← Book details Rabon Kwado Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 24

Sashe 3

Rabon Kwado Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read

08147110349
[8/31, 3:39 PM] Nana BMB: 🤍💞🤍💞
RABON KWADO....
BOOK 3
💕💕💕💕💕
NA NANA BMB.
🤍❤️🤍❤️
page 7-8
Auntie tana cikin waya taga nana ta fado mata daki a firgice da mamaki ta kashe wayan tana kallon nana tace lafiyanki kuwa? cikin kuri kuri da ido tanata haki tace wlh auntie meenal aljanune suka shigeta nifa tun wannan tafiyar datayi gaba daya meenal tasauyamin gayamikene kawae banba kullum cikin baccinta inajin tana wani yare to wlh yanzu harshen natama yajuye se hauka take ita kadae nidae bazan iya kwana a dakinba wlh wae seta auri ya mujaheed tanata hauka, cikin tsananin farin ciki auntie tamike tasoma babbaka dariya harda tafawa sannan tace zokiyi kwanciyarki anan nana aljanun su haukata ta itakadae ninasan abinyi yikwanciyarki kinjee nana jiki a sanyaye tahau kan makeken bed din na auntie takwanta tae tsumu mamakin mimi gaba daya yahanata sakat,
WASHE GARI
Nana dakyar ta iya tunkarar dakin nasu tana tsoron kada mimi ta danketa shahada tayi ta tura kofan ahankali tashiga dae dae lokacin kuma mimi tafito daga wanka idanunta sunyi luhu luhu saboda kuka ko inda nana take bata kallaba tazauna gaban dressing mirror tana mutsika mae duk abinda nana take tana ankare da ita sedae taki kallon inda takema, wankan nana tashige itama abinda haka zalika koda sukazo breakfast su hudu a dining nana se kallon mimi take takasa cin nata abincin haka itama mimi yanayin datake ciki yasa takasacin komae, gyara zama muhammad yay yana murmushi yakalli mimi yace my wife kici abincin mana haba kinsan banason damuwan nan naki ina tare dakefa akowani lokaci so kada kikara sama kanki damuwa kinji kodae dakaena kikeso in baki? daga mimi har nana baki sake suke kallonsa saboda yadda yay maganar shagawaba, harda kanne mata ido daya,wani dogon tsaki auntie taja tana antaya musu harara,lura da hakan da yayine yasashi gyara zama yace yawwa inaso natambayeki dama shekararki nawane yanzu?cikin sanyinta mimi da mamaki kuma tace 18 years WOW kinga kingirme 6ter dinki ita tana 17 yanzu mimi tayi murnushi jin yadda muhammad yake mata magana ashe haka yake shine jiya harda sharara mata mari😅😅 cikin jin dadi tace kundace kaeda matarka inayaku da murna yabaku zaman lpy gashi bantaba ganinta ba,muhammad yaji dadin addu ar tata yace ameen ya allah kada kidamu indae 6ter dinkice zaki ganta cikin kwana biyunnan, nan danan idanun mimi suka kawo ruwa tana kallonsa tana girgiza masa kae zatayi magana yadaga mata hannu yace no dolane ne fah kisa aranki wannan tafiya anyishi angama tayama zan kyale banason kukan nan naki babu abunda ze faru ki kwantar da hankalinki, kukan nana ne yasa su suka juya suduka suna kallonta ta rukumkume auntie tana cewa wlh maganata gaskiyace ashe ba meenal bace aljanune ashe ya muhammad ma yasani jiya inajinta tana sumbatu muhammad yasaki murmushi bekae karsheba dariya ta kufce masa haka mimi tana darawa tana kallon ikon allah gurin nana, dukda magan ganun nasu sunsa auntie aduhu hakan behanata dakewa ba cikin tsawa tace banason hauka nana meyake damunkine?
Muhammad mikewa yayi yace wify muje garden mukarasa tattaunawa tunda naga tunyanzu anfara tsorata haka inaga nan gaba kuma?cikin bakin ciki auntie tace to don allah daga garden din ku bulla ta China kada kudawo mana nan karamin mara kunya kaega me mata koh!
