tace.

"Ya muhammad Allah yasa meenal taji maganarka kai, don taki dena kuka haka tayini yau"

Cikin damuwa yace." zata denashi yanzu kuwa mimi kada kidamu" hannunta yaja suka koma ciki yana murmushin mugunta saboda ganin inda mimi tanufa yasan kuma kowaye agurin,

Yana kwance a kan daya daga cikin dogayen kujerun garden din idanun sa a lumshe sam mimi bata kula da mutum bah a gurinba hankalin ta yana kan wayar ta akayi sa ah kuma inda yake ta nufa don gurinne babu haske sosai furanni sunyi yalwa a gurin,
Mimi seda tazo zama tukunna idanun ta suka sauka a kanshi wanda tunda yaji takunta yabude idanun sa ya saukesu a kanta,
Wata irin kara mimi tasaki saboda firgitar datayi tasaki wayar hannun nata tana shirin jada baya, sedai kash ta makaro, mujaheed hannun sa yasa yafisgo ta tafado jikinsa yashiga bin ko ina najikin ta da idanu, wanda jikin nata in banda kar karwa babu abinda yakeyi,

Cikin kallon kurilla dayake mata cikin sexy voice yace." burinki yacika yau koh, kin auri mujaheed"
Idanun ta ne suka soma fidda hawaye jin wani rainin hankali da mujaheed ke shirin yimata yana maganar yana kara matseta ajikinshi, voice dinta da lips dinta suna rawa,tace.

" Pls kasakeni natafi niban san kana nan bah ay"
Tayi maganar kuka yana shirin kwace mata domin kuwa a tsorace take dashi matuka,
Matsa mata hannu yayi cikin mugunta, zafinda ya ratsata ne yasata sakin 'yar siririyar kara, tana shirin janye jikinta daga nasane gyalen kan nata yafadi kasa takuwa rintse idanunta tana matse kirjinta da tuni idanun mujaheed suka sauka kansu, nan da nan yanayin mujaheed yacan za cikin wani kalan voice da mimi batasanshi da itaba yace.

"Ke banason gulma malama kawai kin kawo kanki shine zaki fara kaucewa,jaraba tasa kin kasa hakuri shine kika biyoni koh,to yanzu kuwa zakiyi mamaki nah"

Zuciyan mimi ne tawani harba ga bakin cikin rainin hankalin nan na mujaheed, cikin kuka tace.

"Naroke kah kayi hakuri kasakeni natafi cikin gida nibansan kana nan bah da babu abinda ze kawoni gurin....Hade bakinsu da mujaheed yayine yasata yin shirun dole tana fiddo da manyan idanunta waje tsoro da firgici suka dirar mata, sosai take kokarin kwace jikin ta daga gareshi abu ya gagari kundila,
Jin tana shirin kwacewa ne yazura hannuwanshi cikin rigarta yamatseta dakyau sam babu abinda yamasa shamaki don kuwa batasa bra bah kuma seyanzun take dana sanin rashin sawarta,
" Ke banason rainin hankalin nan naki kin manta na biya sadakin kine?"
A kunne yayi mata rada,daga haka ya kwanto ta kan laps dinsa yanayin abinda yaga dama,
Zuwa yanzun mimi tagama sallamawa rainin hankalin mujaheed.

meenal tana kwance ta dora kanta akan laps dinsa hawaye ne kawai yake bimata fusta tana cewa.
"Ya muhammad meyasa zaka bari ayi min aure bayan kuma kasan banaso, kuma ma bansan waye mjin nawaba"

TAKU A KULLUM NANA BMB.

08147110349
[8/31, 3:39 PM] Nana BMB: ❣️RABON KWADO....!!

BOOK 3

NA NANA BMB

GARKUWA WRITTER'S ASSOCIATION
{ Marubuta masu garkuwa da alkalami domin fadakar da al'ummah}

page 25 - 26

Dagota muhammad yay yana murmushi yace." sweetie wayasan to bakyason auren,ay bamusan kinada wanda kikesoba saboda bakiyi mana bayaniba ashe bakyason zabin da daddy yamiki"
Hawayene yakuma ciccikuwa a idanunta saboda yousep dinta datake tunawa,cikin sanyin jiki tariko hannunsa tana cewa

" Bazan taba kin zabin da daddy yay minba saboda nasan baze taba zabamin abinda ze cuceniba don haka zabinshi nima nawane babu abinda zancewa daddy sedai Allah ya saka masa da gidan Aljannah" sarkewa muryanta yasomayi zata cigaba da kuka tunowa da cewar daddy ba mahaifinta bane
" Ya muhammad ina ganin wannan abin kamar a film wai daddy bashi yahaifeni bah haryanzu zuciyata takasa aminta wlh, gaskiya nayi asarar rayuwa dana kasance 'ya ga azzalumi kuma butulu, ashe shinema wanda ummi tabamu labarinsa, Allah sarki auntie har abada bazanga bakinki bah ashe ba ita bace ta haifeni shiyasa tafi kaunar yaya akaina, but dukda haka ina alfahari da ita kosau daya bata taba goran taminba wan nan ma abin ajin jina matane!"

Cikin kuka ta karashe maganar tata harda shasheka domin kuwa abin yana matukar taba mata zuciya,tamatukar bashi tausayi haryama rasa dawani kalami ze rarrsheta dole daman yasan zatayi kuka, to koba komai daga karshe auntie taga matsayinki a yanzu da irin gatanki a rayuwa,
Seda tayi kuka har kanta yasara mata ta lafe a jikinsa tadena shasheka sedai hawaye,
Chapter 10 · 0% Book details