Shidae muhammad ficewa yayi yana dariya mimi tabi bayansa sebayan sun zaunane yake cemata mimi inason kigayamin gaskiya shin kece mujaheed yatabawa jikinta ko meenal ce?wata irin kunya kuwa takama mimi kanta aduke tace nice ba meenal bace, muhammad besan sanda yasaki ajiyan zuciyaba yana godewa allah a zuciyansa tanason magana takasa, seda yabudi baki zeyi maganar ne ta tareshi da cewa dama abisa tsautsayi abin yafaru yatabani badon yana...Sekuma tayi shiru,
Muhammad yasaki shu umin murmushi yana cije lips dinsa azuciyansa yana cewa shegennan bakada dama wlh ayzamu hadu, sunjima suna tattaunawa a garden din wanda hakan yakara samusu fahimtar juna yafahimci so silent ce ita amma yana mamakin yanda kowa yaki fahimta duk karadi irinna meenal.
Yau talata takama ranar tafiya adamawa duka an hallara su inna da baba mummy da daddyn mujaheed dashi din kansa harda kanwar mahaifiyar muhammad hafsa,mimi kwallace tacika mata idanu ganin mujaheed yadda yakoma a 'yan kwanaki yawani rame se 'yar fuska, daddy tinda yadawo yake kallon mimi yana kara gasgata maganar dannasa dasukayi awaya, tunda garin allah yawaye auntie taketa faman sababi da masifa da tujara akan me za ah kirkirar musu tafiya adamawa kuma aki fadan abinda za aje yowa shidae daddy ta tafasa bece mataba yamayi kamar besan tanae bah anata shirin tafiya donkosu baba da inna basusan neza ahje yowa canba,
Mujaheed suna bedroom suna shiryawa yakalli muhammad yace waekae waca irin tafiyace wannan muhammad ka kaga mana anki kuma sanar mana abinda zamuje yowa,muhammad yay murmushi yace to maida wuyar aure zamuje nema maka wani irin kallo mujaheed yamasa yace kamarya? banganeba!manta kawae to inmunje can ka gane,
Wae kuwa majaheed dakukaje bikin sameer babu abinda yafaru da meenal,mujaheed yay shiru yana tunano abinda yafaru,cikin rashin fahimta yace kamarya ba abinda sameta?muhammad yay murmushi yace ina nufin bata tafi wani gurin kunnemeta kunrasaba?mujaheed cikeda mamaki yake kallon muhammad taya akayi yasan hakan kodae meenal tagaya masa komaene kallonshi yayi yace eh bamu nemeta munrasaba ya akayi kake tambaya, muhammad yace babu komae tasowa mujaheed yay yana cewa wlh karya kake da akwae wata akasa,
Muhammad yana murmushi yace to shikenan kabar komae semunje can zaka fahimci komae basena yimaka bayani bama pls kayi kashirya kasan da tafiya agabanmu, cikin jin haushi mujaheed yace a ah tafiyace a bayanmu ba agabanmuba! muhammd yakuwa bushe da dariya mujaheed yakyaleshi yacigaba da saka kayansa,muhammad kuwa turaruka yake fesawa kala kala zuciyanshi taf da farin ciki yau zega sweetienshi shigan dayayi tamatukar yimasa kyau yasha shaddi brown light tanata zuba uban kyalli haka hukansama daya dora shikansa daya kalla kansa a mirror seda ya kanne ido daya, shikuwa mujaheed boyel ne yasaka me tsadar gaske peach color kalarda mimi take matukar kaunar soh sosae yahadu inkace zaka tsaya tantance wanda yafi wani kyau acikinsu bata time ne ma, suka fito a tare abin sha awa, mimi koda tahango sahibinta batasan dmsanda tai gunsaba tarikeshi tana murna tace ya mujaheed baka taba yimin kyau irin na yauba pls katsaya muyi selfie,zuciyan mujaheed kamar zata fado dama yaya karfin hali kawae yake koda camera tahaskasu kasa fara ah yayi seda tasaki nata murmushinne tukunna besanda sanda yay nashi smile dinva shima tabbas yabada kala wadannan couple din abinda sha awa, mota biyu sukayi abinsu ta tafiya sunbata lokaci sosae gurinyin hotuna kafin akadauki hanya kuma dodar muhammad baki yaki rufuwa....

TAKU A KULLUM NANA BMB.

08147110349
[8/31, 3:39 PM] Nana BMB: 🤍💞🤍💞
RABON KWADO....
BOOK 3
Chapter 3 · 0% Book details